Yaya shirin sake mayar da tubabbun mayaƙan Boko Haram cikin al'umma yake?

Mutane sanya da farin kaya da koriyar hula zaune a kujera

Asalin hoton, OTHERS

Lokacin karatu: Minti 4

Rundunar sojin Najeriya ta ce za ta aiwatar da shirin sakin tubabbun mayaƙan Boko Haram da aka sauya wa tunani har su 381 inda za a mayar da su rayuwa cikin sauran al'umma gama-gari.

Haka kuma rundunar sojojin ta buƙaci gwamnatocin jihoin da za a danƙa wa mutanen da su ɗauki matakan samar musu da aikin yi.

Za a sake gudanar da wannan shirin ne a yanzu bayan kwashe shekara kusan goma da fara fito da shi, lokacin da tsofaffin mayaƙan na Boko Haram, su kusan 2,190 suka tuba, inda gwamnatin da ta shuɗe ta Shugaba Muhammadu Buhari ta fito da shi.

Zuwa yanzu dai ana ganin dubban tsofaffin mayaƙan ƙungiyar ta Boko Haram ne suka ci gajiyar wannan shiri na sake mayar da su cikin al'umma bayan sun zubar da makamansu, an ba su horo na sauya musu tunani da kuma shigar da su al'umma

Yaya shirin yake?

Shiri ne wanda a tsari na samar da zaman lafiya a ƙasar da ke fama da rikici da wuya a iya samun dauwamammen zaman lafiya ko zaman lafiya na tsawon lokaci ba tare da samar da irin wannan tsari ba na sake shigar da tsofaffin mayaƙa da suka tuba cikin al'umma.

Yawanci wannan shiri ne da ake aiwatarwa bayan yaƙi ko rikici ya ƙare to amma a wannan da hukumomin sojin Najeriya suka ɓullo da shi duk da cewa ya dace to amma ana ganin rikicin bai ƙare ba to amma ya dace, amma kuma sai dai a yi amfani da dabaru da suka fi dacewa da yanayin rikicin na Najeriya, wanda bai ƙare ba, domin a 2015 an ƙiyasta cewa ana buƙatar sama da dala biliyan tara wajen aikin sake gina yankin arewa maso gabas, yanklin da ke zaman cibiyar Boko Haram.

An yi hasashen cewa zuwa shekara ta 2030 idan har rikicin ya ci gaba za a buƙaci dala biliyan 30 a sake gyara yankin da rikicin ya lalata.

Har zuwa wannan lokaci ba za a ce an gama da ƙungiyar ta Boko haram ba kacokan.

To amma duk da haka an gudanar da irin wannan shiri a baya na yafe wa tubabbun mayaƙan ƙungiyar tare da sake sauya musu tunani da kuma mayar da su cikin al'umma, wanda wannan babban mataki na wanzar da zaman lafiya a inda ake fama da rikici.

Ƙalubalen shirin a Najeriya

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A matsayin wannan shiri na zaman wata hanya ta tabbatar da zaman lafiya, sake shigar da tubabbun na Boko Haram cikin al'umma bayan sauya musu tunani ya fuskanci ƙalubale da dama da ke zama tarnaƙi ga nasararsa amma duk da haka ba za a ce an karaya ba.

Ana ganin rashin aikin wannan shiri kamar yadda ya kamata a Najeriya ya haifar da fargaba da damuwa a tsakanin al'umma.

Wannan matsala kuwa ta kasance sakamakon ƙarancin wayewa da fahimtar batutuwan da suka shafi shirin.

A sakamakon haka akan samu yanayi na fargaba da damuwa, da tsoro da neman ramuwar-gayya a cikin al'ummar da aka nemi aiwatar da wannan shiri.

Saboda haka akwai buƙatar yin aiki gagarumi a kan su tubabbun mayaƙan na Boko Haram kan daidaita tunani da fahimtarsu ta koma ta zama irin ta al'ummar da za a mayar da suu cikinta su rayu, tare da yi musu tanadi na tattalin arziki.

Haka su ma kuma al'ummar da za ta karɓe su sai ta samu faɗakarwa yadda ya kamata kan zama da mutanen da a da suka kasance abokan gabarsu ko ma suka hallaka masoya da 'yanuwansu.

Bincike ya nuna cewa yawanci al'umma sun fi maraba tare da tallafa da kuma mu'amulla da matan da suka tuba fiye da mazan ƙungiyar ta Boko Haram.

Wannan ya nuna cewa duk da yadda jama'a ke nuna goyon bayansu ga shirin sake shigar da tubabbun mayaƙan na Boko Haram, jama'a na ɗari-ɗari da maza saboda fargaba da tsoro bisa ga dukkan alamu.

Yayin da yawancin mutane ke fatan ganin an sake shigar da tubabbun mayaƙan cikin al'umma sun ci gaba da rayuwa, akwai wasu 'yan ƙalilan ɗin jama'a da ke nuna ganin ya kamata a ɗauki matakan kare su daga ramuwar-gayya.

Sannan kuma akwai ɗaiɗaikun tsofaffin mayaƙan da aka shigar cikin al'umma bayan an yi musu duk wani horo na raba su da wannan aƙida da kuma tunani, amma suke komawa ruwa daga baya.

Wannan ma ana ganin wata matsala ce da jama'a kan nuna rashin yarda da wasu tubabbun mayaƙan wanda hakan ke sa ake ɗari-ɗari da su da rashin karɓarsu hannu bibbbiyu.