Matsalolin tsaro biyar da suka raba hankalin sojojin Najeriya

Sojan Najeriya a yankin Damasak da ke kan iyakar Najeriya da Nijar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sojan Najeriya a yankin Damasak da ke kan iyakar Najeriya da Nijar
    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 7

Rikice-rikice a sassan Najeriya daban-daban na ci gaba da raba hankalin rundunar sojin Najeriya.

Matsalar tsaro dai lamari ne da ke ci gaba da ci wa Najeriya tuwo a ƙwarya, inda a kowace rana ake samun rahotonnin kai hare-hare tare da kashe-kashe.

Lamarin da ya sa wasu ke ganin sojojin ƙasar na ci gaba da fuskantar babban ƙalubale wajen yaƙi da matsalar tsaron da ke yi wa ƙasar katutu.

Kan haka ne BBC ta ta yi nazarin wasu daga cikin manyan rikice-rikicen da sojojin Najeriya ke yaƙi da su.

1) Masu iƙirarin jihadi

Ƴanbidiga

Asalin hoton, Getty Images

Dakta Kabiru Adamu shugaban kamfanin Beacon Security, mai nazarin matsalolin tsaro a yankin Sahel, ya ce babban abin da rundunar sojin Najeriya ke fama da shi shi ne yaƙi da ayyukan masu iƙirarin jihadi, waɗanda ke kai hare-hare, kan fararen hula da jami'an tsaro.

''Akwai ƙungiyoyi fitattu aƙalla guda biyar da ke da'awar iƙirarin jihadi a Najeriya, kuma dukkanninsu rundunar sojin ƙasar na bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta kawar da su'', in ji shi masanin.

Ƙungiyoyin sun haɗa da Boko Haram da tsaginta na ISWAP, wadda ke samun goyon bayan ƙungiyar ISIS, da suke addabar yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Boko Haram ta shafe fiye da shekara 15 tana ƙaddamar da hare-hare yankin arewa maso gabashin Najeriya, musamman jihohin Borno da Yobe.

A shekarar 2014 ne ƙungiyar ta kai hari makarantar ƴanmatan Chibok tare da sace ɗalibai fiye da 200 kodayake daga baya an kuɓutar da mafi yawansu, sai dai har yanzu akwai wasu a hannun mayaƙan kungiyar.

Mutuwar shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau da zafafa hare-haren sojoji ta raunana ƙungiyar, lamarin da ya sa ta janye daga yankunan da ta ƙwace.

To sai dai a baya-bayan nan ana ganin yadda ƙungiyar ISWAP, wadda ta ɓalle daga Boko haram a shekarun baya, ke ƙara ƙaimi wajen ƙaddamar da hare-hare a wasu sassan jihohin Borno da Yobe.

Sojojin Najeriya

Baya ga waɗanann biyun akwai kuma wasu ƙungiyoyin masu iƙirarinjihadi kamar Lakurawa da ta ɓullo a baya-bayan nan a wani yankin arewa maso yammacin ƙasar, a cewar Dakta Kabiru Adamu.

''Haka kuma akwai ƙungiyar Ansaru, wadda ita ma tana da alaƙa da ƙungiyar IS, ko Al-qeada wadda ke ayyukanta a wasu yankunan arewa maso gabas da wasu yankunan arewa ta tsakiya'', in ji Dakta Kabiru Adamu.

Sannan kuma akwai ƙungiyar Mahmudawa da ta bayyana a baya-bayan nan a jihohin Kwara da wasu yankunan jihar Neja da ma wasu yankunan Benin, da kuma saura ƙananan ƙungiyoyi masu alaƙa da al-Qaeda da IS.

A ƙoƙarin sojojin na murƙushe wannan sun kafa rundunoni masu yawa, fitacciya daga ciki ita ce Operation Hadin Kai mai yaƙi da Boko Haram da ISWAP, wadda ke da shalkwata a Borno.

2) Ƴanfashin daji/Masu garkuwa da mutane

ƴanbindiga

Asalin hoton, Social Media

Wata matsalar da sojojin Najeriya ke fuskanta a ƙasar ita ce ta ƴanfashin daji da masu garkuwa da mutane - matsalar da ta fi ƙamari a yankin arewa maso yammacin Najeriya da wasu sassa na arewa maso tsakiya.

