Wane matsayi ake ciki game da yunƙurin tsige gwamna Fubara?

Asalin hoton, Siminalayi Fubara /Facebook
Majalisar jihar Rivers ta ce babu gudu babu ja da baya wajen yunƙurin tsige gwamnan jihar Rivers Siminialayi Fubara da mataimakiyarsa Farfesa Ngozo Nma Odu.
Sun bayyana haka ne bayan majalisar ta koma zama bayan ɗan hutun da ya yi daga inda suke zama na wucin-gadi a Fatakwal.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Major Jack mai wakiltar Akuku Toru I, ya ce za su ci gaba da shirinsu na tsige gwamnan ne saboda yadda a cewarsa gwamnan da mataimakiyarsa suka ci gaba da yi wa doka karan-tsaye.
Ya ce tunda suka aika musu takardar yunƙurin tsigewar, ba su mayar musu da martani ba, wanda a cewarsa shi ya sa ya buƙaci shugaban majalisar da a ci gaba da yunƙurin.
Sun umarci babban alƙalin jihar da ya kafa kwamitin da zai binciki gwamnan da mataimakiyarsa bisa zargin da suke musu na aikata manyan laifuka da suka ce sun saɓa doka.
Su kansu ƴanmajalisa guda huɗu da suka buƙaci majalisar ta dakatar da yunƙurin, sun lashe amansu, inda suka janye goyon bayan da suke ba gwamnan.
Shugaban marasa rinjaye na majalisar, Sylvanus Nwankwo, mai wakiltar Omuma ya ce duk da yunƙurin da suka yi na shiga tsakani da goyon bayan gwamnan, ya yi zargin cewa gwamnan ya cigaba da tunzura ƴan jihar a kan majalisar.
'Abin da ya janyo matsalar'
Da yake magana kan musabbabin matsalar, mai ba gwamnan jihar shawara kan harkokin siyasa, Darlington Oji ya ce rashin gabatar da ƙarin kasafin kuɗin 2025 a gaban majalisar ne ya jawo matsalar.
Oji ya bayyana haka ne a zantawarsa da tashar Arise News, inda ya ce bayan ƙarewar wa'adin mulkin dokar ta-ɓaci a jihar, gwamnan ya gana da shugaban majalisar da shugaban masu rinjaye domin sanin yadda za a yi.
Ya ce gwamnan ya buƙaci su mayar da ƴanmajalisar jihar guda uku da suke goya masa baya, amma suka ƙi.
Ya ce amma sai suka nace dole sai ya gabatar da ƙarin kasafin kuɗin, amma gwamnan bai yi ba.
Wannan kuma ya faru ne saboda gwamnan ya ce ba ya buƙatar ƙarin kasafin kuɗi, saboda ya gaji naira biliyan 6000 a asusun jihar bayan komawa mulki, wanda a cewarsa ya ishe shi.
Sai ya ƙara da cewa duk wani abu da yake buƙata zai saka a kasafin kuɗin jihar na 2026, amma suka ƙi amincewa.
Yadda aka kusa samun tangarɗa

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Da farko an kusa samun tangarɗa bayan mataimakiyar shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Ribas ɗin ta kuma ce tana fatan Gwamnan Fubara da mataimakiyarsa za su gyara kura-kuransu tare da girmama yarjejeniyar da aka cimma da Shugaba Tinubu.
A farkon wannan makon ne shugaban marasa rinjaye na majalisar, Sylvanus Nwankwo da wani ɗan majalisar, Peter Abbey suka yi kira da takwarorinsu sun janye daga matakin tsige gwamnan, domin warware matsalar ta hanyar lalama.
Barista Karibi George wani lauya kuma mai sharhi ya ce abin da hakan ke nufi (janyewar ƴanmajalisa huɗu) shi ne matakin zai samu tangarɗa saboda yunƙurin ba zai samu kashi biyu cikin uku na yanmajalisar dokokin jihar ba, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Barista George ya kara da cewa zai fi kyau idan ƴanmajalisar suka sake duba wata hanya ta warware rikicin cikin lalama.
Ya ce ya yi mamakin yadda ƴan majalisar suka sanar wa da gwamnan matakin tsige shi, saboda a cewarsa abin da kundin tsarin mulki ya tadana shi ne ya kamata majalisar ta aike wa gwamnan sanarwar maimakon wallafa a jaridu.
Lauyan ya kuma ce idan ƴanmajalisar suka gaza yin hakan, to akwai wata matsalar, domin gwamnan zai iya cewa bai san da matakin ba a hukumance, wanda shi ma hakan ya saɓa wa kundin tsaroin mulki.
"Ni a ra'ayina zan ce a bi hanyar da ta dace don warware wannan matsala. tuni wasu masu ruwa da tsaki na ƙoƙarin shiga tsakani, kamar ƙungiyar waɗanda tuni suka kafa kwamitocin sasanci domin warware matsalar. ina ganin a ba su dama domin warware wanna matsala'', in ji shi.






