KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 19/01/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 19/01/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Haruna Kakangi da Ahmad Bawage

  1. Ƴanbindiga sun yi garkuwa da aƙalla mutum 160 a coci a Kaduna

    Bindiga

    Asalin hoton, Getty Images

    A jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya, rahotanni sun nuna cewa wasu ƴanbindiga sun yi garkuwa da sama da mutane 160 a wasu coci-coci da ke ƙauyen Kurmin Wali a ƙaramar hukumar Kajuru a jihar.

    Lamarin dai ya auku ne jiya Lahadi, lokacin da mutanen ke ibada a coci da ke ƙauyen.

    Shi ma shugaban ƙungiyar kiristoci ta Najeriya CAN, reshen jihar Kaduna Reberan Joseph John Hayab ya tabbatar wa jaridar Daily Trust aukuwar lamarin.

    Ya ce, "duk da cewa ban cika son ambata adadi ba, amma bayanan da na samu daga yankin na nuna cewa ƴanbindiga sun sace kusan mutum 172, amma guda 9 sun tsere sun koma gida, amma har yanzu ana neman mutum 163," in ji shi.

    Ya ce ko ma dai mene ne maƙasudin sace mutanen, "ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba. Za mu ci gaba da ba jami'an tsaro da gwamnati haɗin kai domin tabbatar da ceto mutanen."

    Har zuwa lokacin haɗa wannan labarin dai gwamnatin jihar Kaduna da rundunar ƴansandan jihar ba su ce komai ba.

  2. Shugaban Saliyo ya nemi afuwar waɗanda yaƙin basasa ya shafa bayan shekaru 24

    ...

    Asalin hoton, ISSOUF SANOGO/AFP/Getty Images

    Shugaban ƙasar Saliyo, Julius Maada Bio ya nemi afuwar waɗanda yaƙin basasa ya shafa bayan shekaru 24 inda ya amince da irin azaba da wahalhalun da al’umma suka fuskanta a lokacin da rikici ya addabi ƙasar daga shekarar 1991 zuwa 2002.

    Yaƙin ya yi sanadiyar mutuwar ɗaruruwan dubban mutane tare da barin dayawa da raunuka masu tsanani.

    Da yake jawabi a ranar Lahadi, shugaba Bio ya ce yana neman afuwa “a madadin ƙasa baki ɗaya,” yana mai amincewa da raɗaɗin da waɗanda suka tsira da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu suka fuskanta.

    Ya ce lokaci ya yi da ƙasar za ta fuskanci abin da ya faru domin samun warkarwa da haɗin kai.

    Jawabin ya zo ne a yayin bikin Ranar Tunawa ta Ƙasa ta farko ga waɗanda suka mutu a yaƙin basasar, inda wasu tsoffin sojoji, waɗanda aka yanke musu gaɓoɓi da sauran waɗanda rikicin ya shafa suka taru a tsohon ginin kotun musamman ta zaman lafiya a babban birnin ƙasar domin girmama waɗanda suka rasu.

    Ana ɗaukar yaƙin basasar Saliyo, wanda ya yi sanadiyar mutuwar kusan mutum 120,000 tare da raunata da nakasa dubban mutane, ana ɗaukarsa a matsayin ɗaya daga cikin mafi munin rikice-rikicen zamani.

    Rikicin ya ɗauki tsawon shekaru goma, kuma ya ƙare a hukumance a ranar 18 ga Janairu, 2002.

  3. Sifaniya ta ayyana makokin kwana uku bayan hatsarin jirgin ƙasa da ya kashe mutum 39

    ...

    Gwamnatin Sifaniya ta ayyana makokin kwana uku a ƙasa baki ɗaya bayan mummunan hatsarin jiragen ƙasa biyu da suka yi taho mu gama da juna a kudancin ƙasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutum 39, tare da jikkata wasu da dama.

    Hatsarin ya faru ne lokacin da wani jirgin ƙasa mai sauri da ke kan hanyarsa daga Malaga zuwa Madrid ya kauce daga layinsa, inda ya shiga ɗaya layin dogo da wani jirgin ke tafiya a kai, abin da ya jawo karon.

