Sabbin hare-haren Boko Haram: 'Ga sojoji amma rayuwarmu na cikin haɗari'

Asalin hoton, Boko Haram
- Marubuci, Aisha Babangida
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
- Aiko rahoto daga, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 6
Duk da cewa an daɗe ana ganin cewa dakarun Najeriya tare da hadin gwiwar ƙasashen makwabta sun raunana ƙungiyar Boko Haram, hare-haren da ƙungiyar ke kai wa a Najeriya sun ƙaru sosai a cikin shekaru uku da suka gabata.
A cewar binciken da BBC ta yi bisa bayanai daga cibiyar SBM Intelligence – wani kamfani da ke tattara bayanan tsaro a nahiyar Afirka – hare-haren da ake danganta wa Boko Haram sun ƙaru daga 105 a shekarar 2022, zuwa 147 a sekarar 2023, sannan suka kai 191 a shekarar 2024.
A shekarar 2025 kuma, harin farko da Boko Haram ɗin suka kai ya faru ne a ranar 4 ga watan Janairu, lokacin da Boko Haram ta yi wa sojojin Najeriya kwanton ɓauna a kauyen Sabon Gari, inda suka kashe sojoji shida. Kwana tara bayan haka, a ranar 13 ga Janairu, ƙungiyar ta sake kai wani hari a ƙauyen Dumba kusa da Baga, inda ta kashe manoma da masunta 40.
Tun daga wannan lokaci, ƙungiyar Boko Haram ta ci gaba da kai hare-hare a kowane wata a wannan shekara, tare da ƙaruwar yawan su. Wannan yana nuna wata matsala ta sake dawowar tashin hankali, musamman a yankunan karkara da kuma gefen birane.
Boko Haram ta farfaɗo ne?

Asalin hoton, Getty Images
A ranar 8 ga watan Afrilun 2025, gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana damuwa game da dawowar hare-haren Boko Haram da kuma ƙaruwar sace-sacen mutane. Ya ce ƙungiyar na ƙoƙarin dawowa inda sau da dama ta kai hari kan sansanonin sojoji da kashe fararen hula.
"Kashe fararen hula da jami'an tsaro abin damuwa ne matuka, kuma yana nuna koma baya mai girma ga jihar Borno da yankin arewa maso gabas gaba ɗaya," in ji Zulum.
Rahotanni daga jihohin Borno da Yobe na nuna cewa ƙaruwar hare-haren ƙungiyar na nuni da cewa ba a ci galaba ba yadda ake tunani wajen kawar da ƙungiyar.
"Abin da muka gani ba ƙaramin abu bane, yana nuna cewa mutane na fara rasa fata da karfin gwiwa. Kowa na cikin tsoro, zuciya cike da fargaba, mutane na kokarin daidaita tunaninsu," in ji Aliyu Harande, wani mazaunin garin Mafa, cikin hirarsa da BBC bayan harin da aka kai a shekarar da ta gabata.
"Ga mu da muka ɗauka cewa hare-haren Boko Haram ɗin sun lafa, wannan harin ya bayyana mana cewa ba haka bane, harin ya nuna mana cewa suna sake taruwa" in ji shi.
Zanna Umara, wani jami'i a ƙaramar hukumar Tarmuwa, ya shaida wa BBC cewa: "Ba ma fatan dawowarsu, amma ganin irin harin da suka kai a Mafa, yana nuna kamar da gaske suna kokarin dawowa ne."
Dr. Kabir Adamu, shugaban kamfanin tsaro na Beacon Security and Intelligence Limited kuma masani a fannin tsaro ya ce ƙaruwar hare-haren da ake gani a baya-bayan nan na da nasaba da wasu dalilai.
Na farko, in ji shi, shi ne sakin wani umarni daga kungiyar ISIS da ke buƙatar duka rassanta su kara yawan hare-hare, kuma an ga ƙungiyoyi daban-daban suna amsa wannan kiran.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Abu na biyu da Dr. Adamu ya danganta karuwar hare-haren Boko haram da shi shi ne wani yanayi na lokaci.
"Kafin lokacin damina, wadannan ƙungiyoyi sukan ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare, domin sun san ayyukan soji kan ragu a lokacin saboda wahalar hanya da ƙarancin gani," in ji shi.
Ya kara da bayyana cewa rashin zaman lafiya a yankin Sahel na daya daga cikin manyan dalilai. "Tashe-tashen hankula a Sahel, musamman a kasashen Chadi da Nijar da Burkina Faso, sun raunana tsaron iyakoki, hakan ya bai wa waɗannan ƙungiyoyi damar motsawa da ɗaukar sabbin mambobi da samun tallafi cikin sauki," in ji masanin.
Dr. Adamu ya kuma ce sauye-sauyen da aka yi a tsarin rundunar sojin Najeriya sun taimaka wa Boko Haram ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare musamman yadda aka mayar da kayan yaƙi da sojoji daga arewa maso gabas zuwa arewa maso yamma domin sabbin hare-hare.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta ce karuwar hare-haren Boko Haram yana da nasaba da yawaitar ayyukan 'yan tada ƙayar baya a ƙasashen makwabta.

