Me ya sa zanga-zangar Iran ta zama ta daban a wannan karon?

Asalin hoton, MAHSA / Middle East Images / AFP via Getty Images
Zanga-zangar adawa da gwamnati da ake yi a Iran ta kai matakin da ba a taɓa gani ba a tarihin Jamhuriyar Musuluncin ƙasar mai shekara 47, a cewar masana da shaidu da dama.
Yayin da wasu yanƙasar suka fantsama kan titunan ƙasar, shugaban Amurka Donald Trump ya yi gargaɗin ''kai hari mai muni'' ƙasar, idan mahukunta suka kashe masu zanga-zangar, kuma ya ce a shirye Amurka take ''don taimaka wa''
Hukumonin Iran sun alƙawarta mayar da martani, idan har Amuka ta kai musu hari, inda suka cve za ua kai hari kan sansanonin sojin Am urka da kawayenta da ke yankin Gabas ta Tsakiya.
Ko me ya bambanta wannan zanga-zangar da waɗanda suka faru a ƙasar a baya?
Mamaye wurare masu yawa

Masana sun ce wannan zanga-zangar ba a taɓa ganin irinta ba a baya a Iran.
Eli Khorsandfar, mai bincike kan ilimin zamantakewa ya ce yayin da ake gudanar da zanga-zangar a manyan biranen ƙasar, sun kuma bazu zuwa ƙananan garuruwan ƙasar ''waɗanda mutane da dama ba su taɓa jin sunayensu ba''.
A baya Iran ta fuskanci zanga-zanga.
A 2009 an samu zanga-zangar da aka yi wa laƙabi da 'Green Movement', wanda mutane masu matsakacin ƙarfi suka gudanar saboda zargin maguɗin zaɓe.
Duk da cewa zanga-zangar ta yi ƙarfi, an yi ta ne kawai a manyan biranen ƙasar.
Sannan kuma zanga-zanga da aka yi a 2017 da 2019 an yi su ne a wuraren da talakawa suka fi yawa.
Zanga-zanga ta baya-bayan nan da za a iya kwatantata da wannan ita ce wadda aka yi a 2022, wadda ta auku bayan mutuwar wata matashiya Mahsa Amini, a hannun ƴansanda.
Zanga-zangar ta bazu bayan mutuwarta, inda ta yi ƙamari bayan kwana shida, akmar yadda rahotonni suka bayyana a lokacin.
To amma wannan zanga-zanga ta yanzu da alama ta zarta ta Mahsi Amini girma, kuma kullum karuwa take tun bayan fara ranar 28 ga wata Disamba.

Asalin hoton, Ameer Alhalbi/Getty Images
''Mai kama-karya ya mutu''
Kamar dai zanga-zangar 2022, ita ma wannan ta haifar da sabbin kiraye-kirayen samar da canjin gwamnati.
"Zanga-zangar 2022 ta samo asali ne daga matun mata. Amma daga baya abubuwa da dama sun shiga, haka ita ma wannan ta faro ne daga matsin tattalin arziki, amma cikin ƙanƙanin lokaci ta ƙunshi abubuwa masu yawa,'' a cewar Khorsandfar.
A ƙarshen watan Disamban da ya gabata, ƙungiyar ƴankasuwa suka fara yajin aiki a tsakiyar birnin Tehran, saboda nuna adawa da faɗuwar darajar kudin ƙasar.
Zanga-zangar ta bazu zuwa yankin yammcin ƙasar da ya fi kowane yankin talauci a ƙasar. Kamar dai ta 2022 lardunan Ilam da Lorestan sun kasance cikin wuraren da ta fi ƙamari.
Masu zanga-zangar da ke akn tituna sun riƙa rera waƙoƙin ''Dama mai kama-karya ya mutu'', inda suke kiran cire jagoran Addinin Ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei da gwamnatinsa.

Asalin hoton, Getty Images
Tasirin Reza Pahlavi
Zanga-zangar 2022 kamar ba ta da shugabanci, lamarin da ya sa aka samu nasarar kwantar da ita da wuri, saɓanin ta yanzu, wadda wasu fitattun mutane ke jagoranta - ciki har da ɗan gidan tsiohon Sha na ƙasar Reza Pahlavi da ke zaman gudun hijira a Amurka - wanda ke ƙoƙarin saita zanga-zangar daga nesa.
Wannan na daga cikin abin da ya sa ake ganin za ta iya jimawa.
A zanga-zangar yanzu, an riƙa jin waƙoƙin kiraye-kirayen komawar Pahlavi ƙasar fiye da a baya.
Pahlavi ya taɓa ayhyana kansa a matsayin sarkin Iran, yayin da yake zaman gudun hijirar.
Mutane da dama sun yaɗa kiraye-kirayen da ya yi na fitowa zanga-zangar.
Matasa da dama a shafukan sada zumunta na ƙarfafa wa juna gwiwa wajen shiga zanga-zangar.
Yawan mutanen da suka fito zanga-zangar a birane kamar Tehran ya tabbatar da amsa kiran Pahlavi.
Barazanar shigar Trump

Asalin hoton, Chip Somodevilla/Getty Images
Wani abu da ya kara ƙarfafa zanga-zangar ta 2025 fiye da na baya shi ne - Amurka.
Wannan zanga-zangar na samun goyon bayan Fadar gwamnatin Amurka, saɓanin na baya.
Shugaba Trump ya yi barazanar kai hari kan hukumomin ƙasar, a wani ɓangare na nuna goyon baya ga masu zanga-zanga - wani abu da ba a taɓa gani ba a baya.
A lokacin zanga-zangar 2009, masu zanga-zangar sun riƙa rera waƙoƙin cewa ''Obama na tare da mu ko da su''
Tsohon shugaban Amurka, Barack Obama - da ke mulki a 2009 - daga baya ya bayyana damuwarsa kan rashin goya wa masu zanga-zangar baya a lokacin.
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce wasu ne daga waje da ya kira ''makiyan'' Iran ke ingiza zanga-zangar.
Ya ce abin damuwa ga ƙasar shi ne yadda ƙasar ta rasa wasu daga cikin abokanta.
Hukumomin Iran sun rasa manyan ƙawayensu kamar Bashar al-Assad shugaban Siriya da aka tumɓuke da ƙungiyar Hezbolla a Lebanon da Isra'ila ta nakasa da yawa.

Asalin hoton, Morteza Nikoubazl/NurPhoto via Getty Images
Zuwanta bayan yaƙin kwana 12
Saɓanin ta 2022, zanga-zangar wannan shekara na zuwa ne jim kaɗan bayan yaƙin kwana 12 da aka gwabza tsakanin Isra'ila da Iran da hare-haren da Amurka ta kai ƙasar.
Abbas Abdi, wani ɗan jarida ne a ƙasar, ya yi imanin cewa lamarin ya bai wa hukumomin Iran damar samun tausayawa da goyon baya tgsakanin al'ummar ƙasar, to amma gwamnatin ta kasa samun hakan.
Wasu ƙwararru na ganin cewa mummunar illar da aka yi wa rundunar sojin ƙasar a shekarar da ta gabata ya rage wa dakarun juyin-juya halin ƙasar - wadda ita ce babbar rundunar sojin ƙasar - ƙarfi.