    Firaiministan Sifaniya, Pedro Sanchez, ya bayyana lamarin a matsayin abin tashin hankali da kaɗuwa, yana mai miƙa sakon ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu tare da fatan samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata.

    Masu aikin ceto sun ce kai wa ga fasinjojin da suka maƙale a cikin jiragen na da matuƙar wahala, sakamakon yadda jiragen suka lotse bayan karon, yayin da ake ci gaba da aikin ceto da kula da waɗanda suka jikkata a asibitoci.

  4. ‘Yansanda sun fara farautar ƴanbindigar da suka kai hari a kamfanin Aqua Triton a Oyo

    ...

    Asalin hoton, NPF

    Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta fara farautar wasu ‘yan bindiga da suka kai hari kan kamfanin Aqua Triton da ke Ogunmakin, kusa da Ibadan a Jihar Oyo.

    Rahotanni sun ce mahara sun far wa rukunin kamfanin ne a wani samame na ba zata, inda suka kashe wani jami’in ‘dan sanda da ya yi ƙoƙarin dakile su, sannan suka yi awon gaba da wani ɗan kasar China wanda yake ɗaya daga cikin manyan daraktocin kamfanin.

    Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da farautar masu laifin tare da amfani da dukkan bayanai da shaidu da aka tattara domin kamo su cikin gaggawa.

    Rundunar ta ce jami'anta na aiki tukuru domin ganin an ceto ɗan Chinan da aka sace lafiya, sannan a hukunta wadanda suka aikata laifin bisa doka.

    Wannan lamari ya jefa ma’aikatan kamfanin cikin tsoro da damuwa, yayin da rundunar ke ƙoƙarin tabbatar da tsaro a yankin da rage yiwuwar aukuwar irin wannan harin nan gaba.

  5. Sojoji sun lalata sansanonin ƴanbindiga a Arewa maso Gabashin Najeriya

    ....

    Asalin hoton, Nigerian Army

    Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojin haɗin gwiwarta ta Operation haɗin kai da JTF a Arewa maso Gabashin ƙasar sun samu nasarori a gagarumin samamen da suka gudanar da ake kira da Operation DESERT SANITY, inda suka lalata sansanonin ‘yanbindiga da dama tare da ƙwace makamai da kayan yaƙi.

    Sojojin sun kuma daƙile hare-haren da aka shirya a yankin Timbuktu Triangle a lokacin samamen.

    Sanarwar da rundunar ta fitar wa manema labarai ta ce a ranar Lahadi, 18 ga Janairu, 2026, sojoji sun tashi daga wuraren da suke tsarewa inda suka gudanar da samamen bisa bayanan sirri a kan wasu sansanonin ‘yanbindiga da aka gano, ciki har da Chilaria, Garin Faruk da Abirma.

    A yayin samamen, an samu kwatar kayan soji da dama, ciki har da wayoyi, rediyo, harsasai, bindigogi na AK-47 guda 5, tutocin Boko Haram/ISWAP, kayan aikin noma, motar daukar kaya, da man fetur, da sauran kayayyakin yaƙi na ‘yanbindiga.

    Sojojin sun fuskanci harin jiragen sama marasa matuki daga ‘yanbindiga a lokacin samamen, amma hakan bai hana su ci gaba da gudanar da ayyukansu ba.

    Haka kuma, an dakile wani harin a yammacin ranar, wanda ya tilasta wa ‘yanbindiga ja da baya, abin da ya nuna cikakken rinjayar sojoji a yankin da kuma ƙarfin su wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

  6. Dubban mutane sun rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa a Mozambique

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Dubban mutane ne suka rasa muhallansu sakamakon mummunan ambaliyar ruwa a Mozambique lamarin da ya tilasta wa Shugaban ƙasar, Daniel Chapo, soke tafiyarsa zuwa taron tattalin arziki na Duniya da za a gudanar a Davos a wannan makon.

    Ambaliyar ta lalata manyan gine-gine tare da shafar dubban mutane a sassa daban-daban na ƙasar yayin da Mozambique ke shiga lokacin damina na shekara-shekara.

