Bayern Munich na son Guehi, Guler zai ci gaba da taka leda a Real Madrid

Marc Guehi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Marc Guehi
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester City na zawarcin dan wasan Ingila da Nottingham Forest Elliot Anderson mai shekara 23. (Teamtalk)

Bayern Munich ta kara kaimi wajen siyan dan wasan bayan Crystal Palace da Ingila Marc Guehi, mai shekara 25, wanda Manchester City da Liverpool ke zawarcinsa. (Sky)

Roma ta amince da yarjejeniyar aro tare da zabin siyan dan wasan gaban Aston Villa da Netherlands Donyell Malen, mai shekara 26, kan Yuro miliyan 28.5. (Sky Sports Italia)

Atletico Madrid na nazari kan tayin yuro miliyan 35 da Manchester United ta yi mata kan Marcos Llorente, mai shekara 30. (Fichajes )

Ana alakanta dan wasan Manchester City da Portugal Bernardo Silva, mai shekara 31 da Como kuma ana ganin zai koma kungiyar ne a bazara. (Sky Calcio Club via Four Four Two)

Manchester United da Tottenham da kuma Newcastle United na bibiyar dan wasan Sassuolo Tarik Muharemovic mai shekara 22. (CaughtOffside)

Dan wasa mai kai hari na Ingila da Roma Tammy Abraham, mai shekara 28, wanda a halin yanzu yana aro a Besiktas, ya kosa ya koma Ingila inda ake ganin zai koma tamaula a Aston Villa. (Talksport)

Bournemouth da Lazio na zawarcin dan wasan Ferencvaros da Hungary Alex Toth, mai shekara 20. (Teamtalk)

Dan wasan tsakiyar Real Madrid Arda Guler, mai shekara 20, ba shi da niyyar barin kungiyarsa suk da cewa Arsenal na son daukarsa. (Teamtalk)

Monaco na zawarcin dan wasan Leicester Wout Faes. Dan wasan kasar Belguim mai shekara 27 ya koma kungiyar ne ta the Foxes a shekarar 2022. (FootMercato)