Jami'an tsaro sun yi artabu da ƴanbindiga a Mariga da ke jihar Neja

.
Bayanan hoto, Sojan Najeriya
Lokacin karatu: Minti 2

Al'ummomin garuruwan Maigoge da Dan-Auta da Beri na yankin ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja, sun kwana cikin tashin-tashina, har mafi rijayen su sun tsere zuwa cikin dazuka, wasu sun yi gudun hijira, wasu ma ba a san inda su ke ba.

Al'amarin na da nasaba ne da artabun da aka daɗe ana yi tsakanin ƴanbindiga da jami'an tsaron Najeriya a daren Alhamis.

Wani mutumin yankin, wanda ke cikin halin damuwa da firgici a inda ya sami mafaka ya shaidawa BBC cewa alummar yankin sun shiga cikin halin kaka-ni-ka-yi.

''Matanmu da mazajen mu da yaran mu duk basa gari, wasu na Minna wasu na Kontagora wasu na Mariga wasu na Tegina ko wajen gari, wani ma bai san inda yake ba'', in ji shi.

Ya kuma ce wasu da ba su da mota na samun mafaka ne a cikin dazuka ko duwatsu kuma a cikin kashi 100 na mazauna yankin, kashi 90 sun tsere, yayin da kashi 10 ne kawai suka rage.

Hakan dai ya biyo bayan harin da ƴanbindiga suka kai garuruwan uku ne, inda suka kwashi dabbobi masu ɗimbin yawa. Amma kuma jami'an tsaro suka datse su da ɓarin wuta, a cewar mutumin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro.

Kafin nan dai, bayanai daga yankin ƙaramar hukumar ta Mariga ta jihar Nejar, sun ce sai da ƴanbindigan suka ƙaddamar da hari a garin Mongoro, inda aka ce sun kashe mutum fiye da goma, ciki har da jami'in tsaro guda, da ƴan sa-kai uku.

''Halin da ake ciki yanzu ana faɗa da ɓarayin dajin tun daga misalin ƙarfe biyar na yamma, suna son su ƙetara ba su samu dama ba. Jami'an tsaro su na ƙoƙarin ganin cewa sun samu galaba a kan ƴan bindigar''

''Su ƴanbindigar sun fito da shanunmu da suka dauka za su nufi jihar Zamfara inda suka fito, to amma hanyar da ke tsakanin Kontagora zuwa Minna, ta nan ne suke son su ƙetara, amma Jami'an tsaronmu sun taresu da faɗa, suka datse bakin titin, sojoji na saman titin, su suna cikin dutwasu, ana ta ɓarin wuta'', in ji shi.

Wakilin BBC ya yi ƙoƙarin jin ta bakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴansandan Najeriya a jihar ta Neja, SP Wasiu Abiodun ta waya, dangane da batun waɗannan hare-hare, amma ya ce zai bincika.