    Shugaban ya sanar da soke tafiyar ne a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, inda ya ce ƙasar “na cikin mawuyacin hali kuma mafi muhimmanci a wannan lokaci shi ne ceto rayuka.”

    Aƙalla mutane 95 ne suka rasa rayukansu tun lokacin da ruwan sama mai ƙarfi ya fara tsakiyar Disamba adadin da hukumomi ke fargabar zai ƙaru yayin da ambaliyar ke ci gaba.

    An samu ambaliyar ruwa a manyan larduna na Maput da, Gaza da Sofala, wanda ya shafi rayuwar dubban mutane

    Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da harkokin jin kai (OCHA) ya ƙiyasta cewa fiye da mutum 400,000 abun ya shafa kuma ana sa ran wannan adadi zai ƙaru yayin da ruwan sama ke ci gaba.

  7. An kama ƴan Najeriya 53 da zargin aikata laifukan intanet a Ghana

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin tsaron Ghana sun cafke mutum 53 da ake zargi da aikata manyan laifukan intanet a wani gagarumin samame da suka kai cibiyoyin aikata laifukan intanet a birnin Accra da kewaye.

    Daga cikin waɗanda aka kama, an bayyana mutum 44 a matsayin waɗanda aka yaudare su aka shigar da su ƙasar da sunan samun aiki yi amma aka tilasta musu aikata laifukan intanet, amma kuma an samu nasarar ceto su.

    Rahotanni sun nuna cewa dukkan mutanen 53 da aka kama ’yan Najeriya ne.

    A cewar hukumomin, samamen na tsawon kwanaki biyu wanda aka gudanar bisa sahihan bayanan sirri, ya haɗa Hukumar tsaron Intanet ta Ghana da sauran hukumomi.

    A yayin aikin, an ƙwato kwamfutoci tafi-da-gidanka 62, wayoyin hannu 52 da kuma bindigogi biyu. Haka kuma, an kama mutum tara da ake zargi su ne jagororin ƙungiyar aikata laifukan.

    Hukumomi sun ce yaudarar mutanen wasu ƙasashe,da alkawarin basu ayyukan yi masu tsoka amma daga bisani a ƙulle su a gidaje, a ƙwace takardun tafiyarsu tare da tilasta musu aikata laifukan intanet kamar damfara ta soyayya, da satar kuɗi ta banki da sauransu ya zama ruwan dare a Ghana

    Ministan Sadarwa na Ghana, Sam George, ya bayyana a shafinsa na X cewa dukkan waɗanda aka cafke an tantance su tare da miƙa su ga Hukumar Shige da Fice ta Ghana domin tsaro da ƙarin bincike.

  8. Tinubu ya yi alhinin rasuwar ɗan kasuwar Kano Bature Abdulaziz

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhini da jimami kan rasuwar fitaccen ɗan kasuwa kuma jagoran al’ummar ’yan kasuwa a Jihar Kano, Alhaji Bature Abdulaziz, wanda ya rasu a ƙarshen mako.

    Cikin wata sanarwa da fadarsa ta fitar, Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ga al’ummar ’yan kasuwa a Kano da iyalan marigayin, da gwamnatin Jihar Kano bisa wannan babban rashi.

    Shugaban ya bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi ba ga al’ummar kasuwancin Kano kaɗai ba, har ma da sassa da dama na Najeriya, duba da tasirinsa a harkokin kasuwanci.

    A cewar Tinubu, marigayi Bature Abdulaziz ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa harkokin kasuwanci a ƙasar, inda ya shugabanci ƙungiyoyi da dama masu alaƙa da kasuwanci.

    Kafin rasuwarsa, shi ne Shugaban Ƙungiyar ’Yan Kasuwa ta Najeriya tare da bayar da gudunmawa mai yawa wajen haɗa kan ’yan kasuwa a faɗin ƙasa.

    Tinubu ya kuma tuna da irin goyon bayan da marigayin ya ba shi a lokacin yaƙin neman zaɓensa a shekarar 2023, tare da rawar da ya taka wajen inganta haɗin kan ƙasa da kishin ƙasa ta hanyar ƙungiyar Patriotic Elders Network for Peace (PENP) da ya kafa.

