Everton na son raba Arsenal da White, Dortmund na sa ido a kan Bobb

Asalin hoton, Getty Images
Everton na harin sayen dan bayan Arsenal Ben White, na Ingila mai shekara 28, domin shawo kan matsalar da suke fuskanta a bagaren dama na baya. (Football Insider)
Borussia Dortmund na sa ido ta ga yadda za ta kaya a kan dan wasan tsakiya na Manchester City Oscar Bobb, dan Norway mai shekara 22, bayan zuwa Antoine Semenyo na Ghana mai shekara 26. (Florian Plettenberg)
Har yanzu Tottenham na sha'awar sayen dan wasan tsakiya na Atletico Madrid da Ingila, Conor Gallagher, duk da cewa Aston Villa ake ganin ita ta fi damar samun dan wasan mai shekara 25. (Teamtalk)
Haka kuma Aston Villa na nuna sha'awarta a kan dan gaban Newcastle United, William Osula na Denmark mai shekara 22, bayan da kungiyar ta kasa samun matashin dan gaban Real Madrid Gonzalo Garcia, mai shekara 2, wanda ke tawagar Sifaniya ta 'yan kasa da shekara 21. (Talksport)
Matashin dan bayan Como Jacobo Ramon ya burge Liverpool da Chelsea, kuma kungiyoyin Firmiya da dama na tura masu yi musu farautar 'yan wasa domin su je su ga yadda dan wasan mai shekara 21 ke taka leda. (CaughtOffside)
Paris FC na daga cikin kungiyoyin da ke son aron dan gaba Faransa na gefe Mathys Tel a watan nan, amma kuma Tottenham na son dan wasan mai shekara 20 ya tsaya kar ya tafi. (Fabrizio Romano)
Darektan wasanni na Tottenham Fabio Paratici na dab da barin kungiyar domin tafiya kungiyar Serie A, Fiorentina bayan kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta Janairu. (Athletic)
Dan bayan Farans, Dayot Upamecano, mai shekara 27, zai ci gaba da zama a Bayern Munich har zuwa 2031 bayan da ya kawar da yuwuwar damar tafiya Real Madrid a matsayin kyauta - dan wasan da ba shi da wani kwantiragi a kansa a bazarar nan. (Fichajes)













