Museveni ya lashe zaɓen Uganda karo na bakwai

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Hukumar Zaɓen Uganda ta ayyana Shugaba Yoweri Museveni a matsayin wanda ya lashe zaɓen ƙasar na ranar Alhamis.
Da wannan sakamako Mista Museveni zai tsaiwata wa'adin mulkinsa na shekara 40 da ƙarin shekara biyar nan gaba.
Museveni ya samu kashi 72 na ƙuri'un da aka kaɗa, yayin da jagoran adawar ƙasar Bobi Wine ya samu kashi 25 a cewar hukumar zaɓen.
Bobi Wine ya yi watsi da sakamakon inda ya bayyana shi da ''ƙarya'', tare da kiran ƴan ƙasar su yi zanga-zangar lumana don nuna adawa da sakamakon.
Museveni, mai shekara 81, ya fara zama shugaban ƙasar a matsayin jagoran ƴantawaye a 1986, kuma daga nan ya riƙa lashe duka zaɓukan ƙasar da aka yi.
An samu tashe-tashen hankula a zaɓen, inda Bobi Wine ya ce mutum 21 aka kashe a rikicin.
Sai dai kawo yanzu mutum bakwai hukumomi suka tabbatar da mutuwarsu.
Tun a ranar Talata aka katse intanet a ƙasar, wani abu da ya haifar da wahalar tantance sahihancin bayanai.
Hukumomi dai sun kare matakin hana yaɗuwar labaran ƙarya, da aikata zamba da rura rikici, matakin da Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da shi.












