Ko Najeriya za ta iya fitar da Moroko ta kai wasan ƙarshe a Afcon?

Afcon

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 6

Nigeriya za ta fafata da Moroko mai masaukin baki a zagayen daf da ƙarshe na gasar Cin Kofin Afirka da za su kara ranar Laraba a filin Prince Moulay Abdellah a birnin Rabat.

Super Eagles na fatan lashe Afcon karo na huɗu jimilla, wadda rabonta da shi tun 2013, ita kuwa Moroko tana da kofin nahiyar Afirka da ta ɗauka a 1976.

Dukkan tawagar biyu ba su yi rashin nasara ba a gasar bana, inda Najeriya ta lashe dukkan wasa biyar da ta buga kawo yanzu, ita kuwa Morocco ta yi nasara huɗu da canjaras ɗaya.

Sun fafata a Afcon karo biyar, kuma kowanne daga ciki ana samun wadda kan doke wata a tsakaninsu.

Wannan shi ne karo na biyu da za su fuskanci juna a shekara 22, kuma karo na biyu da za su kece raini a zagayen daf da ƙarshe a babbar gasar tamaula ta Afirka.

Wasa huɗu baya sun kara a cikin rukuni a 1976 sau biyu da a 2000 da kuma 2004.

Karon farko da suka fara tata ɓurza a Afcon shi ne a 1976 a cikin rukuni, inda Moroko ta yi nasarar lashe wasan da 3-1 da kuma 2-1, wadda daga baya ta ɗauki kofin kuma a karon farko a tarihi.

Wannan shi ne karo na biyu da za su fafata a daf da karshe a Afcon, inda Najeriya ta yi nasarar cin 1-0 a 1980, kuma Felix Owolabi ya ci ƙwallon da ta kai ta ɗauki kofin a karon farko a tarihi a gasar da ta shirya a Legas.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sun kuma kara a 2000, inda Najeriya ta yi waje da Moroko a wasan ƙarshe na rukuni na huɗu da cin 2-0, inda Finidi George da kuma Julius Aghahowa suka ci wa Super Eagles ƙwallayen.

Wasan ƙarshe da suka fuskanci juna a Afcon shi ne a zagayen cikin rukuni a 2004, inda Moroko ta yi nasara 1-0 a wasan farko a rukuni na huɗu, kuma Youssef Hadji ne ya ci ƙwallon.

Super Eagles ta fuskanci mai masaukin baƙi karo 10 a Afcon da cin wasa uku da canjaras uku da rashin nasara huɗu.

Wannan shi ne karo na biyu da za ta fuskanci mai masaukin baƙi a jere, bayan wasa da Ivory Coast a cikin rukuni a 2023 da cin 1-0, sannan Najeriya ta yi rashin nasara 2-1 a karawar ƙarshe na gasar ta gabata.

Haka kuma Najeriya ta yi nasara a kan mai masaukin baƙi a 2002 da ƙarewa a mataki na uku da doke Mali da yin nasara a kan Senegal da cin 2-1 a cikin rukuni a 1992

Sai dai Najeriya ta yi rashin nasara a wasa huɗu da ta kara da mai masaukin baƙi, sau biyu a hannun Aljeriya a wasan cikin rukuni da kuma fafatawar karshe da wanda Ghana ta yi nasara a 2008 a kwata fainals da wanda Ivory Coast ta lashe kofin a da 2023.

Haka kuma Najeriya ta yi canjaras uku da mai masaukin baƙi a Afcon a 1978 a karawa da Ghana a 2002 a wasa da Mali a cikin rukuni da 2004 a wasa da Tunisia a daf da ƙarshe daga baya ta yi rashin nasara a fafatawar ƙarshe

Wannan shi ne karo na 12 da za a kara tsakanin tawagogin biyu, Moroko ta yi nasara shida da canjaras biyu, Najeriya ta ci wasa uku.

Sau nawa aka kara tsakanin Najeriya da Morocco?

Najeriya da Morocco sun fuskanci juna sau 11 a dukkan fafatawa, inda Najeriya ta yi nasara uku da canjaras biyu aka doke ta shida daga ciki ta ci ƙwallo takwas aka zura mata 14 a raga.

A wasan Afcon kuwa sun fafata sau biyar, Najeriya ta yi nasara biyu da rashin nasara uku aka zura mata ƙwallo shida a raga ita kuma ta ci shida.

