Ko za a iya sake samun Sardauna a Arewa?

Alhaji Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto

Asalin hoton, Arewa

Lokacin karatu: Minti 3

Ƙungiyoyin kare muradun arewacin Najeriya sun sha alwashin ƙirƙirar wata gamayya da za saita halin da yankin ke ciki.

Sun ce suna son mayar da yankin kan turba kwatankwacin lokacin firimiyan yankin na farko, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto da ya fara ginawa kafin rasuwarsa.

Ƙungiyoyin sun hada da ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa (ACF) da Gidauniyar tunawa da marigayi Sardauna da Kuma ƙungiyar dattawan Arewa. Sun haɗu ne kan wannan manufa yayin da ake cika shekara 60 da mutuwar Sardauna.

Tarihin yankin arewacin Najeriya ba ya cika ba tare da ambaton Sardauna ba. Zagin Sardauna kamar zagi ne ga mutanen Arewa.

Wasu al'ummar yankin na ganin ba za a sake yin wani Sardauna ba wanda ake yi wa kirarin Gamji Dan Ƙwarai.

Dr Hakeem Baba Ahmed, na daga cikin dattawan Arewa da ke fatan cimma tabbatar da farfaɗo da yankin arewa ya shaida wa BBC cewa da wahala a iya samun wani Sardauna.

"Sardauna fa jiha ɗaya ya yi mulki wadda yanzu ita ce jihohi 19, ba yadda za ka yi ka sake irin Sardauna sai dai a diba abubuwan da ya yi wanda akwai irin dattawa da za su iya tunawa," in ji shi.

Ya ƙara da cewa kisan da aka yi wa su Sardauna ne dalilin da ya kawo wa Najeriya koma bayan da har yanzu ba a gama warwarewa ba.

"Ya kamata al'ummar arewacin Najeriya su sani cewa koma bayan da aka samu a cikin shekaru 60 da kisan da aka yi wa su Sardauna, ya fi fitowa a yanzu musamman idan aka yi la'akari da irin shugabancin da muke da shi a yanzu."

Dr Hakeem Baba Ahmed, ya ce,"Irin tsarin shugabancin da su Sarduna suka yi, da tsarewa jama'a hakkinsu da sadaukar da kai da suka yi da kuma rike kowa da amana, shi ne muke so a dawo da shi a yanzu."

A cewarsa nan da wasu shekaru masu zuwa za su duba yadda za su kawo wa yankin ci gaba da yadda zamu gyara alakarmu da sauran al'ummar sauran shiyoyin Najeriya da ma yadda za su dawo da kimar kasar da yankin arewa a ido duniya."

"Shekara 60 bayan juyin mulkin soji na farko a Najeriya, har yanzu tabon da ya bari bai goge ba, kuma abin da ya faru na ci gaba da tasiri a tsarin zamantakewar al'ummar kasar," In shi Dr Hakeem

Wane ne Sardauna?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An haifi Alhaji Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto a ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1910 a garin Rabbar na jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya.

Kakansa shi ne sarkin Musulmi Muhammad Bello, wanda na ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa daular Sokoto, kuma ɗa ne ga marigayi Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodiyo.

Ahmadu Bello ya fara makaranta a garin Sokoto, sannan ya wuce zuwa makarantar horas da malamai ta Katsina.

Kafin daga bisani Sultan ya naɗa shi malami a makarantar Middle School ta Sokoto.

A shekarar 1938 aka naɗa shi Sardaunan Sokoto, sannan ya halarci ƙasar Ingila domin yin karantu kan harkokin mulki a shekarar 1948.

Ya kuma fara shiga harkokin siyasa gadan-gadan bayan dawowarsa daga karatu, inda har aka zaɓe shi mamba a majalisar dokoki ta Arewacin Najeriya. Ya kuma zama ministan ayyuka da raya ƙasa.

Ya kasance Firimiyan farko na yankin Arewa daga shekarar 1954 zuwa 1966.

Sannan ya jagoranci jam'iyyar NPC ta lashe kujeru da dama a zaɓen da aka gudanar bayan samun ƴancin kai.

Bayan kammala zaɓe, ya zaɓi ya ci gaba da kasancewa Firimiya na arewa, inda ya zaɓi Abubakar Tafawa Ɓalewa ya zamo Firaministan Najeriya.

An kashe Ahmadu Bello a ranar 15 ga watan Janairun shekara ta 1966, bayan wani juyin mulki da wasu sojoji ƴan ƙabilar Ibo suka jagoranta.