  9. Yoweri Museveni ya sake lashe zaɓen shugabancin Uganda

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban ƙasar Uganda wanda ya jima yana mulkin ƙasar, Yoweri Museveni, ya sake samun nasarar lashe zaɓen shugabancin ƙasar bayan ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen da aka gudanar da kashi 71.6 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa.

    Hukumar zaɓen ƙasar ta bayyana sakamakon ne bayan kammala ƙirga ƙuri’u.

    Babban abokin hamayyarsa, jagoran adawa, Bobi Wine dai ya ƙi amincewa da sakamakon zaɓen, inda ya bayyana shi a matsayin na bogi.

    Bobi Wine ya ce sakamakon bai wakilci haƙiƙanin ra’ayin al’ummar Uganda ba, tare da zargin maguɗi a zaɓen.

    Museveni ya gudanar da yaƙin neman zaɓensa ne bisa abin da ya kira nasarorin gwamnatinsa, inda ya yi alƙawarin ci gaba da samar da zaman lafiyar siyas da, bunƙasa tattalin arziƙi da kuma ƙoƙarinsa na mayar da Uganda ƙasa mai matsakaicin kuɗin shiga nan da shekarar 2030.

    Sai dai masu sa ido kan al’amuran siyasa na ganin cewa shekaru biyar masu zuwa, wanda ake hasashen zai zama wa’adinsa na ƙarshe, za su fi karkata ne kan batun miƙa mulki

  10. Tinubu ya yi tir da kisan mace da ƴaƴanta shida a Kano

    Tinubu

    Asalin hoton, Fadar shugaban Najeriya/X

    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kakkausar suka kan kisan gilla da aka yi wa wata matar aure mai suna Fatima Abubakar, da ƴaƴanta shida a unguwar Chiranci da ke Jihar Kano.

    Cikin wata sanarwa da fadarsa ta fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana lamarin a matsayin mummunan rashin imani da rashin tausayi, wanda ya girgiza al’umma da ma ƙasa baki ɗaya kuma ya saɓa wa ƙa’idojin bil’adama.

    Tinubu ya nuna matuƙar alhini kan wannan mummunan iftila'in, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan.

    Shugaban ya kuma yaba wa rundunar ƴansandan Najeriya bisa gaggawar ɗaukar matakin da ya kai ga kama manyan waɗanda ake zargi da aikata laifin.

    Ya umarci hukumomin tsaro da su tabbatar da gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a cikin kisan a gaban kotu.

  11. Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin da zai jagorancin shari'ar kisan mace da ƴaƴanta 6

    ...

    Asalin hoton, FACEBOOK/Abba Kabir Yusuf

    Gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta jagoranci shigar da ƙara kan kisan gillar da aka yi wa wata matar aure da ƴ aƴanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi da ke birnin Kano, lamarin da ya jefa al’ummar jihar cikin alhini da girgiza.

    Gwamnatin ta bayyana kisan a matsayin mummunan aiki na rashin tausayi da rashin imani wanda ya girgiza zukatan al’ummar jihar tare da zama babban cin zarafi ga bil’adama da doka.

    A cikin wata sanarwa da babban lauyan jihar kuma kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru Maude, SAN ya ce bisa umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf, gwamnatin jihar ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan mamatan da daukacin al’ummar Kano.

    ''Gwamnati na tare da iyalan da abin ya shafa, tare da tabbatar musu da cewa ba za a barsu su kaɗai ba a wannan mawuyacin lokaci," in ji sanarwar.

    Gwamnatin ta yaba wa rundunar ƴansandan jihar bisa gaggawar ɗaukar matakin bincike da ya kai ga kama manyan waɗanda ake zargi da aikata laifin.

    A cewar sanarwar, wannan mataki na nuna ƙudirin hukumomin tsaro na tunkarar aikata laifuka da dawo da amincewar jama’a ga tsaro da adalci.

    Gwamnatin ta jaddada cewa za a gudanar da shari'ar cikin gaggawa da ƙwarewa ta hannun Ofishin Babban Lauyan Jihar, inda za a kafa tawagar lauyoyi ta musamman domin tabbatar da adalci.

