RB Leipzig ta sayi Sani, Jurgen Klopp da Maresca za su iya maye gurbin Alonso

Suleiman Sani

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto, Suleiman Sani
Lokacin karatu: Minti 3

Manchester City na shirin gabatar da tayin siyan dan wasan bayan Crystal Palace da Ingila Marc Guehi, mai shekara 25, kafin karshen kasuwar sayar da 'yan wasa ta Janairu, amma da wuya ta iya bada fam miliyan 35 da Palace ta bukaci a biya ta.(Talksport), external

Sai dai darektan wasanni na Bayern Munich Max Eberl ya rika kira ta waya a baya baya nan domin shawo kan Guehi ya koma kungiyar da taka leda a bazara. (Sky Germany), external

Duk da tafiyar kocinta Ruben Amorim, Manchester United ba ta da anniyar dawo da dan wasan gaban Ingila Marcus Rashford, mai shekara 28, lokacin da kwantaragin aronsa ya kare a Barcelona.(Talksport), external

Dan wasa mai kai hari na Manchester United da Ingila a tawagar masu shekaru kasa da 20, Ethan Wheatley, mai shekara 19, zai tafi Bradford City a matsayin aro a karshen kakar wasa. (Manchester Evening News), external

Nottingham Forest na zawarcin dan wasan Bournemouth da Ingila Marcus Tavernier, mai shekara 26, amma Cherries ba za ta siyar da shi ba .(Daily Mail), external

Tottenham Hotspur ta toshe duk wata hanyar samun bayyannai kan dan wasan gaban Faransa Mathys Tel, mai shekara 20, duk da cewa Paris FC na son a ba ta shi aro. (Florian Plettenberg), external

Bournemouth na ci gaba da tattaunawa da Ferencvaros kan kula yarjejeniya da dan wasan tsakiyar Hungary Alex Toth, mai shekara 20, bayan da aka yi watsi da tayinsu na farko na fam miliyan 8.6. (Sky Sports), external

Newcastle na neman dan wasan baya a watan Janairu bayan da dan wasan Ingila Tino Livramento, mai shekara 23, ya ji rauni a kafarsa wanda zai sa ya yi jinyar makwanni takwas. (Sky Sports), external

Manchester City da Brentford da kuma Tottenham na gab da rasa dan wasan Nigeria mai kai hari a tawagar masu shekaru kasa da 20 Suleiman Sani,mai shekara 19, bayan da RB Leipzig ta kamala cinikin siyansa kan fam miliyan 4.5 daga kungiyar Trencin na kasar Slovakia. (Daily Mail), external

Liverpool ba za ta sallami dan wasan bayan Ingila Joe Gomez, mai shekara 28, a wannan watan ba, bayan da dan wasan baya na Arewacin Ireland Conor Bradley, mai shekara 22, ya samu rauni a gwiwarsa .(Football Insider), external

Tsohon kocin Liverpool Jurgen Klopp na cikin wadanda za su maye gurbin Xabi Alonso a matsayin kocin Real Madrid.Haka kuma Antonio Conte da Enzo Maresca suma suna ciki.(Fichajes - in Spanish), external

Arsenal ba za ta sayar da dan wasan bayan Ingila Ben White, mai shekara 28, duk da cewa baya tamaula yadda ya kamata amma yana jan hankalin kungiyoyi irinsu Everton da Manchester City. (Teamtalk)