Yadda rarrabuwar kawuna ke ɓulla tsakanin shugabannin Taliban

Asalin hoton, AFP via Getty Images
- Marubuci, BBC Afghan
- Lokacin karatu: Minti 16
Wata murya da aka naɗa da BBC ta samu ne ya bayyana abin da ya fi damun shugaban na Taliban.
Ba wani abu da ke yi barazana daga waje ba ne, amma abu ne da ke bayyana daga cikin Afghanistan, wanda Taliban suka ƙwace iko da shi yayin da gwamnatin da ta shuɗe ta ruguje sannan Amurka ta fice a 2021.
Ya yi gargadin cewa akwai "wadanada ke cikin gwamnati" da ke adawa da juna a masarautar Islama da Taliban ta kafa domin gudanar da mulkin ƙasar.
A cikin muryar da aka fitar, ana iya jin shugaban ƙoli Hibatullah Akhundzada yana jawabi yana mai cewa rashin jituwar cikin gida na iya kawo cikas a ƙarshe.
"Sakamakon wannan rarrabuwar kawuna, masarautar za ta ruguje," in ji shi.

Asalin hoton, AFP / Universal Images Group via Getty
Jawabin da aka yi wa ƴan ƙungiyar Taliban a wata makaranta da ke kudancin birnin Kandahar a watan Janairun shekara ta 2025, ya kara ruruta wutar jita-jitar da aka shafe tsawon watanni ana ta yaɗawa - jita-jitar bambance-bambance a shugabancin ƴan Taliban.
Rabe-rabe ne da a kodayaushe shugabannin Taliban ke musantawa - ciki har da lokacin da BBC ta tambaye su kai tsaye.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sai dai jita-jitar ta sa sashen na BBC na Afganistan ya fara gudanar da bincike na tsawon shekara guda kan wannan ƙungiya mai cike da sirri - inda ta gudanar da hirarraki sama da 100 tare da na yanzu da tsoffin ƴan Taliban da ma wasu majiyoyi na cikin gida da ƙwararru da tsoffin jami'an diflomasiyya.
Saboda haɗarin da wannan rahoton ke tattare da shi, BBC ta amince da kada a bayyana sunayensu domin kare lafiyarsu.
Yanzu, a karon farko, mun sami damar fayyace ƙungiyoyi guda biyu a cikin shugabannin Taliban - kowannensu yana gabatar da na shi taswirar ci gaban Afghanistan na daban.
Ɓangare ɗaya ya kasance mai biyayya ga Akhundzada, wanda daga sansaninsa na Kandahar, ya ke jagorantar ƙasar zuwa ga manufarsa ta kafa daular Musulunci - wadda ta ƙeɓance kanta daga sauran duniya, inda shugabannin addini da ke goyon bayansa ke iko da kowane ɓangare na rayuwar al'umma.
Sai ɓangare na biyu kuma, wanda ya ƙunshi ƴan Taliban masu ƙarfin faɗa a ji da ke Kabul babban birnin ƙasar, masu ra'ayin kafa ƙasar Afganistan wadda - yayin da take bin tsattsauran ra'ayin addinin Islama - tana harkoki da ƙasashen waje, tana gina tattalin arzikin ƙasar, har ma da bai wa ƴan mata da mata damar samun ilimin da a halin yanzu ake hana su bayan makarantar firamare.
Wani mai bincike ya siffanta wannan lamari da "Gidan Kandahar da Gidan Kabul".
To sai dai a kodayaushe abin tambaya shi ne ko ɓangaren na Kabul da ya ƙunshi ministocin majalisar ministocin Taliban, da masu faɗa a ji da kuma manyan malaman addini waɗanda ke samun goyon bayan dubban mayaƙan Taliban, za su taɓa ƙalubalantar Akhundzada mai ƙarfin iko ta kowace hanya mai ma'ana, kamar yadda jawabinsa ya nuna.
