KAI TSAYE, Afcon 2025/29: An je hutu Masar 0-0 Najeriya

Wasan neman mataki na uku tsakanin Masar da Najeriya a gasar cin kofin nahiyar Afirka da Morocco ke karɓar bakunci 2025/26

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. An je hutu Masar 0-0 Najeriya

  2. , Masar 0-0 Najeriya

    Afcon

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan Masar, Emam Ashour yana taka leda duk inda ka duba shi zaka gani yana ta kai komo a wasan san.

  3. , Masar 0-0 Najeriya

    Mohamed Salah na Masar ya samu bugun tazara

  4. Gooool Najeriya ta ci ƙwallo, Paul Onuachu

    Akor

    Asalin hoton, Getty Images

    An soke ƙwallon da Onuachu ya ci bayan da aka duba VAR, kuma Akor ne ya buga shi ne ta bugi keyar Onuachu

  5. , Masar 0-0 Najeriya

    Masar ta kara kai kora daga ɓangaren dama an kuma bugo ƙwallon sama, amma ta yi yawa ta fita wajen filin. bugun falan ɗaya ga Nageriya.

  6. , Masar 0-0 Najeriya

    Har yanzu dai Masar ta fi riƙe ƙwallo fiye da Najeriya a wasan neman mataki na uku da na huɗu a Afcon, saura minti 15 a je hutu, banda karin lokaci.

  7. , Masar 0-0 Najeriya

    Masar ta bugo ƙwallo daga ɓangaren dama a lokacin da mai tsaron ragar Najeriya, Nwabble sai Mohamed Salah ya taɓa ƙwallo amma dai daga baya ba ta zama haɗari ba.

  8. , Masar 0-0 Najeriya

    Masar sun fi riƙe ƙwallon da rabawa a wasan nan na neman mataki na uku da na huɗu a Afcon

    Senegal ce ta fitar da Masar da cin 1-0 a daf da karshe.

    Mai masaukin baki Morocco ce ta yi waje da Najeriya a bugun fenriti 4-2, bayan da suka tashi 0-0.

  9. , Masar 0-0 Najeriya

    An yi minti 20 da take leda kuma Zizo na Masar ya ja ƙwallo daidai da fita waje daga Najeriya ya taɓa ta zama ƙwana, bai ji daɗin abinda ya faru ba, so ya yi ƙwalon ta faɗa ragar Super Eagles.

  10. , Masar 0-0 Najeriya

    Masar ta kai kora da ƙwallo a sama zuwa wajen Mostafa Mohamed, wanda ya yi kokarin tarewa da kirji amma sai ƙwallo ya taɓa hannusa, an kuma hura.

  11. , Masar 0-0 Najeriya

    Masar ta fara wasa tun daga mai tsaron gidanta zuwa yan baya ta kai ga Salah shi kuma ya buga zuwa cikin da'ira ta 18 ta Nageria, amma Nwaballi ya ankara ya yib sauri ya sa kafa ya buge ƙwallon.

  12. , Masar 0-0 Najeriya

    Akor Adams ya yi kokarin buga ƙwallo daga ɓangaren hagun fili, amma ba ta yi zafi ba an tare ta cikin ruwan sanyi.

  13. , Masar 0-0 Najeriya

    Har yanzu dai wasan bai ɗauki zafi ba, kuma ba a fara kai hare-hare masu zafi ba, an fi yin ƙwallon daga tsakiyar fili, tsakanin ƴan wasan Masar da na Najeriya.

  14. , Masar 0-0 Najeriya

    Ana gyaran tuta ta kusurwar fili, bayan Emam Ashour na Masar, wanda ya yi kokarin fitar da ƙwallo kada ta je kwana sai ya tuge tutar, amma yanzu an gyara za a ci gaba da wasan neman mataki na uku da na hudu a gasar cin kofin Afirka a Morocco.

  15. , Masar 0-0 Najeriya

    An buga kawana an kuma fitar da ƙwallon daga gidan Masar, amma yanzu dai Najeriya za ta yi fifa gidan Masar - har yanzu wasan bai ɗauki zafi ba.

  16. , Masar 0-0 Najeriya

    Chukwueze na Najeriya ya kai kora gidan Masar amma ƙwallo ta je kwana.

  17. , Masar 0-0 Najeriya

    Trezequet ya bugo kwallo amma mai tsaron raga ya kama daga gefen hagu ba wani haɗari.

  18. An fara wasa Masar da Najeriya, Masar 0-0 Najeriya

    An fara wasan neman mataki na uku da na huɗu a gasar cin kofin nahiyar Afirka tsakanin Masar da Najeriya da ake yi a Morocco.

  19. , Masar 0-0 Najeriya

    Ƴan wasa na daf da take leda suna cikin fili ana taken kasashen biyu daga nan kowa ya kama guri ya zauna a fara wasan neman mataki na uku a gasar cin kofin Afirka da ake yi a Morocco.

  20. Karo na biyu tsakaninsu a gasar da Morocco ta shirya, Afcon Morocco 2025/26

    Wannan ce haduwarsu ta biyu a gasar da Morocco ta dauki nauyin shiryawa, bayan ta farko a shekarar 1988.

    Daga cikin haduwarsu tara a gasar AFCON, takwas sun kasance ne a matakin rukuni.

    A shekarar 1976 sun hadu a zagaye na biyu na rukuni, yayin da sau bakwai suka kara a tsarin rukuni.

    A shekarar 1963, Masar ta tsallaka zagaye, yayin da a shekarar 1988 da 1990 Najeriya ta samu nasarar wucewa zagayen gaba a kan Masar.

    Gaba ɗaya, kasashen biyu sun hadu sau 20, inda Najeriya ta yi nasara takwas, Masar ta ci shida, yayin da shida suka kare da canjaras