Barca na son mallakar Rashford, Chelsea za ta ɗauko Vinicius

Ɗanwasan gaba na Ingila forward Marcus Rashford,

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Barcelona na son mallakar ɗanwasan gaba na Ingila forward Marcus Rashford, mai shekara 28, wanda ta karɓo aro daga Manchester United. (Athletic - subscription required)

Aston Villa na son ta ɗauko ɗanwasan gaba na Ingila Tammy Abraham, wanda ke taka leda a Besiktas a matsayin aro daga Roma. (Telegraph - subscription required)

Manchester United na fatan doke Arsenal kan ɗanwasan Blackburn Rovers da Ingila Igor Tyjon, mai shekara 17. (Sun)

Newcastle United na nazari kan ɗanwasan baya na Atalanta Giorgio Scalvini, mai shekara 22, bayan raunin da ɗanwasan Switzerland Fabian Schar, 34 ya ji. (Teamtalk)

Chelsea na son shan gaban abokan hamayya da ke ribibin ɗanwasan Brazil da Real Madrid Vinicius Jr. (Fichajes - in Spanish)

Kocin Crystal Palace Oliver Glasner na kan gaba wajen waɗanda ake tunanin Manchester United za ta ɗauko a matsayin koci. (Caughtoffside)