Yadda 'yan bindiga suka hana al'ummar Ƙaramar Hukumar Borgu a jihar Neja sakat

'Yan Bindiga

Asalin hoton, OTHERS

Lokacin karatu: Minti 2

Rundunar 'yan sandan jihar Neja ta tabbatar da cewa wasu 'ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen Damala da ke garin Woko a Karamar Hukumar Borgu ta jihar, inda suka kashe aƙalla mutum hudu.

Harin, wanda aka kai a makon da ya wuce, ya zo ne mako guda bayan da wasu 'yan bindigar suka kashe mutane 42, ciki har da na kasuwar Daji da ke ƙauyen Demo, a ƙananan hukumomin Borgu da Agwara da ke makwabtaka da juna.

Mazauna yankunan karamar hukumar sun shaida wa BBC cewa suna zaune cikin fargaba da tashin hankali a kullum.

Mazauna yankunan sun ce saboda hare-haren da 'yan binidgan ke kai wa a yanzu akwai wasu kasuwanni yankin da aka rufe.

Cikin wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya fitar, ya ce maharan sun mamaye ƙauyen Damala ne da tsakar daren Asabar ɗin da ta gabata, inda suka kashe mutum huɗu tare da yin awon gaba da shanun da ba a tantance adadinsu ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa ƴan bindigan sun kuma ƙone wasu shagunan al'umma kafin su tsere daga wurin.

Hare-haren dai na zuwa ne a yayin da rundunar 'yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da kashe wasu ƴan bindiga da dama tare da tarwatsa maboyar su a wani sabon samame da ta kaddamar.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, William Ay, ya fitar, ya ce nasarar ta biyo bayan wani aikin haɗin gwiwa da 'yan sanda da sojoji suka gudanar, tare da tallafin sashen jiragen sama na Rundunar 'yan sandan Najeriya.

A tsakanin watan Oktoba zuwa Disambar 2025, a jihar Kogi an kai hare-hare kan majami'u biyu, lamarin da ya sanya sarkin Kabba, Oba Solomon Owoniyi, tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Kiristoci ta CAN dake Kabba, ayyana dokar dakatar da duk wasu harkokin addini, har zuwa wani lokaci da ba a bayyana ba.

A gefe guda kuma hukumomin tsaro sun ce suna ci gaba da kai samame domin fatattakar 'yan bindiga a yankin arewa maso tsakiyar ƙasar, tare da jaddada aniyar su ta tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al'umma a daukacin faɗin Najeriyar.