Ƴanfashin dajin kan tare manyan titunan ƙasar domin sace matafiya su sace su, a wasu lokutan kuma suna kai hare-hare wasu ƙauyuka, inda suke sace mutane domin neman kuɗin fansa.

Waɗannan mahara a baya sun riƙa kai hari makarantu da masallatai tare da sace ɗalibai da masu ibada a lokuta da dama, domin neman kuɗin fansa.

Hari na baya-bayan nan da ba za a manta da shi ba, shi ne wanda aka kai makarantar Kuriga da ke jihar Kaduna tare da sace ɗalibai fiye da 100 a 2023.

Rundunar sojin Najeriya ta ƙaddamar da runduna ta musamman, mai suna Operation Fansar Yamma, domin yaƙi da wannan nau'i na ƴanbindigar.

3) Rikicin ƙabilanci

Kasuwa

Asalin hoton, Getty Images

Yankin Arewa ta Tsakiyar Najeriya kuwa ya yi ƙaurin suna wajen rikicin ƙabilanci da na addini ko na manoma da makiyaya.

Jihohin Benue da Plateau da wasu lokuta jihar Nasarawa, ne kan gaba a wannan rikici, inda ake samun asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa, a cewar Dakta Kabiru Adamu.

A ko a watan da ya gabata ma wasu mahara sun kai wasu garuruwan jihar Plateau tare da kashe fiye da mutum 50.

Nan da mai rundunar sojin ƙasar na ƙoƙari wajen ganin ta magance rikicin, inda ta ƙaddamar da runduna ta musamman mai suna Operation safe Haven.

4) Masu fafutikar ɓallewa daga Najeriya

Hoton wasu ƴan bindiga

Asalin hoton, AFP

Can ma a yankin kudu maso gabashin Najeriya, sojojin ƙasar na fama da ƙungiyoyin ƴan'aware masu rajin ɓallewa daga Najeriya domin kafa ƙasarBiafra.

Ƙugiyoyin da ke cin karensu babu babban a wannan yankinsun hada da IPOB da Eastern Security Network, wadanda a lokuta da dama ke ƙaddamar da hare-hare kan jami'an tsaron Najeriya, musamman ofisoshin ƴansanda.

Matasan masu ɗauke da makamai da ke kai hare-hare kan ofisosin jami'an tsaro da gine-ginen gwamnati.

A wasu lokuta sun riƙa kafa dokokin hana fita a kowane mako, domin nuna goiyon baya ga ƙudurinsu na ɓallewa daga Najeriya.

5) Masu fasa bututu don satar man fetur

wasu butun mai

Asalin hoton, Gbaramatu Voice

Dakta Kabiru Adamu ya ce a yankin Naija Delta mai arzikin man fetur matsalar da tsaro da sojojin Najeriya ke fama da ita, ita ce ta masu fasa bututun mai dmin satar ɗanyen man fetur.

''A nan ma rundunar sojin Najeriya tana fama da yaƙi da waɗannan mutane masu ɗauke da makamai, da ke satar mai da aikata wasu laifuka da suka danganci haƙo man fetur'', in ji shi.

Baya ga satar mai, ƙungiyoyin masu aikata laifuka da ke wannan yanki kan yi garkuwa da mutane domin neman kudin fansa a wasu lokata.

Ƙalubalen da sojojin Najeriya ke fuskanta

Dakta Kabiru Adamu ya ce rundunar sojin ƙasar na da tarin ƙalubalen da ke gabanta, wadanda ke yi mata tarnaƙi wajen gudanar da ayyukanta.

Ya kuma ce dole ne rundunar sojin ta magance matsalolin domin samun nasara a ayyukan da ke gabanta.