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da mutanen karkara – waɗanda su ne mafi yawan wadanda hare-haren ya fi shafa ke ci gaba da jimamin rasa 'yan uwa da kuma ƙoƙarin farfadowa da rayuwarsu, suna yin hakan ne cikin fargaba da rashin tabbas kan lokacin da hari na gaba zai iya faruwa.
'Ya'yana suna cikin tsananin fargaba, kuma ba mu da tabbas ko komawa gida shi ne zai fiye mana zaman lafiya. Duk da cewa akwai sojoji, ji nake yi rayuwata tana cikin haɗari," in ji Hajara Idris (ba sunanta na gaske ba), lokacin da take magana da BBC bayan harin da aka kai a Mafa.
Ba ita kaɗai ce ke cikin wannan halin ba. Fatima Bukar (ba sunanta na gaske ba) ma tana da irin wannan tsoro, inda ta ce: "Harin ya bar mana rauni a zuciya. Mun ga abubuwan da ba mu taɓa zato ba, kuma yanzu ji muke muna cikin babban haɗari. Duk da kasancewar sojoji a nan, kullum da dare ina jin tsoron cewa Boko Haram za su dawo."
Za a tura ƙarin sojoji arewa maso gabas

Asalin hoton, Getty Images
Majalisar dattawan Najeriya ta amince da bukatar tura karin jami'an sojoji a shiyyar arewa maso gabas a jahohin Borno da Yobe domin yaki da mayakan Boko Haram wadanda ke ci gaba da zafafa hare-hare a kwanan nan, inda suka kashe gomman sojoji a kananan hukumomin Marte da Moguno dake jihar Borno.
Wannan dai na faruwa ne bayan wani kuduri da Sanata Muhammed Tahir Monguno dan majalisar dattawa mai wakiltar Borno ta arewa, ya gabatar a gaban majalisar.
Sanatan ya ce ya gabatarda kudurin ne ganin yadda matsalar tsaron take neman sake komawa kamar da.
Ya ce a lokacin da ake tsananin fama da Boko Haram wajen kashi biyu cikin kashi uku na kananan hukumomin jihar Borno suna karkashin ikon kungiyar Boko Haram.
''Boko Haram na rike da kananan hukumomin, sun kori hafsoshinmu, su ke rike da ikon duka wadannan yankuna,'' in ji shi.
Danmajalisar dattawan ya kara da cewa, to amma bayan wani lokaci gwamnati ta tashi tsaye an bayar da duk wani abu da ake bukata har sojoji suka yi nasarar korara Boko Haram daga wadannan yankuna.
''Gwamnan jiharmu ya yi kokarin mayar da mutane tare da samar musu abubuwa na jin dadin rayuwa suka koma suna noma da sauran ayyukansu na yau da kullum, sai kuma yanzu Boko Haram suka fara dawowa, suna kai hare-hare,'' ya ce.
Ya kara bayani da cewa matsalar tana neman dawowa ne, saboda 'yan Boko haram sun fahimci cewa an kwashe yawancin sojoji da kayan aiki an mayar da su yankin arewa maso yamma inda ake fama da matsalar tsaro ta barayin daji.
Ya ce wannan shi ya sa mayakan Boko Haram suka fahimci haka shi ya sa yanzu suka samu damar kai hare-hare inda a cikin 'yan kwanakin nan suka kai hari sansanin soji da ke Marte da kuma Gajiram.
''Har ma suna samu su kai hari, inda yanzu shekaran jiya sun kai hari a Marte sun kashe wajen sojojinmu bakwai sun kai hari Gajiram ba su samu sun yi nasara ba,''
''Kuma in haka ya yi yawa duk wani aiki da gwamnanmu ya yi na mayar da jama'a kauyukansu da samar da kayayyaki duk zai zama aikin banza. Kuma bayan haka su Boko Haram sun fara amfani da jirage marassa matuka'' in ji shi.











