Yadda ƙwaƙwalwar ɗan'adam ke sauya fasali idan ya kai shekara 40

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Alejandro Millán Valencia
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo
- Lokacin karatu: Minti 4
Yayin da ƴan'Adam ke ƙara shekaru a duniya, a hankali a hankali sassan jikinsu na rage ƙarfi.
Musamman tsakanin shekara 40 zuwa 50, gaɓoɓin jikinmu na fara fuskantar wani nau'i na rage ƙarfi da kuzari: misali tsokar jiki na rage ƙarfi, ƙarfin idanu na ƙara raguwa kuma gaɓoɓin jiki na fara gazawa.
Amma wani abu na daban na faruwa da ƙwaƙwalwa.
Maimakon ci gaba da taɓarɓarewa, ƙwaƙwalwa na fuskantar wani abu ne mai yanayi da sauya fasali kamar yadda ake sauya wa na'ura wayoyin da ke cikinta.
Ɗaya daga cikin sakamakon da masu bincike daga jami'ar Monday University ta ƙasar Australia suka gudanar da bincike sama da 150 kan yadda jikinmu ke tsufa, musamman ƙwaƙwalwarmu.
"Kwakwawalwa, ko da yake tana wakiltar kashi 2% na jikinmu ne, amma tana cin kashi 20% na sinadarin ƙara kuzari da ke jikinmu, amma idan ta tsufa takan rasa yadda za ta iya amfani sinadirai masu gina jiki," in ji Sharna Jamadar, wata kwararriya daga jami'ar Monash ta bayyana wa BBC Mundo.
"Kwakwalwa tana wani abu ne da ke yanayi da sabunta tsarinta don yin amfani da sinadarai mafi kyau da za ta iya sarrafawa ta yi amfani da su."

Asalin hoton, Getty Images
A cewar masana kimiyya, tsarin yana haifar da "gagarumin sauyi" kuma yana ɓullo da wasu hanyoyin sadarwa tsakanin gaɓoɓi daban-daban da za su inganta jituwa tsakaninsu a cikin shekaru masu zuwa, yana tasiri kan yadda ƙwaƙwalwa ke sarrafa bayanai inda ɗan'adam zai fahimce su.
Wani abin da ya bai wa masu bincike shi ne yadda wannan sauyin fasali ke iya daƙile tsufar ƙwaƙwalwa a wasu lokutan.
"Yana da muhimmanci a fahimta cewa tsarin da ke faruwa a cikin tunaninmu zai iya taimaka mana mu fahimci yadda muke rage saurin tsufar ƙwaƙwalwa," in ji Jamadar.
Sauyin fasali
Ɗaya daga cikin manyan nasarorin da masana kimiyyar ƙwaƙwalwa suka samu a shekarun baya-bayan nan shi ne sanin wani abu kan yadda ƙwaƙwalwar ke aiki.
A ƙarshe dai an kai ga cewa ƙwaƙwalwarmu ta ƙunshi wata haɗaɗɗiyar cibiyar sadarwa da ke da rukunai daban-daban.
"Bisa la'akari da haka, a lokacin da mu ke girma har mu kai ga zama matasa, cibiyar sadarwa da ke cikin ƙwaƙwalwarmu na da matuƙar kaifi, kuma hakan na da tasiri kan yadda mu ke iya fahimtar waɗansu abubuwa masu muhimmanci," in ji masanin ilimin kimiyyar ƙwaƙwalwar.

Asalin hoton, Getty Images
Shi ya sa a lokacin da muke da waɗannan shekaru muke iya koyon wasanni na musamman ko sabon yare, ko kuma waɗansu sabobbin dabaru da za su taimaka mana a rayuwa.
Duk da haka, a cewar binciken da wata tawaga daga Jam'air Monash ta yi a ƙarƙashin jagorancin Dr. Hamish Deery, daga mun kai shekara 40 wannan lamari yana matuƙar sauyawa.
''Hakan na haifar da rashin sauƙin sauyawar tunani, da rage yiwuwar tace magana kafin furta ta,'' in ji Jamadar
''A kan ga waɗannan sauye-sauyen ne a cikin mutane da ke tsakanin shekara 40 zuwa 50 da haihuwa.''
Hakan na kasancewa ne sakamakon ɓangarorin kwaƙwalwar na karkata ne kan sarrafa bayanai na gama-gari, ba na wani abu na musamman ba, kamar yadda su ke yi a shekarun baya.
Jure wa tsufa
Amma kamar yadda masanan suka bayyana, binciken da suka gudanar ya nuna cewa waɗannan sauye-sauye na taimakawa wurin inganta juriyar ƙwaƙwalwa.
''Abu mai muhimmanci a wannan binciken shi ne ya na ba mu bayanan da mu ke buƙata wurin gano yadda ƙwaƙwalwa ke iya jure wa tsufa wanda zai ƙara mana haske kan yadda ƙwaƙwalwa ke aiki yayin da mutum ke ƙara shekaru,'' in ji mai binciken.

Asalin hoton, Getty
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Hakan na nufin cewa waɗansu ayyukan da muke gudanarwa da ba su buƙatar zurfin tunani ko kuma waɗanda muka daɗe muna yi tsawon rayuwarmu ba za su fuskanci wani cikas ba kuma a wasu lokutan ma su na iya ƙara sauƙin aiwatarwa.
''Abubuwa kamar su yare da sauran abubuwan da mu ka koya da su ke da amfani a rayuwarmu za su iya ci gaba da inganta yayin da shekatruynmu ke ƙaruwa,'' a cewar binciken.
Tunda inganta sinadarai na ɗaya daga cikin dalilan da ke haifar da waɗannan sauye-sauyen a ƙwaƙwalwarmu, babbar shawarar da ake bayarwa ita ce kula da ingancin abincin da mu ke ci da kuma ƙoƙarin motsa jiki yayin da mu ke ƙara tsufa.
"Kwakwalwa tana rage yawan sinadarin glucose da ta ke sarrfawa, don haka abincin da muke ci zai yi tasiri ga lafiyar kwakwalwarmu nan da nan," in ji masanin kimiyya.
Wannan shi ne dalilin da ya sa ya kuma ake bayar da shawarar yin wasannin da ke wasa ƙawƙwalwa wanda zai ci gaba da ƙara kaifin kafafen sadarwan da ke cikinta.