Wasu daga cikin matsalolin da ke yi wa rundunar sojin tarnaki kamar yadda Dakta Kabiru Adamu ya zayyano sun haɗa da:

  • Rashin isassun jami'ai: Ɗaya daga cikin manyan matsalolin da rundunar sojin Najeriya ke fuskanta, ita ce rashin isassun jami'i, a cewar Dakta Kabiru Adamu. ''Yanzu idan ka duba girman Najeriya da irin tarin matsalolin tsaron da ke gaban sojojinta, sai kuma a ce maka duka adadin sojojin Najeriya bai wuce 230,000 ba, to ka ga ai akwai matsala'', in ji shi.
  • Rashin wadatattun kayan aiki: Ita ma wannan matsala ce da ke ci wa rundunar sojin Najeriya tuwo a ƙwarya, kamar yadda masanin ya yi ƙarin haske. ''Yaƙi da ƴan'tadda masu iƙirarin jihadi, wadanda galibi ke sajewa cikin mutane, na buƙatar sabbi kayan aiki na zamani na musamman'', in ji shi.
  • Rashin inganta walwalar sojoji: Dakta Kabiru Adamu ya ce wani abu da ke zama tarnaki ga ayyukan sojojin Najeriya shi e rashin kula da haƙƙoƙi da walwalarsu. ''Irin albashin da ake biyansu da muhallin da ake ba su da kuma horo, duka na buƙatar a sake nazarinsu'', in ji shi.
  • Rashin samun goyon bayan jama'a: Wannan ma na cikin tarin matsalolin da ke gaban rundunar sojin na Najeriya, a cewar Dakta Kabiru Adamu. ''Yadda a wasu lokutan sojojin ke gudanar da ayyukansu, musamman a wurare na bincike, da yadda suke rufe kasuwanni da dai sauran nau'ikan takura wa jama'a ya sa mutane sun fara daina ba su haɗin kai'', in ji shi
  • Jinkiri wajen sauya wa jami'a wurin aiki: A ƙa'idar aikin soji akwai adadin lokaci da ba a so soja ya zarta a wurin da aka kai shi domin yaƙi, amma sojojin Najeriya kan kwashe shekaru a wasu wuraren ba tare da sauya musu wurin aiki ba, kamar yadda Dakta Kabiru Adamu ya bayyana.
  • Zargin cin hanci da rashawa: Dakta Kabiru Adamu ya ce akwai zarge-zarge masu yawa da ake yi wa rundunar sojin na karkatar da kuɗaɗen da ake ware wa rundunar domin gudanar da ayyukanta. "Akwai cibiyar CISLAC da ƙungiyar Transperency International, wadanda suka yi bincike mai zurfi tare da bayar da shaida kan wasu manyan sojoji da aka kama game da irin wannan laifi na satar kuɗin rundunar, musamman wajen sayen kayyakin sojin'', in ji mai nazarin harkokin tsaron.
Dakta Kabiru Adamu

Asalin hoton, Beacon Consulting

Bayanan hoto, Dakta Kabiru Adamu, masani kan al'amuran tsaro a yankin Sahel

Abin da ya kamata gwamnati ta yi don ƙarfafa sojojin

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dakta Kabiru Adamu ya ce akwai hanyoyin da ya kamata a bi domin magance tarin ƙalubalen da ke gaban rundunar sojin Najeriyar.

''Na farko ya kamata gwamnati ta inganta yanayin aikin sojojin ta hanyar gyara albashin da alawus da muhallansu, sannan a samar musu kayan aiki masi inganci''.

Sannan kuma gwamnati ta waiwayi dabarunta na yƙi da ƴanbindiga, ta duba dabarun da ke aiki, domin inganta su, sannan ta duba wadanda ba sa aiki, domin sake musu fasali.

Haka kuma ya ce yana da kyau ƴansiyasa su fahimci cewa akwai matsalolin tsaron da ƙarfin soja kaɗai ba zai iya magance su ba.

Dole ya a sauya yadda ake fuskantar matsalolin ta hanyar amfani da ƙarfin soji, maimakon haka a mayar da hankali wajen magance tarin matsallin da ke haifar da matsalar tsaron'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Dakta Kabiru Adamu ya ce akwai abubuwan da ke haifar da matsalar waɗanda dole sai an magance su sannan a samu nasara.

Daga cikin abubuwan da ya ce suna haifar da matsalar tsaron sun haɗa da:

  • Talauci
  • Rashin ilimi
  • Yunwa
  • Rashin aikin yi
  • Rashin kula da kan iyakoki
  • Dumamar yanayi
  • Rashin hadin kai tsakanin ɓangarorin
  • Rashin goyon baya daga al'umma