Sakamakon wasannin da suka buga a Afcon:

1976, Wasan cikin rukunin farko – ranar 6 ga watan Maris

  • Morocco 3 - 1 Nigeria

1976, Wasan ƙarshe ranar 11 ga watan Maris

  • Morocco 2 -1 Nigeria

1980, Daf da ƙarshe, ranar 19 ga watan Maris

  • Nigeria 1 - 0 Morocco

2000, Wasan rukuni na huɗu, ranar 3 ga watan Fabrairu

  • Nigeria 2 - 0 Morocco

2004, Wasan rukuni na huɗu, ranar 27 ga watan Janairu

  • Nigeria 0 - 1 Morocco

Bajintar da Najeriya ke yi a gasar kofin Afirka

Super Eagles

Asalin hoton, Getty Images

  • Ta doke Aljeriya ne a zagayen kwata fainal ta kawo gurbin ƴan huɗu.
  • Ta shi ƙwallo 14 a gasar nan, ita ce kan gaba a yawan zura su a raga a Morocco.
  • Rabon da ta zura 14 a raga a Afcon tun gasar da Kamaru ta shirya a 2021.
  • Ta ci ƙwallo a dukkan wasa biyar da ta yi a Morocco, rabon da ta ci ƙwallo a wasa shida a jere a tun 2013.
  • Ta yi nasarar cin wasa biyar a Afcon a karon farko, kamar yadda ta yi a 2019.
  • Ba ta taɓa lashe shida ba a jere a gasar cin kofin nahiyar Afirka.
  • Kuma karo na 16 da za ta fafata a zagayen daf da ƙarshe a tarihin Afcon.
  • Cikin wasa 15 da ta yi a daf da ƙarshe ta yi nasara takwas aka doke ta bakwai daga ciki, inda aka yi wasa biyu a 1976.
  • Cikin wasa takwas da ta yi nasara a daf da ƙarshe, huɗu daga ciki ba ta kai ga bugun fenariti ba, sannan huɗu a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
  • Idan Najeriya ta yi nasara za ta kai zagayen wasan ƙarshe karo na tara, kuma na biyu a jere a Afcon bayan doke ta da Ivory Coast ta yi a 2023 a wasan karshe.
  • Za ta yi kan-kan-kan da Ghana a yawan zuwa zagayen ƙarshe a Afcon.
  • Tun daga 2013, Masar da Senegal da Ivory Coast ne suka kai wasan ƙarshe karo biyu a jere kamar Najeriya.
  • Wasan ƙarshe takwas da ta kai ta lashe kofin a 1980 da 1994 da kuma 2013, yayin da ta yi rashin nasar a 1984 da1988 da 1990 da 2000 da kuma 2023.
  • Rashin nasarar da ta yi a daf da ƙarshe shi ne a 2010 da kuma2019, sai ta yi nasara 2013 da kuma 2023.
  • Sau uku ne ba ta kaiwa zagayen daf da karshe a gasar Afcon 20, shi ne a 1982 da 2008 da kuma 2021.
  • Wasan da ta yi nasara ba ta kai ga bugun fenariti ba 1980 da 1990 da 2000 da 2013.
  • Zagayen daf da karshe da aka doke ta ba ta kai ga fenariti ba a 1978 da 1992 da 2002 da kuma 2019.
  • Victor Osimhen ya ci ƙwallo huɗu a Morocco shi ne kan gaba a yawan zura ƙwallo a raga tsakanin ƴan Najeriya tun bayan Odion Ighalo a 2019.
  • Najeriya ba ta taɓa yin rashin nasara ba a Afcon idan har Osimhen ya ci ƙwallo ko ya bayar aka zura a raga daga ciki ta yi nasara biyar da canjaras biyu,

Ƙoƙarin da Morocco ke yi a wasannin Afcon

Afcon

Asalin hoton, Getty Images

  • Ta doke Kamaru a kwata fainal da ta kai daf da ƙarshe a karon farko tun 2004.
  • Wannan shi ne karo na biyar da take kai wa daf da ƙarshe a Afcon bayan 1980 da 1986 da 1988 da 2004 da kuma 2025.
  • Wannan shi ne karo na biyu a matakinta mai masaukin baƙi a daf da ƙarshe bayan 2004.
  • Ta lashe wasa ɗaya daga uku a zagayen daf da ƙarshe 2004
  • An doke ta a gasa biyu a jere a Afcon a daf da ƙarshe a 1986 da kuma 1988.
  • Ta yi rashin nasara a wasan farko da ta kai daf da ƙarshe a 1980 a gasar da Najeriya ta gudanar.
  • Idan har ta yi nasara za ta kai zagayen ƙarshe karo na biyu a sama da shekara 21.
  • Dukkan wasan da take yi a daf da ƙarshe baya kai wa bugun fenariti
  • Dukkan wasan da aka doke ta a irin wannan zagayen da cin 1-0 ne.
  • Idan har ta yi nasara za ta zama karo na biyu a jere da mai masaukin baƙi za ta kai wasan ƙarshe, bayan Ivory Coast a 2023.
  • Za kuma ta zama mai masaukin baƙi 15 da za ta kai zagayen ƙarshe a Afcon a tarihi.
  • Mai tsaron raga, Yassine Bounou ya zama na farko daga Morocco da ya yi wasa huɗu ba tare da ƙwallo ya shiga ragarsa ba.
  • Brahim Díaz ya ci ƙwallo biyar, ɗan wasa na farko da ya yi wannan bajintar ta cin ƙwallo a kowanne wasa tun bayan 2021
  • Morocco ce kan gaba a cin ƙwallo ko dai daga bugun tazara ko na kusurwa a gasar bana