A cewar Taliban, Akhundzada shi ne cikakken shugaban ƙungiyar - mutum ne wanda daga Allah sai sshi kuma babu mai iyanƙalubaklantarsa.
Daga nan ne kuma aka yanke shawarar da za ta haifar da ta'azzarar kai-komon da ake yi tsakanin manyan masu faɗa a ji a ƙasar, wanda ya rikiɗe zuwa rikici na son rai.
A ƙarshen watan Satumba, Akhundzada ya ba da umarnin rufe intanet da wayoyi, lamarin da ya kyallace Afghanistan daga sauran ƙasashen duniya.
Bayan kwana uku aka dawo da intanet, ba tare da bayanin wani dalili ba.
Sai dai abin da ya faru a bayan fage ya janyio babban tashin hankali, inji wasu majiyoyi na cikin gida. Ɓangaren Kabul ta yi watsi da umarnin Akhundzada kuma ta sake kunna intanet.
"Taliban, ba kamar kowace jam'iyya ko ƙungiya ta Afganistan ba ce. Ta na da matuƙar haɗin kai - ba a samun rarrabuwar kawuna, ko rashin jituwa," in ji wani masani kan Afghanistan, wanda ke nazarin Taliban tun lokacin da aka kafa ta.
"Akwai aƙidar biyayya ga shugabanni a tattare da ginshikan ƙungiyar, kuma mafi girma shi ne Amir [Akhundzada]. Wannan shi ne abin da ya sa aikin mayar da intanet a baya, ya saɓawa umarninsa, abu ne da ya faru ba zato ba tsammani," in ji masanin.
Kamar yadda wata majiyar cikin gida ta Taliban ta ce: wannan lamari ne da ke kamanceceniya da tawaye.
Mutum mai kishin addini

Ba a wannan matakin Hibatullah Akhundzadam ya fara shugabancinsa ba.
Majiyoyi sun ce an zaɓe shi a matsayin shugaban ƙungiyar Taliban a shekarar 2016 saboda tsarin da ya ke da ita na tabbatar da haɗin kai.
Sakamakon rashin gogewarsa a fagen, ya sami wani mataimaki a Sirajuddin Haqqani - wani kwamandan mayaƙa da ake tsoro, sannan ɗaya daga cikin mutanen da Amurka ke nema ruwa a jallo wanda aka ɗaura ladar $10m (£7.4m) a kansa.
Ya samu wani mataimaki na biyu, Yaqoob Mujahid, ɗan wanda ya kafa ƙungiyar Taliban Mullah Omar – matashi ne, amma kasancewar yana da jinin shugabancin Taliban, yana da yiwuwar na haɗa kan ƙungiyar.
Haka ƙungiyar ta ci gaba da kasancewa a duk lokacin da ake tattaunawa da Washington a Doha don kawo ƙarshen yaƙin shekaru 20 tsakanin mayaƙan Taliban da sojojin da Amurka ke jagoranta. Yarjejeniyar ta ƙarshe, a cikin 2020, ta haifar da sake kwato ƙasar da Taliban suka yi, da kuma ficewar sojojin Amurka cikin ruɗani a watan Agustan 2021.

Asalin hoton, Los Angeles Times via Getty Images
A idon duniya, ƙungiyar ta kasance da kanta a haɗe.
Sai dai duk mataimakan biyu za su samu kansu a wani yanayi, inda aka rage masu matsayi zuwa ministoci jim kaɗan bayan Taliban ta koma kan karagar mulki a watan Agustan 2021, inda Akhundzada ya kasance shugaban ƙungiyar na gama-gari shi kaɗai kamar yadda wasu majiyoyin cikin gida suka shaida wa BBC.
Hatta Abdul Ghani Baradar - wanda ya ke cikin waɗanda suka kafa ƙungiyar Taliban, ya kuma jagoranci tattaunawa da Amurka - ya sami kansa a matsayin mataimakin firaminista maimakon firaminista kamar yadda mutane da yawa suka zata.
A maimakon haka, Akhundzada - bayan da ya kaurace wa babban birnin ƙasar da gwamnati ke zaune don ci gaba da zama a Kandahar, cibiyar iko ga Taliban - ya fara kewaye kansa da amintattun masu akidar tsatsauran ra'ayi.
An bai wa sauran masu biyayya ikon jami'an tsaron ƙasar, da manufofin addini da sassan tattalin arzikin ƙasar.
"[Akhundzada], tun daga farko, ya nemi kafa nasa ɓangaren," in ji wani tsohon ɗan Taliban - wanda daga baya ya yi aiki a gwamnatin Afghanistan da ke samun goyon bayan Amurka..
"Duk da cewa bai samu damar a karon farko ba, yana samun mulki, sai ya fara yin hakan cikin basira, yana faɗaɗa da'irarsa ta hanyar amfani da ikonsa da matsayinsa."

An fara sanar da dokoki ba tare da tuntuɓar ministocin Taliban na birnin Kabul ba, kuma ba tare da la'akari da alƙawuran da jama'a suka ɗauka kafin su karɓi mulki ba, kan batutuwan da suka shafi bai wa ƴan mata damar samun ilimi. Haramcin samun ilimi da kuma aiki ga mata, ya kasance ɗaya daga cikin "babban tushen tashin hankali" tsakanin ƙungiyoyin biyu, in ji wata wasiƙa da ta fito daga kwamitin sa ido na Majalisar Dinkin Duniya ga kwamitin tsaro a watan Disamba.
A halin da ake ciki kuma, wani mai bincike ya shaida wa BBC cewa Akhundzada, wanda ya fara zama alƙali a kotunan shari'ar Musulunci na Taliban a shekarun 1990, yana ƙara yin tsauri a cikin aƙidarsa.
Akidar Akhundzada ta kasance wanda ta sa ya amince ɗansa na cikinsa ya zama ɗan ƙunar baƙin wake , a cewar wasu jami'an Taliban biyu bayan mutuwarsa a 2017.
Kuma yana da yaƙinin cewa yanke hukuncin da bai dace ba zai iya yin tasiri har bayan rayuwarsa, kamar yadda aka sahida wa BBC.
"Duk shawarar da ya yanke sai ya ce: Ina da alhaki a kai na, a ranar ƙiyama za a tambaye ni dalilin da ya sa ban ɗauki wani mataki ba," in ji wani jami'in gwamnatin Taliban na yanzu.
Wasu mutane biyu da suka taɓa ganawa da Akhundzada sun bayyana wa BBC yadda suka fuskanci wani mutum da ba shi da yawar magana, inda akasari ya ke nuna alama wanda, wasu tsofoffin malamai a ɗakin ke fassarawa.
A cikin bainar jama'a kuma, wasu shaidun gani da ido sun ce yana rufe fuskarsa - yana rufe idanunsa da rawani, kuma galibi yana tsayawa a kusurwa lokacin da yake magana da masu sauraro. An haramta ɗaukar hoto ko naɗar bidiyon Akhundzada. Hotunan sa guda biyu ne kawai aka sani suna yawo a duniya.
Samun ganawa da shi abu ne mai matuƙar. Wani ɗan Taliban ya shaida wa BBC yadda Akhundzada ya saba yin shawarwari akai-akai, amma yanzu "mafi yawan ministocin Taliban suna jira na kwanaki ko makonni". Wata majiya ta shaida wa BBC cewa an sahida wa ministocin da ke birnin Kabul cewa "kada su tafi Kandahar, sai dai idan sun samu gayyata a hukumance".
A lokaci guda kuma, Akhundzada yana ɗauke muhimman ma'aikatun gwamnati zuwa Kandahar - ciki har da rarraba makamai, wanda a baya ya kasance ƙarƙashin ikon tsoffin mataimakansa Haqqani da Yaqoob.
A cikin wasikar da ta fitar a watan Disamba, tawagar sa ido ta Majalisar Dinkin Duniya ta lura da cewa Akhundzada "aikin ƙarfafa ikon mulki da Akhundzada ke yi ya kuma hada da ci gaba da gina rundunar jami'an tsaro a ƙarƙashin ikon Kandahar kai tsaye".
Rahotanni sun nuna cewa Akhundzada ya ba da umarni kai tsaye har zuwa sassan ƴan sanda na cikin gida - inda ya ke tsallake ministocin da ke Kabul.
Wani mai sharhi ya ce sakamakon shi ne "an mayar da ainihin karfin hukuma zuwa Kandahar" - abin da kakakin Taliban Zabihullah Mujahid ya musanta wa BBC.
"Dukkan ministocin suna da ƙarfin ikonsu, suna gudanar da ayyukan yau da kullun da yanke shawara - an ba su cikakken iko kan ma'aikatunsu kuma suna gudanar da ayyukansu," in ji shi.
Sai dai kuma, "a ɓangaren Shari'ar musulunci, shi [Akhunzada] yana da cikakken iko", Mujahid ya ƙara da cewa "domin kaucewa rarrabuwar kawuna da Allah ya haramta, hukuncinsa nita ce ta ƙarshe".
Mutanen da suka 'san abin da duniya ke ciki'
Rashin jin daɗi na ƙaruwa a tsakanin ƴan ɓangaren Kabul, kuma an fara ƙarfafa ƙawance.
"Su [ɓangaren Kabul] mutane ne da suka ga duniya," wani mai sharhi ya shaida wa BBC. Don haka sun yi amanna cewa gwamnatinsu a halin da ta ke ciki yanzu ba za ta ɗore ba.
Ƴan ɓangaren Kabul na son ganin Afghanistan wadda ake tafiyar da ita a kan tafarkin ƙasashen yankin Gulf.
Suna nuna damuwa game da yadda ake samun ƙarfin iko a Kandahar, da yadda a ake aiwatar da dokokin da suka shafi zamatakewa da yadda ya kamata Taliban ta shiga cikin al'ummomin duniya da ilimin mata da kuma samar masu aikin yi.

Sai dai duk da cewa fafutukar samawa matan Afganistan ƙarin ƴanci, ba a yi wa ƴan ɓangaren Kabul kallon masu matsakaicin ra'ayi.
Madadin haka, ƴan ƙungiyar suna ganin su a matsayin "masu la'akari' da yadda al'amuran duniya ke tafiya, wanda Baradar ke jagoranta - shi kuma yana ɗaya daga cikin wadanda suka kafa ƙungiyar kuma har yanzu yana da mabiya da dama da ke yi masa biyayya. Ana kuma tunanin shi ne "Abdul" da Donald Trump ya ambata a matsayin "shugaban Taliban" a yayin muhawarar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar Amurka na 2024. Hasali ma, shi ne babban mai sasantawa na ƙungiyar da Amurka.
Duk da haka dai mutane suna la'akari da yadda ɓangaren na Kabul ke sauya ra'ayi.
"Mun tuna cewa su (shugabannin Taliban da ke birnin Kabul)a baya sun kasance masu lalata akwatunan talabijin, amma yanzu suna fitowa a talabijin da kansu," in ji wani manazarci.
Sun kuma fahimci muhimmancin kafofin watsa labarun.
Yaqoob, wanda shi ne tsohon mataimaki a ƙungiyar- kuma mahaifinsa ya jagoranci Taliban a lokacin mulkinta na farko, lokacin da aka haramta kaɗe-kaɗe da kallon talbijin - ya kasance ya fara farin jini a wurin matasa ƴan Taliban da wasu talakawan Afganistan, lamarin da ya tabbata wajen bayan bidiyoyi na TikTok da kayayyaki da aka kawata da hoton fuskarsa.
Amma babu wanda ya fi yin tasiri wajen sake ɗan sauya yadda jama'a ke kallonsa kamar takwaransa tsohon mataimaki, Sirajuddin Haqqani. Ƙwarewarsa wajen gujewa kamu yayin da rundunarsa ta kitsa wasu munanan hare-hare a yaƙin Afghanistan da sojojin da Amurka ke jagoranta - ciki har da wani harin bam da aka kai a shekarar 2017 a Kabul wanda ya kashe fararen hula sama da 90 a kusa da ofishin jakadancin Jamus - ya ɗaga darajarsa zuwa ga wani abin tarihi a tsakanin magoya bayansa.
A wannan lokacin, hotonsa guda ɗaya ne da aka sani ya wanzu - wanda wani ɗan jaridar BBC Afganistan ya ɗauka.

Asalin hoton, FBI
Sai dai watanni shida bayan janyewar Amurka, Haqqani ya fito gaban kyamarorin duniya a wajen bikin yaye jami'an ƴan sanda a Kabul, inda fuskarsa ta bayyana.
Wannan shi ne mataki na farko sake sabunta kansa: ya cire rigar zama ɗan gwaggwarmaya ya koma ɗan siyasa - wanda jaridar New York Times za ta zauna tare da shi a 2024 ta kuma yi tambayar: shin shi ne mafi kyawun fatan Afganistan na samun canji?
Bayan ƴan watanni kaɗan, FBI za ta yi shiru ta kuma janye ladan dala miliyan 10 da ta ɗora a kansa.
Amma duk da haka manazarta da masu sharhi sun sha shaidwa BBC cewa zai yi wuya a iya fitowa fili a yi adawa da shugaban ƙasar, Akhundzada.
Ana iya cewa adawar da ta fi fitowa fili ga hukunce-hukuncen nasa sun kasance ƙanana - misali rashin aiwatar da ƙa'idoji kamar dokar hana aske gemu a yankunan da jami'an ɓangaren Kabul ke iko da su.
Wani tsohon ɗan Taliban ya jaddada wa BBC cewa ana ɗaukar "biyayya ga [Akhundzada] a matsayin wajibi".
Haqqani da kansa, a cikin hirarsa da New York Times, ya yi watsi da duk wani batu na rarrabuwar kawuna. "Haɗin kai yana da mahimmanci ga Afganistan a halin yanzu don mu sami ƙasa mai zaman lafiya," in ji shi.
A maimakon haka, wani manazarci ya ce, ɓanagren Kabul yana zabar aikewa da "sako zuwa ga ƙasashen duniya da ƴan Afganistan", wanda ke cewa: "Muna sane da koke-koke da damuwarku, amma me za mu iya yi?"
Haka dai lamarin ya kasance kafin umarnin rufe intanet.
Matakin ƙarshe

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Shugaban Taliban mutum ne mai tsananin rashin aminta da intanet; ya yi imanin cewa abin da ke cikinsa ya sabawa koyarwar addinin Musulunci, kuma ya sadaukar da kansa ga akidarsa ta yadda wani mataimaki yakan karanta masa sabbin labarai ko rubuce-rubucen kafafen sada zumunta a kowace safiya maimakon shi ya karanta da kansa, kakakinsa ya taɓa bayyana wa BBC.
Ɓangaren Kabul ya yi imanin cewa kasa ta zamani ba za ta iya rayuwa ba sai da intanet.
An fara bayarda umarnin rufe intanet ne a lardunan da ke hannun abokan Akhundzada, kafin a faɗaɗa shi zuwa yankunan ƙasar baki ɗaya.
Wasu majiyoyi na kusa da ɓangaren na Kabul da kuma cikin gwamnatin Taliban sun bayyana abin da ya biyo baya - wanda kusan ba a taba ganin irinsa ba a tarihin Taliban.
