Yadda ƴan Boko Haram ke amfani da TikTok wajen yaɗa manufarsu a Najeriya

Asalin hoton, Boko Haram
Mayaƙan Boko Haram da ISWAP da suke daɗe suna addabar yankin arewa maso gabas suna ta faɗaɗa ayyukansu - ciki har da amfani da kafofin sadarwa wajen yaɗa manufarsu tare da jan hankalin mutane zuwa shiga cikinsu.
Aƙalla mutum 100 ne mayaƙan masu ikirarin jihadi suka kashe a sabbin hare-haren da suka kai a watan Afrilu kaɗai, kamar yadda gwamnan Borno, wadda ta fi fama da rikice-rikicen mayaƙan tun daga shekarar 2009 ya bayyana, inda ya ƙara da cewa mayaƙan sun ƙwace wasu garuruwan jihar.
Haka kuma mayaƙan suna fitowa a kafar TikTok suna holen bindigoginsu da wasu makamai da kuɗaɗe, kamar yadda wasu faye-fayen bidiyo da kafar AFP ta tantance a watan na Afrilu.
Suna fitowa a bidiyoyin kai-tsaye ta hanyar amfani da wasu shafukan da suke yaƙi da abubuwan da suke bayyanawa da manufofin turawa kamar yadda tsohon shugaban ƙungiyar Abubakar Shekau ya riƙa yi a bidiyoyin da ya riƙa fitarwa a baya.
Ba tun yanzu ba ne ake samun ɓatagari suna amfani da TikTok wajen yaɗa manufofinsu.
"Ƴanbindiga ne suka fara," kamar yadda Bulama Bukarti, mataimakin shugaban gidauniyar Bridgeway da ke Texas ya rubuta a shafinsa na X. "Yanzu ƴan Boko Haram ma sun fara yin bidiyon kai-tsaye a TikTok - suna yaɗa farfagandarsu tare da kare abin da suke yi da ma yin barazana ga duk waɗanda suka kushe su."
Bulama ya ce wani ɗan Boko Haram ya taɓa yi wa Bukarti barazana a wani bidiyon da yanzu aka goge a TikTok saboda ya kushe ayyukan ƴan ƙungiyar.
Duk da cewa an fallasa tare da rufe wasu shafukan masu yaɗa manufofin ƴan ƙungiyar, yadda suke yin bidiyoyin kai-tsaye na ƙara jawo tsaiko wajen bibiyarsu da yunƙurin daƙile su.
Kakakin kafar TikTok ya ce akwai wahalar ƙididdige shafukan da suke da alaƙa da ƙungiyoyin ta'addanci da suke goge.
Duk da cewa an goge irin shafukan da dama, har yanzu akwai wasu ire-irensu da dama kamar yadda AFP ta lura a lokacin haɗa wannan rahoton.
"Ƴan ta'adda da abubuwan da suke da alaƙa da ƙungiyoyinsu ba su da mafaka a TikTok, kuma muna ɗaukar matakin ba sani ba sabo kan masu yaɗa irin waɗannan manufofin a kafarmu," kamar yadda kakakin kamfanin TikTok ya shaida wa AFP a saƙonsa ga kafar ta email.
'Suna samun nasara'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Daga cikin shafuka 19 da AFP ta nazarta, ana ganin wasu mutane a shiga irin ta malamai, wasu fuskokinsu a buɗe suna kira a yi adawa da gwamnati.
Wasu shafukan suna nuna tsofaffin bidiyoyin tsohon shugaban Boko Haram Mohammed Yusuf da na Isah Garo Assalafy wanda aka haramta masa wa'azi a bainar jama'a a jihar Neja saboda yana amfani da kalaman ƙiyayya da adawa da dimokuraɗiyya da al'adun turawa.
Shafukan suna yawan yaɗa manufofinsu ne kai-tsaye suna tattaunawa da mabiyansu, suna amsa tambayoyi tare da amsar kyautattuka na kadarorin intanet da za su iya canjawa zuwa kuɗi.
Yaƙin Boko Haram, wanda ya yi shekaru ana fafatawa, ya ci sama da mutum 40,000, sannan ya raba miliyoyin mutane da muhallinsu a Najeriya.
Saddiku Muhammad, tubabben ɗan Boko Haram ne, ya shaida wa AFP cewa mayaƙan sun fara komawa TikTok saboda jami'an tsaro suna daƙile harkokinsu a kafar Telegram.
Haka kuma sun fahimci cewa akwai ɗimbin matasa a kafar TikTok a yanzu.
"Mayaƙan sun gane cewa domin jan hankalin matasa, akwai buƙatar su yi amfani da abin da matasan suke so - maimakon hanyar wa'azin rara-gefe wanda matasan ba sa fahimta," in ji Muhammad.
"Da alama kuma suna samun nasara. Manufofinsu na zuwa ga matasa, waɗanda za su iya ruɗarwa su ja su."
'Ba sa jin tsoro'
Masana sun shaida wa AFP cewa amfani da TikTok da mayaƙan suke yi babban ƙalubale ne ga gwamnati.
Malik Samuel, masanin harkokin tsaro ne a cibiyar masana ta Good Governance Africa da ke Abuja, ya ce daga cikin hanyoyin da Boko Haram ke bi wajen jan hankalin matasa akwai yaɗa farfaganda.
"Da gangan suke bayyana fuskokinsu - domin nuna cewa ba sa jin tsoro sannan su nuna wa mutane cewa suma mutane," in ji Samuel.
Ya ce tsagin ISWAP sun fi nuna ƙwarewa wajen fitar da bidiyoyinsu da tsare-tsarensu sama da mayaƙan Boko Haram wajen fitar da bidiyoyin a TikTo.
Sai dai kamfanin TikTok ya ce yana haɗa hannu da wani kamfanin sadarwa na Birtaniya mai suna Tech Against Terrosm wajen ƙara ɓullo da hanyoyi ganowa tare da goge shafukan da suke yaɗa manufofin ta'addanci.










