'Ƙone Dajin Sambisa ne kawai zai hana tubabbun ƴan Boko Haram komawa ruwa'

Asalin hoton, OTHERS
Wani mai sharhi kuma malami a Jami'ar Maiduguri a Najeriya ya ce ƙone Dajin Sambisa ƙurmus ne kawai abin da ya fi dacewa don hana mayakan Boko Haram da suka miƙa wuya ga gwamnati komawa ruwa.
Dakta Abubakar Othman ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da sashen BBC Hausa, a daidai lokacin da ake fargabar sake komawa ruwan mayaƙan da a yanzu haka suke ta tururuwar miƙa wuya ga gwamnati da nufin sun tuba.
Mayakan Boko Haram din suna ta wannan tuba ne da ajiye makamansu bayan shafe shekara 12 ana fama da tashe-tashen hankula da kashe-kashe a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Malamin ya ce cikin ƙanƙanin lokaci za a iya shafe tarihin Dajin Sambisa don a hana gurɓatattu samun mafaka.
Dr Othman ya ce "lamarin nan ya daɗe, yau wajen shekara 11, yau ne gobe ne haka dai. Rayuka sun salwanta an kuma yi asarar dukiyoyi, ba zaman lafiya haka ake ta tafiya."
Ya ce abu biyu ya kamata a duba kan wannan batu na karɓar tubabbun ƴan Boko Haram da gwamnati ke ci gaba da yi.
"Idan har su da kansu sun ce sun bari sun tuba, to abu na farko da ya kamata a yi shi ne a karbe su ɗin. A ce mun ji kun tuba mun karɓe ku, kamar dai yadda gwamnan Borno ya fada, a fara karbar tasu shi ne matakin farko.
"Don ba a son yaƙi ko ci gaba da faɗa da su. Idan sun shiga hannu an karbe su sai abu na gaba a san me za a yi a kansu."
Mai sharhin ya ce to a nan ne gizo ke saƙar, "abin da nake nufi shi ne a tantance don gane ko tuban ne da gaske ko takura ce ta sa suka fito daga dajin suke so su sha iska su koma.
"Don haka dole ne a yi amfani da ƙwararru a fannin gano masu aikata miyagun laifuka da masana halayyar dan adam da na fannin lafiyar ƙwaƙwalwa da sauransu don yin nazari.
"A yi hira da su don gano inda suka sa gaba," in ji shi.
Hukumomi sun ce fiye da tsofaffin 'yan kungiyar dubu takwas ne suka mika wuya, cikinsu har da mata da kananan yara, kuma bayanai na cewa har yanzu daruruwa na ci gaba da mika wuya.
A yanzu haka dai ana killace da mutanen a wasu sansanonin hukuma a birnin Maiduguri na jihar Borno.
Sai dai masanin ya bayyana damuwa cewa idan haka kawai aka karɓe su har aka gina musu gidaje, "ni kuma su ne fa suka ƙone min gidana suka kashe min 'yan uwa, sannan a karrama su fiye da ni ai ka ga da sauran rina a kaba," kamar yadda ya ce.
Mai sharhin ya ce dole a sanya tababa kan lamarin, ganin sun shafe shekaru a daji suna yakar mutane kuma rana tsaka su fito su ce sun mika wuya.

Asalin hoton, Getty Images
Dalilansu na miƙa wuya
Dokta Othman ya bayyana abubuwan da yake ganin su ne suka sa su mika wuya kamar haka:
- Walau dai dajin ya musu zafi
- Ko kuma da gaske sun ga babu sarki sai Allah ne suka mika wuyan
- Watakila don sun ga abin ya fi karfinsu
- Ko kuma don an kashe shugabanninsu
- Ko don hanyar samun abincinsu duk ta toshe
- Ko kuma don sun ga kowa ma ya gaji da su
- Na biyu masanin ya ce ta iya yiwu dama can sun fada cikin harkar ne bisa rashin fahimta ko cikin maye.
"Sun yi tsammanin a lokaci ƙanƙani komai zai so karshe sai suka ga tafiyar ba mai ƙarewa ba ce."
Na uku in ji Dr Othman sauya salon da gwamnati Babagana Zulum ta yi na zuwa da sabuwar basira ma ya taimaka.
"Ya zo da kamanta gaskiya da mai yiwuwa a baya ba su ga hakan ba. Yanzu kuwa watakila sun gane shi idan ya ce zai yi abu to yana nufin hakan ne.
"Shi din kamar ya fahimci sirrin abin. To ganin hakan ya hadu da dama can ba so suke ba an ingaza su ne sannan sun dade suna wahala rashin mafita ne ya zaunar da su, yanzu kuma ga mafitar gara su miƙa wuya kawai," a cewar Malamin Jami'ar.
Yawanci dai irin wannan lamarin da miƙa wuyan mayaƙan da ka yaƙi da gwamnati da al'umma abu ne da yake buƙatar a yi cikin taka tsan-tsan.
Don haka ne ma masu sharhi ke ya kamata a killace su don gyara ɗabi'unsu kafin mayar da su cikin al'umma.
Masanin dai ya ce ya kamata a bi komai daki daki.
"Ya kamata a karkasa su tukun don akwai wadanda da gaske sun gaji da yakin dama kuma ba da son ransu suka shiga ba. Irinsu cikin sauki za a iya mayar da su cikin al'umma.
"Akwai wadanda su kuma abin ya shiga jikinsu sosai da ake bukatar a yi ta sauya tunaninsu tsawon lokaci kafin a kai su cikin mutane.
"Gaskiya abin zai dau lokaci saboda ko ni idan na ga wanda ya kashe min wani dan uwana ai ba lallai na iya barinsa ba. Hakkin sakin nasu ba a kan gwamnati ba ne kawai."
'Ba duka tubabbun ba ne ƴan jihar Borno'