  12. Gobara ta laƙume shaguna a tsohuwar kasuwar Sokoto

    Wata gobara da ta tashi a safiyar Lahadi ta sanadiyyar wutar lantarki ta ƙone shaguna da dama a tsohuwar Kasuwar jihar Sokoto.

    Gobarar ta lalata kaya da dukiyoyi da darajarsu ta kai miliyoyin naira.

    Hukumar ba da agajin gaggawa ta Ƙasa (NEMA) reshen Sakkwato ta ce tawagar gaggawarta ta garzaya wurin nan take bayan samun rahoton lamarin, tare da haɗin gwiwar Hukumar SEMA da Sashen Kashe Gobara.

    NEMA ta ce haɗin gwiwar hukumomin ya taimaka wajen shawo kan gobarar tare da hana ta yaɗuwa zuwa sauran sassan kasuwar.

    NEMA ta ce za ta ci gaba da fitar da ƙarin bayani game da lamarin yayin da ake samun sababbin bayanai.

  13. Mutum 39 sun mutu a hatsarin jirgin ƙasa a Sifaniya

    Jirgin ƙasa

    Asalin hoton, Reuters

    Akalla mutum 39 sun rasa ransu sannan wasu da dama sun jikkata bayan wasu jiragen ƙasa biyu sun yi taho mu gama da juna a kudancin Sifaniya.

    Ɗaya daga cikin jiragen na kan hanyarsa ne daga Malaga zuwa Madrid inda ya kauce wa hanyarsa, ya koma kan ɗaya layin dogon da a nan ne suka yi karo da wani jirgin da ke tafiya a kan layin dogon.

    Firaiministan Sifaniya, Pedro Sanchez ya bayyana lamarin a matsayin abin tashin hankali da kaɗuwa.

    Ministan harkokin sufuri na ƙasar ya ce har yanzu ba a san dalilin da ya sa jirgin ya kauce daga hanyarsa ba.

    Tuni dai masu aikin ceto suka ce kai wa ga waɗanda suka makale a cikin jirgin na wahala saboda yadda jiragen suka lotse.

  14. Waɗanne makamai Najeriya ke buƙata don yaƙi da ƴanbindiga?

    ....

    Asalin hoton, Reuters

    A makon da ya gabata ne Amurka ta sanar da kai wa Najeriya makaman yaƙi a wani wani mataki na taimaka wa ƙasar yaƙi da ƴanbindiga.

    Masu sharhi da ƴanƙasar da dama sun jima suna kokawa kan rashin wadatattun makamai ga jami'an tsaron ƙasar.

    A lokuta da dama an sha jin wasu jami'an tsaron ƙasar na ƙorafin rashin isassun makamai a matsayin ɗaya daga cikin matsalolin da suke fuskanta.

    Ƴanbindigar kan yi amfani da manyan makamai na zamani da ba kowane jami'in tsaro ke riƙewa ba.

    Hakan ya sa wasu ke ganin akwai buƙatar samar wa dakarun tsaron ƙasar wadatattun makamai na zamani domin daƙile ayyukan ƴanbindigar.

  15. China ta cimma burinta a fannin tattalin arziki a bara

    Tattalin arzikin ya haɓaka da kashi biyar cikin 100, kodayake yana cikin matakin da gwamnati ta yi hasashe.

    Sai dai tattalin arzikin ya nuna tafiyar hawainiya a bara, karon farko a tsawon gomman shekarun da aka jima ba.

    Matakin ya nuna raguwar da aka samu a kasuwanni cikin ƙasar.

    A makon daya gabata, Beijin ta rawaito cewa irin ribar da ta samu a wasu kayayyaki da ta siyar ko ta kai wasu ƙasashen duniya.

    To amma a cikin ƙasar ana ci gaba da samun faɗuwa musamman a ɓangaren cinikin gidaje.

  16. Lale maraba

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar Litinin, Mande tushen aiki ko da nasara na tsoronki, kamar yadda Hausawa ke yi mata kirari.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku kasance da mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa