Me ya sa koci ɗan Ingila bai taɓa lashe Premier League ba - wa zai fara ɗauka?

Zuwan Liam Rosenior Chelsea zai ba shi damar sauya alkiblar tarihin gasar Premier League ga manyan kociyoyi ƴan Ingila.
Tun bayan yi wa Premier League ƙwaskwarima kusan shekara 34 da suka wuce, ɗaya daga cikin manyan abubuwan ban mamaki a gasar shi ne da aka kasa samun kociya ɗan Ingila da ya lashe babban kofin gasar tamaular ƙasar.
Howard Wilkinson, wanda yanzu yake da shekara 82 kuma dattijo a harkar kwallon kafa, shi ne ɗan Ingila na karshe da ya ɗauki kofin tare da Leeds United a kakar 1991–92, amma a lokacin ana kiran gasar da First Division ne.
Tun daga wancan lokaci, koci 12 ne suka jagoranci ƙungiyoyinsu zuwa ɗaukar Premier League, amma babu ko ɗaya ɗan kasar Ingila daga ciki.
Kuma daga nasarorin da aka samu ɗan kasar Scotland, Sir Alex Ferguson ne kan gaba mai Premier League 13 a Manchester United da kuma ɗan kasar Sifaniya, Pep Guardiola mai shida a Manchester City.
Rosenior, mai shekaru 41, shi ne koci na huɗu ɗan Ingila a halin yanzu a gasar Premier League, bayan da ya koma Stamford Bridge daga Strasbourg — sauran sun ha haɗa da Sean Dyche na Nottingham Forest da Eddie Howe na Newcastle United da kuma Scott Parker na Burnley.
Michael Carrick ya karɓi aikin jan ragamar Manchester United bayan korar Ruben Amorim, amma na wucin-gadi ne kawai zuwa karshen kakar wasan bana.
Wannan karancin adadin ƴan Ingila masu horaswa a Premier League ya yi kasa sosai matuka idan aka kwatanta da manyan gasanni biyar na Turai wajen wakilcin ƴan kasa.
A Italiya, koci 16 daga cikin 20 a gasar ƴan Italiya ne, a Sifaniya, 11 daga cikin 20 ƴan Sifaniya ne, a Jamus, 12 daga cikin 18 ƴan Jamus ne; yayin da a Faransa, 10 daga cikin 18 ƴan Faransa ne.
Idan aka hada da kociyoyin rikon ƙwarya da na wucin gadi, an samu 92 wadanda ba ƴan Birtaniya ko Ireland ba a tarihin Premier League.
A halin yanzu, teburin gasar na Premier League, Arsenal kan gaba tare da mai horarwa, Mikel Arteta, sai Manchester City ta biyu karkashin Pep Guardiola, sannan Aston Villa ta uku tare da Unai Emery — dukkaninsu ƴan kasar Sifaniya ne.
To, me ya sa Premier League ta gagari kociyoyin Ingila haka — kuma shin akwai wanda zai iya kawo karshen wannan kasa lashe kofin?
Yadda ake samun ƙarancin masu horarwa a Premier ƴan kasar Ingila a kowacce kaka

Zamanin da Ferguson ya yi da sauran kociyoyin kasashen waje
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tun bayan da aka tsarin gasar Premier League a kakar 1992–93 ta zo daidai da lokacin da Ferguson ya kawo karshen shekaru 26 da Manchester United ta kasa lashe lik, wanda sai da ya ɗauki 13 tun bayan da ya koma Old Trafford - har yanzu ba a samu kociyan da ya yi wannan ƙwazon.
A kuma lokacin Aston Villa, karkashin jagorancin Ron Atkinson, ta kammala kakar a matsayi na biyu. Hakan ya kasance ɗaya daga cikin damar da wani ɗan Ingila ya lashe Premier League.
Wani ɗan Scotland, Sir Kenny Dalglish, ya takawa Ferguson burki, lokacin da ya jagoranci Blackburn Rovers zuwa lashe Premier League a kakar 1994–95, kafin nan Premier League ta zama matattarar manyan kococin Turai.
An tarbi Arsene Wenger da kanun labarai da cewa "Arsene wa?" lokacin da ya koma Arsenal daga ƙungiyar, Nagoya Grampus Eight ta Japan ranar 30 ga Satumba, 1996.
