Afcon: Sakamakon wasan Morocco da Tanzaniya da Afirka ta Kudu da Kamaru

ƴanwasan Morocco na murna

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 5

A ranar Lahadi ne Morocco da Kamaru suka samu gurbi a wasan zagayen kwata fayinal na gasar cin Kofin Afirka da ake fafatawa a ƙasar Morocco.

Morocco ta samu nasara a kan Tanzaniya da ci 1-0, yayin da ita ma Kamaru ta lallasa Afirka ta Kudu da ci 2-1 tare da samun gurbi a zagayen ƴan takwas na gasar.

Senegal ce ta farko da ta kai zagayen kwata fainal a Afcon, bayan da ta doke Sudan 3-1 ranar Asabar, karo na tara da ta kai wannan matakin a tarihi.

Ta kuma yi karawa 15 a jere ba tare da rashin nasara ba a Afcon da cin wasa 10 da canjaras biyar daga ciki.

Itama Mali ta kai zagayen ƴan takwas, amma da kyar da gumin goshi, wadda ta doke Tunisiya 3-2 a bugun fenariti bayan sun tashi 1-1 har da karin lokaci.

Kuma Mali ta kare wasan da yan ƙwallo 10 a ciki fili tun daga minti na 26 da take leda, bayan da aka bai wa Woyo Coulibally jan kati.

Golan Mali, Diarra shi ne fitatcen dan wasa a karawar, wanda ya buge fenariti biyu.

Da wannan sakamakon ranar Juma'a 9 ga watan Janairu Mali da Senegal za su kara a zagayen kwata fainal.

Wasan farko Morocco da Tanzaniya

Afcon

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mai masaukin baƙi, Morocco ta kara da Tanzaniya a wasa na uku a zagaye na biyu a gasar cin kofin nahiyar Afirka da take gudanarwa.

Wannan shi ne karo na biyu da suka fafata a Afcon, bayan da suka haɗu a wasannin cikin rukuni a 2023 da aka yi a Ivory Coast.

Wannan shi ne karo na biyu da Tanzaniya ta fuskanci mai masaukin baƙi a Afcon, bayan da ta yi rashin nasara 3-1 a hannun Najeriya a Legas a 1980.

Morocco da Tanzaniya sun fuskanci juna a wasa takwas a dukkan karawa, mai masaukin baƙi ta yi nasara bakwai har da biyar baya, yayin da Tanzani ta ci ɗaya daga ciki.

Wasan da Tanzaniya ta yi nasara a kan Morocco shi ne a 2014 a neman shiga gasar kofin duniya, wadda ta ci 3-1 a gida ranar 24 ga watan Maris a Dar es Salaam.

A karawa ta biyu kuwa Morocco ta yi nasara cin 2-1 a cikin watan Yunin 2013, sai dai dukkansu ba wadda ta samu zuwa gasar da aka yi a Brazil.

Sun fafata sau takwas a tsakaninsu, inda Morocco ta yi nasara bakwai da cin ƙwallo 15 aka zura mata biyar a raga da rashin nasara ɗaya.

Daga ciki wannan shi ne wasa na biyu a Afcon da za su buga, bayan da Morocco ta yi nasara 3-0 a rukuni na shida ranar 17 ga watan Janairun 2024 a wasannin da aka yi a Ivory Coast a 2023.

Ƙwazon Morocco a gasar cin kofin Afirka

Afcon

Asalin hoton, Getty Images

  • Wannan shi ne karo na huɗu da ta kai zagayen ƴan 16 a Afcon.
  • Ta haura matakin gaba a 2021.
  • An kuma fitar da ita a zagayen ƴan 16 a 2019 da kuma 2023.
  • Ita ce ake fara zura wa ƙwallo a raga a gasa uku a zagayen ƴan 16.
  • Idan har ta yi nasara za ta kai kwata fainal karo na biyar, wadda ta fara zuwa a 1998 da 2004 da 2017 da kuma 2021.
  • Ta yi rashin nasara a irin wannan matakin a hannun Masar a 2021 a kwata fainals da kuma a wajen Afirka ta Kudu a 2023 a zagayen ƴan 16.
  • Karawar da ta doke Malawi a 2021, ita ce ta farko daga wasa biyar a zagayen ziri ɗaya ƙwale.
  • Brahim Diaz ya ci ƙwallo a dukkan wasa uku a bana, shi ne na biyu a wannan bajintar daga Morocco a Afcon, bayan Ahmed Faras a gasar 1972 da kuma a 1976.
  • Watakila Diaz ya zama na farko da zai zura ƙwallo a raga a wasa huɗu a jere a Morocco a tarihi.
  • Morocco ta kai hari zuwa raga kai tsaye sau 20 a bana da cin ƙwallo shida.
  • Babu wadda ta kai Morocco raba ƙwallo a Afcon a bana mai 1,581.