Wata majiya ta ce "Ya ba wa da yawa daga cikin ƴan ƙungiyar mamaki."
A takaice dai ministocin ƙungiyar masu karfin faɗa a ji a birnin Kabul sun taru tare da shawo kan firaminista Mullah Hassan Akhund na birnin Kabul da ya ba da umarnin a sake buɗe intanet ɗin.
Hasali ma, ƙungiyar ta riga ta nuna rashin jin daɗin ta da dokar da aka sani kafin a yanke intanet a duk faɗin ƙasar: shugaban ƙungiyar, Baradar, ya yi tattaki zuwa Kandahar don gargaɗin ɗaya daga cikin gwamnonin Akhundzada mafi aminci da cewa suna buƙatar su "tashe shi" - ya ƙara da cewa dole ne su daina zama ƴan ''amshin shatan'' shugaban ƙolin.
"Ba za ka faɗa masa gaskiya a fili ba, duk abin da ya faɗa sai ka aiwatar da shi," kamar yadda wani ɗan majalisar malamai na Kandahar – ƙungiyar malaman addini na lardin ya ruwaito.
Majiyar ta ce, an yi watsi da kalaman nasa. A ranar Litinin, 29 ga Satumba, umarni ya iso cikin ma'aikatar sadarwa kai tsaye daga shugaban ƙoli na rufe komai. "Ba za a amince da wani uzuri ba, kamar yadda wata majiya a ma'aikatar ta shaida wa BBC.
A safiyar ranar Laraba, gungun ministocin ɓangaren Kabul - waɗanda suka haɗa da Baradar, da Haqqani da Yaqoob - sun hallara a ofishin Firaminista, tare da ministan sadarwa. A nan ne suka buƙaci firaministan da ke da alaƙa da Kandahar da ya ɗauki nauyin gudanar da wannan aiki na sauya odar. A cewar wata majiya, sun shaida masa cewa cikakken alhakin wannan aiki ya rataya ne a wuyarsu.
Haƙarsu ta cimma ruwa, domin kuwa, Intanet ya dawo.
Amma wataƙila mafi mahimmanci, a cikin waɗannan ƴan kwanakin, kamar dai abin da Akhundzada ya yi ishara a cikin wannan jawabin watanni da suka gabata ya faru: ƴan ƙungiyar na yin barazana ga haɗin kai na Taliban.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Amma me yasa aka ƙalubalanci wannan umarnin? Wani masani ya nuna cewa ƴan Taliban a shirye su ke su bi umarnin Akhundzada duk da rashin amincewa da dokoki irin na ilimin ƴaƴa mata.
A halin yanzu, da yawa daga cikin waɗanda suka ƙalubalance shi a baya sun fuskanci fushinsa.
A cikin watan Fabrairun 2025, mataimakin ministan harkokin waje na wancan lokacin ya tsere daga ƙasar bayan gargadi a bainar jama'a cewa shugabannin sun kauce daga "hanyar Allah" wajen "yin zalunci ga mutane miliyan 20" - abin da ke nuni da dokar hana karatun mata.
Masu sa ido na Majalisar Dinkin Duniya sun yi nuni da aƙalla wasu biyu da aka kama bayan da suka yi tambayoyi game da dokar Akhundzada da ta shafi ilimin yara mata, a cikin watannin Yuli da Satumban 2025.
Sai dai kuma akwai alamun Akhundzada da abokansa na yunƙurin kusantar mutanen da ke kusa da Haqqani - duk da sukar da jama'a ke yi na ƙarfafa ikon shugaban ƙasa.
Duk da haka, nuna bijirewa ta hanyar furta kalmomai ya bambanta da watsi da umarni baki ɗaya.
Matsayinsu ya zo da iko da kuma "hanyoyin samun kuɗi", in ji masanin. Amma duka biyun sun dogara ne da intanet, yanzu suna da mahimmanci ga mulki da kuma kasuwanci.