Kafin zuwan Wenger, koci biyu ne kacal daga kasashen waje — Osvaldo Ardiles da Ruud Gullit — da suka taba horarwa a Premier League.
Wenger ya zama mutummin da ya sauya fasalin gasar baki ɗaya, saboda sabbin tsare-tsare da dabara da hangen nesa a lokacin da ya gudanar da aikinsa.
Ya lashe kofin lig uku — ciki har da kakar da aka yiwa lakabi "The Invincibles" a 2003–04 inda Arsenal ba ta yi rashin nasara ba a kakar gabaki ɗayanta — sannan ya dauki kofin FA, bakwai (shi ne kan gaba a wannan tarihi), da kuma Charity/Community Shieldnshida. Haka kuma ya ɗauki lig da FA Cup a kaka ɗaya kuma sau biyu a shekarar 1998 da kuma 2002.
Ƙwazon kociyoyi ƴan Ingila a kowacce gasar Premier League sai yin kasa yake

Daga nan Chelsea ma ta fara farfadowa karkashin jagorancin "The Special One" wanda ake kira Jose Mourinho, wanda ya koma Ingila daga Porto a shekarar 2004 a matsayin wanda ya lashe gasar Champions League, inda nan take ya kawo karshen kasa lashe kofi da ƙungiyar ke fama tun bayan 1955.
Wannan ne ya buɗe kofa ga shigowar masu horarwa da suke lashe manyan kofuna ƴan kasar waje, irin su ƴan Italiya da ya haɗa da Carlo Ancelotti da Antonio Conte da Roberto Mancini da Claudio Ranieri da ɗan Chile, Manuel Pellegrini, sannan ɗan Jamus Jurgen Klopp a Liverpool, wanda daga baya ɗan kasar Holland Arne Slot ya biyo baya.
Dion Dublin, wanda yana cikin ƴan wasan Manchester United a kakar 1992 zuwa 93, ya shaida wa BBC cewar:
"Yawancin koci ƴan kasashen waje da suka zo nan sun yi nasara a sauran gasar Turai kuma sun lashe kofuna, don haka watakila sun san yadda ake cimma hakan. Wata kila wannan ne ya sa babu wani ɗan Ingila da ya taɓa lashe Premier League.
Premier League ta fara ne a 1992, don haka abubuwa sun sauya sosai tun daga wancan lokaci. Na yi imani wani mai horarwa ɗan Ingila zai lashe Premier League nan gaba, babu shakka. Amma yaushe? Ban tabbatar ba."
Tun daga 1992, Ingila ta yi kasa tsakanin manyan lik-lik biyar a Turai, inda aka samu nasara 29 ƴan Italiya a Serie A, 24 ƴan Jamus a Bundesliga, 23 ƴan Faransa a Ligue 1 da kuma 14 ƴan Sifaniya a La Liga.
Shin kociyoyi ƴan kasar Ingila suna da dama kuwa?
Yawan lokutan da ake bai wa kociyan Ingila a manyan ƙungiyoyin Premier League yanzu ya ragu sosai, duk da cewa Newcastle United ce ke amincewa da koci, ƴan Ingila tun bayan Ron Atkinson da ya kare a mataki na biyu, sai lokacin da suka bayar da tazarar maki 12 daga baya Manchester United ta sha gabanta a 1995/96.
Sai kuma yanzu Eddie Howe da yake horar da ƙungiyar St James Park.
Newcastle tana aiki da kociyoyin Ingila cikin kaka tara a Premier League fiye da idan ka ƙwatanta da Tottenham da Aston Villa da sauran su.
Tsohon kocin Tottenham, Harry Redknapp, ya kare a matsayin koci ɗan Ingila mafi matsayi sau biyar a Premier League, ya zarce Howe wanda ya yi hakan sau hudu, sai Sam Allardyce da Sir Bobby Robson, kowannensu sau uku.
Don haka tambayar ita ce: shin rashin kociyoyin Ingila da ke lashe Premier League ya samo asali ne daga karancin damar da ake ba su — ko kuwa kawai ba su kai matakin kwarewar wadanda ake kawowa daga kasashen waje ba, domin rike manyan mukamai a gasar?
Rosenior ya samu damar zuwa Chelsea ta wata sabuwar hanya, inda aka ba shi aikin ta tsarin horar da ƙungiyar Stamford Bridge saboda Chelsea tana daga cikin mallakin kamfanin BlueCo.