Amma ya yaba wa matakin da gwamnatin Bornon ta dauka kwanan nan na yin sulhu da al'ummomin da abin ya shafa inda ake ba su hakuri da cewa su daure su karbi tubabban don idan ba a karbe su ba ba a san halin da za su iya fadawa ba kuma.
Sai dai ya ce Inda aka samu kuskure kawai shi ne an dauka kamar dukkan maɓarnatan 'yan jihar Borno ne ko kuma a can kawai aka yi rikicin.
"Ya kamata a tuntubi har da 'yan Yobe da Adamawa da Gombe don duk faɗan ya zaga can.
"Barnar nan ba a Maidiguri ko jihar Borno kawai aka yi wa ba. Abin ya fi karfin Borno ita kadai," ya ce.
Ya ce kamata ya yi a duba kowa a gano daga inda ya fito sai a mayar da su jihohinsu.
Ya kara da cewa: "Ni na tabbata ba 'yan Borno ne kawai a cikinsu ba. Kowace jiha a bar ta ta dauki nauyin nata mutanen."
Me ya kamata al'ummar da aka bata wa su yi?
Dr Othman na ganin ya kamata gwamnati ta dinga sara tana duban bakin gatari, wato idan tana duba su masu tuban to ta kuma duba wadanda aka yi wa laifin ma.
"Ko ni nan na yi manyan asarori a dalilin rikicin. Ya kamata gwamnati ta yi duba kan al'ummomin da bala'in nan ya shafa ta gane cewa su ma suna son tallafi don sun yi asara sosai," a cewarsa.
Amma duk da haka ya bayyana cewa afuwa da sulhu sun fi komai alkhairi a lokuta da dama, don haka yana ganin akwai rawar da al'ummoin da aka ɓatawa za su yi.
- Na farko su bar wa Allah tun da sun yarda kaddara ce kuma ga shi har sun tsira da rayukansu.
- Na biyu a tuna baya kan wani abin da su ma suka yi. "Ai a matakin farko na fadan ai mambobinsu da muke zaune da su a nan su suka fara kare mu ma. Kafin daga baya wasu da suka zo daga sauran wutare suka far mana.
- Na uku kamar yadda na ce gwamnati ta san cewa an yi mana barna kuma a yi mana abin da ranmu zai dan kwanta. Sai ka ga mu ma mun yafe.

Asalin hoton, HQNIGERIANARMY
To ko mene ne tunanin masana kan mata da kananan yaran da suka mika wuya na kungiyar?
Dr ya ce "Yara kam watakila ma a ciki aka haife su amma mata akwai wadanda sosai 'yan Boko Haram din ne.
"Don haka sai su ma a tantance su a gano ainihin mata sojonin Boko Haram da suka yi yaki bisa son ransu, sai kuma a ware wadanda tilasta musu aka yi, a ware wadanda sace su aka yi.
"Sai kowa ya san wadanda za a sallama da wuri da wadanda za a gyarawa ɗabi'a," Dr ya ƙara da cewa.
Dawowar wadannan mutane cikin al'umma na nufin za su dinga fuskantar tsangwama sosai daga wajen al'umma, amma masana na ganin hakan bai dace ba
Dr ce kamata ya yi idan dai hukumomi suka kammala tantance su aka mai da cikin mutane to a guji tsangwamarsu don hakan ba dadi.
"Idan akwai tsangwama kenan zaman ɗarɗar zai shigo ka ga kenan ba za a saki jiki a zauna lafiya ba.
"Su kuma tubabbun sai kar su nuna halaye na shakku su koma halayen mutanen kirki da aka sani kamar yadda suke a can baya."
Ƙone Dajin Sambisa ƙurmus

Asalin hoton, NIGERIAN ARMY
Wata fargabar da ake da ita kuma ita ce kar tarihi ya maimaita kansa na abin da ya faru a baya inda bayan mayakan suka mika wuya daga baya sai suka koma daji.
Malam ya ce idan dai har Dajin Sambisa yana nan to za su koma, "sai dai da wuya hakan ta faru saboda ai dajin ya ci wuta ya musu zafi komawar za ta yi wuya," in ji shi.
Wata tambayar da ke nukurkusar 'yan Najeriya ita ce ko miƙa wuyan da mayakan ke yi da kashe Abubakar Shekau da kashe Al-Barnawai da ake rade-radi zai iya kawo karshen Boko Haram?
Malam Othman ya ce kwarai wadannan alamu ne na fara ganin karshen Boko Haram.
"Amma abin da zai hana wadannan tubabbun koma wa dajin shi ne gara a yi rugu-rugu da dajin.
"Dajin Sambisan nan cikin awa 24 za a iya ƙone shi ƙurmus dama ba shi da wani amfani na tattalin arziki. A ƙone shi ƙurmus a gina barikin sojoji a wajen.
"Su din ma tubabbun sai a yi musu gidaje ta wajen ya zama babu dajin buya."
Ya jaddada cewa hakan zai yiwu ne kawai idan aka hada kai tsakanin gwamnatocin jihohin arewa maso gabashin Najeriya.
Sai dai wannan batu na Dakta abu ne da zai iya jawo tarnaki daga wajen masu kare muhalli.
Amma ya ce "dazuzzukan da ake ta samun gobararsu a manyan kasashen duniya da suka ƙone ƙurmus me ya faru? Ai babu komai.
"Ai idan aka yi ƙurmus da shi ma sabbin abubuwa ne za su tsuro a wajen.
"Sambisa ba shi da amfanin da ya wuce a ƙone shi.
"Ba shi da wani amfani da ya wuce a gina abubuwan more rayuwa a wajen," ya jaddada.











