Ƙungiyoyin Italiya na rubibin Maguire, Valencia na son Onyeka

Asalin hoton, Getty Images
Aston Villa na son kammala yarjejeniyar sayen ɗanwasan gaba na Ingila Tammy Abraham, wanda ke taka leda a Besiktas a matsayin aro daga Roma. Ɗanwasan mai shekara 28 ya taba taka leda a kakar 2018-19 a Villa inda ya taimaka wa ƙungiyar haurowa zuwa gasar Premier. (Times - subscription required)
Ƙwarin guiwar Manchester United na ƙaruwa kan ɗanwasan tsakiya na Kamaru Carlos Baleba, mai shekara 22 daga Brighton. (Sun)
Juventus ta tuntuɓi Crystal Palace kan ɗanwasan gaba na Faransa Jean-Philippe Mateta, mai shekara 28, yayin da take neman maye gurbin Dusan Vlahovic, mai shekara 25. (Sky Sports)
Inter Milan da Napoli da Fiorentina na ribibin ɗanwasan baya na Manchester United da Ingila Harry Maguire, mai shekara 32, a Janairu. (Tuttomercato - in Italian),
Ɗanwasan baya na Nottingham Forest da Brazil Murillo, mai shekara 23, na cikin waɗanda Manchester United ke nema domin maye gurbin Maguire. (Mail)
Chelsea na son ɗauko ɗanwasan baya na Bournemouth da Argentina Marcos Senesi, mai shekara 28. (Talksport)
Kocin riƙon ƙwarya na Manchester United Michael Carrick na don ɗauko ɗanwasan tsakiya na Middlesbrough da Ingila Hayden Hackney, mai shekara 23, wanda kuma Tottenham ke nema. (Teamtalk)
Valencia ta tuntuɓi Brentford kan ɗanwasan tsakiya na Najeriya Frank Onyeka. (Sky Sports)
Nottingham Forest na matsin lamba kan ɗanwasan Italiya da Inter Milan Davide Frattesi, mai shekara 26. (Tuttomercato - in Italian)
Aston Villa na nazarin ɗauko ɗanwasan tsakiya na Real Madrid da Spain Dani Ceballos, mai shekara 29, bayan gaza ɗauko Conor Gallagher. (Talksport)
Tottenham na diba yiyuwar sayar da ɗanwasan gaba na Argentina Alejo Veliz, mai shekara 22, wanda ta ba Rosario Central a matsayin aro. (Athletic - subscription required),
Galatasaray da Napoli da Juventus da wasu ƙungiyoyin Saudiyya na sa ido kan ɗanwasan tsakiya na Portugal midfielder Bernardo Silva, mai shekara 32, wanda ke shekararsa ta ƙarshe a Manchester City kuma har yanzu bai sabunta kwangilar shi ba. (Caught Offside)