Da Rosenior — wanda Hull City ta sallama a watan Mayun 2024 kafin daga bisani ya bar Strasbourg yana matsayi na bakwai a Ligue 1 — ya samu wannan dama a Chelsea ba tare da kasancewa cikin wannan tsarin ba?
Wayne Rooney, wanda Rosenior ya taba zama mataimakinsa lokacin da yake koci a Derby County, ya ce:
"Matasa kociyoyi ƴan Ingila ba sa samun irin wannan dama sosai, amma shi ya tafi ya je ya yi aiki tukuru.
Ga matasa kociyoyin Ingila, wannan babbar dama ce matuka. Ba kasafai muke ganin kociyoyin Ingila a manyan ƙungiyoyin ba, don haka shi ne zai rika jan ragamar hanya a gare mu."
Harry Redknapp ne ya fi karewa a matsayi mai kyau a Premier League.
Tony Pulis, wanda ya taba fafatawa da manyan kociyoyin Turai a lokacin da yake Stoke City, ya yi imanin cewa akwai babban dalili guda ɗaya da ya sa jerin manajojin da suka lashe Premier League bai kunshi sunan wani dan Ingila ba.
Ya shaida wa BBC Sport cewa:
"Zan yi tambaya ne kawai, kociyan Ingila nawa ne suka taɓa jagorantar manyan ƙungiyar a cikin shekaru 25 da suka gabata? Wannan ne dalilin da ya sa babu wani koci ɗan Ingila da ya taɓa lashe Premier League.
"Idan ka duba ƙungiyoyin da suka lashe kofuna da dama a wannan lokaci, kungiyoyin suna nan, ƴan wasan suna nan masu iya lashe kofuna, amma galibi kociyoyi ƴan kasashen waje ne ke zabar ƴan wasan. Idan ba ka da ƙungiya mafi kyau da kuma ƴan wasa mafi nagarta, ba za ka iya lashe Premier League ba."
Sai dai Gary O'Neil, wanda ya gaji Rosenior a Strasbourg bayan da ya taɓa horar da AFC Bournemouth da Wolverhampton Wanderers, yana da ra'ayi daban. Ya ce:
"Abu ne mai sauki a ce kociyoyin Ingila ba sa samun dama, amma ban ga wannan a matsayin cikakkiyar gaskiya ba.
"Ina ganin Premier League ita ce gasar ƙwallon kafa mafi ƙyau a duniya, wadda ke da kuɗi mafi yawa. A matsayinka na koci ɗan Ingila, dole ne ka cancanci wannan dama. Ba wanda ake bai wa manyan mukamai a matsayin kyauta ba. Dole ne sai ka cancanta, kuma wasu daga cikin masu horarwa da suka zo nan suka yi nasara suna da kwarewa mai matukar girma."
Wane koci ne ɗan Ingila zai fara lashe kofin Premier League?
Rosenior ya fi dacewa saboda damar da yake da ita a hannunsa, hazaka da kuma yadda Chelsea ke shirye-shiryen zuba jari — amma wasu suna da fata ga Eddie Howe da kuma Frank Lampard.
Howe ya lashe kofin cikin gida a karon farko cikin shekaru 70 na farko cikin shekaru 56, lokacin da suka doke Liverpool a wasan karshe a Carabao Cup a kakar da ta gabata. Haka kuma ya kai su gasar Champions League karo na biyu.
Aikin kociya da Frank Lampard ke yi na farfadowa cikin nasara a Coventry City, waɗanda suke na ɗaya a gasar Championship, bayan da ya horar da Chelsea sau biyu, haka kuma a Derby County da Everton.
Tsohon mai tsaron bayan Manchester United da tawagar Ingila, Phil Jones, ya shaida wa BBC Sport cewa:
"Na yi tsammanin wanda ya fi dacewa shi ne Eddie Howe.
"Abin da ya yi a Bournemouth abin al'ajabi ne, abin da yake yi yanzu a Newcastle — kuma ina ganin idan aka ba shi lokaci, idan aka ba shi tawagar ƴan wasa, da izinin gudanar da aikin yadda ya kamata da damar yin nasara, ina ganin zai iya zama wanda zai kai ga nasara.''











