Ko Osimhen ne ginshiƙin tawagar Najeriya?

Victor Osimhen with his thumbs up

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Victor Osimhen na cikin waɗanda suka fi zura ƙwallo yanzu haka a gasar Afcon 2025
    • Marubuci, Charlotte Coates
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport journalist
  • Lokacin karatu: Minti 4

A duk lokacin da Osimhen ke wasa, ƴan Najeriya na sa ran tawagarsu za ta taɓuka abin kirki.

Ɗan wasan na gaba mai shekara 27 zai fuskanci Moroko a gasar kusa da ƙarshe na Gasar cin Kofin Afirka a ranar Laraba, bayan tawagar Najeriya ta lashe wasanninta biyar a baya.

Osimhen na cikin sahun ƴan wasan da suka zura ƙwallo huɗu a gasar, tare da ƴan wasa kamar Mohammed Salah na Liverpool, waɗanda ke bin bayan Brahim Diaz na Moroko.

Sai dai wasu abubuwa da suka faru a gasar sun kusa dakushe ƙoƙarin da ɗan'wasan na ƙungiyar Galatasary ya yi, musamman musayar yawu da saɓani da ya riƙa samu da abokan wasansa.

Daga ciki akwai musayar yawunsa da Ademola Lookman a ranar da Najeriya ta lallasa Mozambique da ci huɗu da nema, inda har aka yaɗa jita-jitar cewa ɗan'wasan ya yi yunƙurin ficewa daga tawagar Najeriya da ke buga wasan.

Osimhen ya ƙalubalanci Lookman ne kan ƙin jefa masa ƙwallo a daidai lokacin da yake tunanin ya fi kusa da jefa ta a raga, sannan ya buƙaci kocinsu Eric Chelle ya canja shi, wanda shi kuma ya yi. Da aka cire shi, sai shi kuma ya wuce kai-tsaye zuwa ɗaki, maimakon ya zauna tare da sauran ƴan benci har a tashi.

Tuni dai ƙurar ta lafa, inda kocin da Osimhen ɗin suka nuna cewa duk wata ɓaraka da aka samu, ta cikin gida ce, kuma a cikin gida za a magance ta.

A yanzu da yake buƙatar zura ƙwallo biyu domin kamo Rashidi Yekini a matsayin wanda ya fi zura ƙwallo a cikin ƴan'wasan Najeriya da ƙwallo 37, Osimhen na gab da kafa tarihi a harkar tamaular Najeriya.

Ya ce, "Ba kamo Rashidi Yekini ko wuce shi ba ne babban burina, ina tunanin Mr Rashidi ne gwarzon ɗan'wasan gaba da Super Eagles ta taɓa samu a tarihi."

"Ni dai ina iyakacin ƙoƙarina, tabbas akwai daɗi mutum ya samu kansa a cikin waɗanda suka kafa tarihi da tawagar Super Eagles. Burina in samu lashe kofi domin ƙasata tare da taimakon abokan wasana. Kuma mun kama hanya."

'Yadda ya taso a Legas'

An haife shi ne a Legas, inda za a iya cewa ya sha gwagwarmaya lokacin da yake ƙarami.

Rasuwar iyayensa tun yana ƙarami ya sa dole ya fara sayar da ruwa a bakin titunan Legas domin kula da kansa da ƴan'uwansa.

Tsohon kyaftin ɗin tawagar Super Eagles William Troost-Ekong ya ce yanayin yadda Osimhen ya taso cikin gwagwarmaya ya taimaka masa wajen ƙara himma.

"Ya sha wahalar rayuwa a lokacin da yake tasowa," in ji a zantawarsa da BBC.

"Shi yake kula da kansa da ƴan'uwansa. Ya rasa iyayensa tun yana ƙarami, don haka sai ya taso da ƙoƙarin nema da himma.

"Kullum yana da burin zura ƙwallo, kuma kullum burinsa ya zama na farko a komai, hatta wajen cin abinci.

"Ana buƙatar irin su a tawaga. Himmarsa ta sa ya zama abin koyi ga ƴanƙwallo na yanzu da masu tasowa.

'Ana masa kallon abin koyi'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Yekini ya ci wa Najeriya ƙwallo 37 a wasa 58 da ya buga, shi kuma Osimhen zuwa yanzu ya zura ƙwallo 35 a wasa 50.

Idan Osimhen ya karya tarihin Yekini a wannan gasar ta Afcon, Najeriya ma za ta iya samun nasarar lashe gasar nahiyar ta Afirka karo na huɗu domin rage zafin rashin samun gurbin zuwa gasar cin kofin duniya.

Amma Troost-Ekong ya ce babban burin Osimhen a yanzu shi ne lashe gasar cin kofin AFCON.

"Yekini babba ne, zan so Osimhen ya karya tarihinsa na zura ƙwallo, amma dai ina jin daɗin yadda yake girmama Yekini."

"Don haka ina da yaƙinin zai zura wasu ƙwallayen da dama a nan gaba, kuma ina tunanin nan gaba shi ne za a riƙa hanƙoron karya wa tarihin zura ƙwallaye."

A nasa jawabin, mai bibiyar harkokin wasannin Najeriya Oluwashina Okeleji, ya bayyana Osimhen a matsayin, "sarkin ƙwallon Najeriya."

Okeleji ya ce, "tun lokacin da ya fara buga ƙwallo a tawagar ƴan ƙasa da shekara 17 ne ya fara nuna ya kama hanyar zama gwarzo kuma gawurtaccen ɗan'ƙwallo.

"A cikin ƴan'wasan tawagar, ana masa kallon babban tauraro, kuma mutane suna masa kallon abin koyi. Shi ya sa idan ba ya nan, ake ganin alama.

"Duk da cewa ba kyaftin ba ne, amma ana masa kallon jagora a cikin tawagar," in ji shi.

Victor Osimhen in a Napoli shirt

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Osimhen ne ya zura ƙwallon da ta taimakawa Napoli lashe gasar Serie A bayan shekara 33

Tashe a ƙungiyoyin da ya buga

Duk inda matashin ɗan'wasan ya je, yana samun nasarar zura ƙwallaye da dama ba tare da ƙaƙƙautawa ba.

Ya fara nuna kansa ne a turai a kakar 2019-20, lokacin da ya zura ƙwallo 18 a wasannin da ya buga wa ƙungiyar Lille a gasar Ligue 1, kafin ya koma ƙungiyar Napoli na Italiya.

A Italiya ne Osimhen ya fara jan hankali a duniyar tamaula, inda ya fara zama ɗan'wasan gaba da ake tsoro matuƙa.

Ya kafa tarihi a ƙungiyar Napoli bayan zura ƙwallo 26 a kakar 2022-23, inda suka lashe gasar Scudetto bayan shekara 33 tana nema. A kakar ce Osimhen ya zarce George Weah a matsayin ɗan Afirka da ya fi zura ƙwallo a gasar Serie A, inda ya zura ƙwallo 47.

Ɗan'wasan ya bar Napoli a kakar 2023, inda da farko aka fara batun wasu ƙungiyoyi a gasar Premier League na zawarcinsa, amma a ƙarshe sai ya koma Galatasary ta Turkiyya.

Da farko ya je ƙungiyar ne a matsayin ɗan'wasan aro, inda ya zura ƙwallo 26 a wasa 30, inda ya lashe ɗan'wasan da ya fi zura ƙwallo a ƙungiyar, sannan suka lashe kofuna biyu.

Yanzu dai ya zama ɗan'wasa na dindindin a Galatasary, inda zuwa yanzu ya zura ƙwallo shida a wasa 12.