"Kashe intanet ya yi barazana ga gatansu ta hanyar da hana manyan ƴan mata ilimi bai taɓa yi ba," in ji masanin.
"Wataƙila shi ya sa suka nuna jarumta a wancan lokaci."
Bayan da aka sake kunna intanet, an yi ta cece-kuce game da abin da zai biyo baya.
Wata majiya ta kusa da ɓangaren Kabul ta yi nuni da cewa ana iya cire ministocin sannu a hankali ko kuma a rage masu matsayi.
Sai dai wani ɗan Majalisar Malamai na Kandahar ya ce wataƙila shugaban ne ya ja da baya "saboda yana tsoron irin wannan adawa".
Yayin da shekara ta ƙare, ya bayyana a fili cewa babu abin da ya canza.
Wasiƙar zuwa ga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ta yi nuni da cewa wasu ƙasashe mambobin MDD ''sun yi watsi da batun rarrabuwar kawuna tsakanin shugabannin Kandahar da Kabul kamar yadda rikicin iyali ya kasance wanda ba zai canza halin da ake ciki ba; dukkan manyan shugabannin sun zuba jari ne don samun nasarar kasuwancin Taliban.
Zabiullah Mujahid, babban mai magana da yawun gwamnatin Taliban, ya musanta cewa akwai wata ɓaraka.
"Ba za mu taɓa yarda a raba kanmu ba," kamar yadda ya shaida wa BBC a farkon watan Janairun 2026. "Dukkanin jami'ai da shugabanni sun san cewa rarrabuwar kawuna na iya zama illa ga kowa, ga Afghanistan, da addini ya haramta kuma Allah ya haramta."
Duk da haka, ya kuma yarda cewa akwai bambance-bambancen "ra'ayi" tsakanin ƴan Taliban, amma ya kwatanta shi da "bambancin ra'ayi a cikin iyali".
Yayin da watan Disamba ta kai tsakiya, waɗannan "bambance-bambancen" sun sake bayyana.
An ɗauki hoton Haqqani ne a lokacin da yake jawabi a lardin Khost wanda shi ne mahaifansa a lokacin sallar Juma'a, yana mai gargaɗin cewa duk wanda "ya hau kan karagar mulki ta hanyar amincewa da ƙauna da imanin al'ummar ƙasar sannan ya yi watsi da ɓanagren al'umma ɗaya ko ya manta da muradun ƙasar... ba gwamnati ba ne".
A wannan rana, wani mai biyayya ga Akhundzada, Neda Mohammad Nadem - ministar ilimi mai zurfi - ya yi nasa jawabin ga ɗaliban da suka yaye a wata makarantar sakandare da ke lardin makwabtaka da Khost.
"Mutum ɗaya ne ke jagoranta, sauran kuma suna bin umarni, wannan gwamnatin Musulunci ce ta gaskiya," inji shi. "Idan shugabanni suka yi yawa to matsaloli za su kunno kai kuma wannan gwamnatin da muka samu za ta lalace."
Bayan takaddama kan intanet, waɗannan maganganun na baya-bayan nan sun kasance a cikin wani yanayi na daban da Akhundzada ya yi a cikin muryar da aka naɗa aka kuma fitar a farkon 2025.
Amma duk da haka ko 2026 za ta kasance shekarar da ɓangaren Kabul ke yunƙurin kawo sauyi mai ma'ana ga mata da maza na Afganistan har yanzu ana ci gaba da muhawara.
"Kamar yadda aka saba… tambaya ta kasance bayan rashin jituwa da ke tsakanin manyan shugabannin Masarautar - shin kalmomin za su taɓa kai wa matakin da har za a aiwatar da su?" inji wani masani.
"Ba su kai wannan matakin ba tukuna."
Tacewa: Zia Shahreyar, Flora Drury da sashen bincike na BBC Afghan.






