KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 18/01/2026

Wannan shafi ne da ke kawo mu ku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed da Abdullahi Bello Diginza

  1. Gobara ta kashe aƙalla mutum 5 a Pakistan

    Wuta gobara da ta tashi a wasu rukunin shaguna a birnin Karachi na Pakistan ta yi sanadin rasa rayukan aƙalla mutum biyar.

    Gobarar ta tashi ne a rukunin shaguna na Gul Plaza a yammacin jiya Asabar da kuma har kawo yanzu ba a kammala kashe ta ba.

    Jami'an kashe gobara sun ce tsananin zafin da kuma yadda wutar ke ci sosai suna na kawo cikas ga aikin ceton da ake kuma ana fargabar adadin waɗanda mutu zai iya ƙaruwa saboda akwai waɗanda suka maƙale a cikin shaguna.

    Gobarar ta ginin na Gul Plaza mai ɗauke da shaguna sama da dubu ɗaya ta tashi ne da yammacin Asabar.

    Wani mai magana da yawun hukumar bayar da agajin gaggawa ya shaidawa BBC cewa za a iya ɗaukar kwanaki kafin a iya kashe wutar.

  2. Tarayyar Turai za ta yi taron gaggawa kan barazanar harajin Trump

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na sanya sabon haraji kan wasu ƙasashe takwas da ke adawa da shirinsa na karɓe iko da yankin Greenland ya janyo suka daga shugabannin ƙasashen Turai.

    Firaministan Burtaniya Keir Starmer ya ce matakin ba daidai ba ne, yayin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana lamarin a matsayin "abin da ba za a amince da shi ba".

    Kalaman na zuwa ne bayan da Trump ya sanar da ƙarin harajin kashi 10 cikin 100 kan kayayyakin da ake shigar da su Amurka daga Denmark da Norway da Sweden da Faransa da Jamus da Burtaniya da Netherlands da kuma Finland, wanda zai fara aiki a ranar 1 ga Fabrairu.

    Mr Trump ya ce zai iya ƙara harajin zuwa kashi 25 - kuma zai ci gaba har sai an cimma yarjejeniya.

    Bayan barazanar Trump, Tarayyar Turai ta kira taron gaggawa da karfe a Brussels ranar Lahadi.

    Taron dai zai samu halarcin jakadu daga ƙasashe 27 na ƙungiyar ta EU, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.

    A halin da ake ciki kuma, dubban mutane sun fito kan tituna a yankin Greenland da Denmark a ranar Asabar din da ta gabata don nuna adawa da shirin Amurka na mamaye yankin.

  3. Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afrika ta yi martani kan ƙorafin tawagar Senegal

    ...

    Asalin hoton, CAF

    Hukumar kwallon ƙafa ta Afrika (CAF) CAF ta yi watsi da iƙirarin da hukumar kwallon kafa ta Senegal (FSF) ta yi game da rashin adalci a tsare-tsaren da ake yi gabannin wasan ƙarshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) da ke gudana a Moroccoi.

    A wata sanarwa da ta fitar hukumar ta jaddada cewa ta yi ƙoƙarin tabbatar da daidaito tsakanin dukkan tawagogin da suka halarci gasar ta bana.

    "Hukumar CAF ta himmatu kan tabbatar da adalci da gaskiya da kuma bin ƙa'idojinta ," in ji sanarwar.

    Ta kuma ƙara da cewa CAF ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da kwamitin tsare-tsaren gasar na cikin gida (LOC) don tabbatar da yanayi iri ɗaya ga dukkan tawagogin da ke halartar gasar.

    Martanin na CAF dai na zuwa ne bayan Senegal ta fitar da wata sanarwa inda ta yi zargin rashin adalci a tsare-tsaren da suka shafi walwala da tsaron ƴanwasa gabannin wasan da za ta fafata da Morocco mai masaukin baƙi.

  4. An sake buɗe intanet a Uganda bayan kammala zaɓen Shugaban ƙasa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    An dawo amfani da shafukan intanet a Uganda bayan rufewar da aka yi a lokacin zaɓen shugaban ƙasa da aka kammala a ƙarshen makon jiya.

    Hukumar da ke kula da harkokin sadarwa ta ce, an daƙile intanet ɗin ne domin kiyaye zaman lafiyar jama’a da kuma hana yin amfani da kafafen sadarwa na zamani, da sauran manhajoji wurin yaɗa labaran da ka iya haddasa ɓarkewar rikici.

    Amma ofishin kare haƙƙin ɗan'adam na Majalisar Dinkin Duniya ya soki matakin, wanda ya bayyana a matsayin abin da ya haifar da "matuƙar damuwa."

    Cire dakatarwar na iya nuni da ƙwarin gwiwa da hukumomin tsaro ke da shi cewa ƙasar ta kaucewa barazanar tarzoma.

    Tun da farko dai hukumar zaɓen ƙasar ta bayyana shugaba Museveni a matsayin wanda ya lashe zaɓen da kashi 72 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa.

    Babban abokin hamayyarsa, Bobi Wine, wanda ya samu kashi 25 cikin 100, ya yi watsi da sakamakon tare da yin kira da a gudanar da zanga-zangar lumana don ƙalubalantar sakamakon.

  5. Amurka ta yi iƙirarin kashe wanda ake zargi da hannu a kisan sojojinta a Syria

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'an gwamnatin Amurka sun ce dakarun asar sun kai wani hari da ya hallaka wani shugaban ƙungiyar Al-Qaeda "wanda ke da alaƙa kai tsaye" da ƙungiyar 'yan ta'adda ta IS da ke da alhakin kai harin kwanton ɓauna da ya kashe Amurkawa uku a ƙasar Siriya.

    A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Amurka ta Centcom ta fitar ta ce an kashe Bilal Hasan al-Jasim a harin da aka kai a ranar Juma'a, wanda aka kai a arewa maso yammacin Siriya.

    Sanarwar ta ce yana da alaƙa da ɗan bindigar ƙungiyar IS wanda ya kashe tare da jikkata jami'an Amurka da na Syria.

    BBC ba ta tabbatar da iƙirarin na Amurka Amurka ba.

    Tun bayan mutuwar Amurkawa uku a ranar 13 ga watan Disamban 2025 a yankin Palmyra da ke tsakiyar ƙasar Syria, Amurka ta kai hare-hare da dama kan mayaƙan IS a Syria, a ƙarƙashin wani shiri da ta yi wa laƙabi da 'Operation Hawkeye Strike'.

    A farkon wannan watan, Centcom ta ce ta kashe ko kuma ta kama ƴan ƙungiyar IS kusan 25 a cikin ayyuka 11 da ta gudanar tsakanin ranakun 20 zuwa 29 ga watan Disamba.

  6. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Lahadi.

    Ibrahim Yusuf Mohammed da Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo a shafukanmu na sada zumunta, domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.