Kokarin da Tanzania ke yi a wasannin Afcon

Afcon

Asalin hoton, Getty Images

  • Wannan shi ne karon farko da Tanzaniya ta kai zagaye na biyu a Afcon.
  • Ta kuma kawo wannan matakin da maki biyu mafi karanci da tawaga ta kai zagayen gaba, kuma ɗaya dagq huɗun da aka yi wa alfarma tun lokacin da aka fito da tsarin a 2019.
  • Har yanzu ba ta ci wasa ba daga 12 da ta yi a Afcon, wadda ta yi kan-kan-kan da Guinea-Bissau na kasa cin karawa a tarihin gasar cin kofin Afirka.
  • Feisal Salum, ya zama na farko daga Tanzaniya da ya ci ƙwallo a Afcon mai taka leda a babbar gasar kasar tun bayan ƙwazon da Thuwein Waziri ya yi a 1980.
  • Tanzaniya ta kai hari 15 a wasa ukun da ta yi a cikin rukuni da cin ƙwallo uku.

Wasa na biyu tsakanin Afirka ta Kudu da Kamaru

Afcon

Asalin hoton, Getty Images

Afirka ta Kudu da Kamaru sun fuskanci juna ranar Lahadi a wasa na huɗu a zagaye na biyu a Afcon da ake yi a Morocco

Sun fara wasa a 1996, inda Afirka ta Kudu ta yi nasara a wasannin da ta shirya sannan ta lashe kofin a karon farko a tarihi.

Sai dai sau tara suka kece raini a tsakaninsu jimilla, inda Afirka ta Kudu ta yi nasara uku da canjaras biyar, yayin da Kamaru ta ci wasa ɗaya.

Wasa tilo da Kamaru ta doke Afirka ta Kudu shi ne a sada zumunta ranar 9 ga watan Yulin 1992 da ta ci 2-1.

Tun daga lokacin ne Kamaru ta kasa yin nasara a kan Afirka ta Kudu daga ciki suka yi canjaras biyar aka ci Kamaru wasa biyu daga ciki.

Hugo Bross, mai horar da Afirka ta Kudu a yanzu haka, ya ja ragamar Kamaru ta lashe Afcon kuma a karo na biyar a 2017.

Ya yi kociyan kasar tsakanin Maris ɗin 2016 zuwa Nuwambar 2017.

Ya kuma yi wasa 25 da cin tara da canjaras 10 da rashin nasara shida.

Jimilla an kara tsakanin Afirka ta Kudu da Kamaru sau tara, inda Afirka ta Kudu ta yi nasara uku da cin ƙwallo 14 aka zura mata tara a raga da rashin nasara ɗaya.

Daga ciki ne suka fuskanci juna a Afcon da Afirka ta Kudu ta shirya a 1996, inda Kamaru ta yi rashin nasara 3-0 a rukunin farko ranar 13 ga watan Janairun 1996.

Gwagwarmayar Afirka ta Kudu a Afcon

Afcon

Asalin hoton, Getty Images

  • Wannan shi ne karo na uku da ta yi wasa a zagayen ƴan 16, ta kuma yi nasara a biyu a kan Masar a 2019 da kuma Morocco a 2023.
  • Ta yi amfani da yan wasa 17.
  • Ƴan wasanta shida duk sun buga mata karawa uku daga cikin rukuni.

Ƙwazon da Kamaru ke yi a gasar kofin Afirka

Afcon

Asalin hoton, Getty Images

  • Wannan shi ne karo na 17 da Kamaru ta kawo wannan matakin.
  • Karo na biyar a jere da ta buga zagaye na biyu a Afcon.
  • A yanzu za ta buga wasa na 11 a zagayen kwata fainal kenan.
  • Bryan Mbeumo ya samar da damar cin ƙwallo har sau takwas a bana.
  • Kamaru ta yi amfani da ƴan yawa 22 a Afcon a bana, kuma Devis Epassy ya yi minti 270 a wasannin da ake yi a Morocco.