Arsenal na sa ido kan Livramento, Juve na son Bernardo Silva

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal na isa ido kan ɗanwasan baya na Newcastle United da Ingila Tino Livramento, mai shekara 23, wanda take son ɗaukowa a bazara. (Sun)
Aston Villa na diba hanyoyin cimma yarjejeniya kan ɗanwasan tsakiya na Atletico Madrid da Ingila Conor Gallagher. (Talksport)
Rahotanni sun ce Atletico na son fam miliyan 35 kan Gallagher, amma Villa na diba yiyuwar dokar kashe kuɗi. (Mail)
Ɗanwasan tsakiya na Hungary Dominik Szoboszlai, mai shekara 25, ya cimma yarjejeniya kan tsawaita kwantaraginsa da Liverpool, inda ya yi watsi da tayin Real Madrid da Bayern Munich. (CaughtOffside)
Manchester City ta amince ta ɗauko matashin ɗanwasan tsakiya na Scotland Keir McMeekin, mai shekara 15, daga Hearts. (Fabrizio Romano)
Rangers ta tuntuɓi Sunderland kan ɗanwasan tsakiya na Ingila Dan Neil, mai shekara 24, da kuma Romaine Mundle, mai shekara 22. (Sky Sports)
Kocin tawagar Ingila Thomas Tuchel da na Brazil Carlo Ancelotti da na Amurka Mauricio Pochettino na cikin jerin waɗanda Manchester United ke nazarin ɗaukowa a matsayin sabon koci. (Mirror)
Hull City na tattaunawa da Manchester United kan ɗanwasan tsakiya na Ingila mai shekara 22 Toby Collyer a mnatsayin aro. (Sky Sports)
Kocin Real Madrid Xabi Alonso na danganta shi a matsayin wanda ya fi dacewa ya maye gurbin kocin Manchester City Pep Guardiola. (Football Transfers)
Juventus na kan gaba wajen buƙatar ɗanwasan tsakiya na Manchester City da Portugal Bernardo Silva, mai shekara 31, idan kwangilar shi ta kawo ƙarshe a ƙarshen kaka. (Fichajes - in Spanish)
Ɗanwasan Aston Villa da Jamaica Leon Bailey, mai shekara 28, zai iya komawa Girona a matsayin aro har zuwa ƙarshen kaka idan har wa'adinsa ya kawo ƙarshe a Roma da ya yake taka leda a mastayin aro. (Fichajes - in Spanish)











