Me kalaman gwamna Zulum kan dawowar hare-haren Boko Haram ke nufi?

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya nuna damuwa kan yadda jihar ke rasa wasu yankunanta sakamakon hare-haren ƙungiyar Boko Haram a baya-bayan nan.
Zulum ya bayyana haka ne ranar Talata a wani taro kan harkar tsaro da ya kira domin tattauna batun.
A makonnin baya-bayan nan ma, wasu da ake zargi ƴan ƙungiyar ta Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya da dama, yayin da wasu da dama suka jikkata a jihar - a hari da suka kai Wajirko a Damboa da sansanin soji na Wulgo a Gamboru Ngala.
Jihar dai ta shafe tsawon shekaru tana fama da matsalar Boko Haram, wanda ya janyo asarar rayukan gomman mutane da kuma ta dukiya.
Me Zulum ya faɗi?

A jawabin da gwamnan ya yi a taron majalisar tsaron jihar da ya kira ranar Talata, ya ce abin takaici shi ne yadda sabbin hare-haren Boko Haram da satar mutane a kowace rana.
Zulum ya ce gwamnatinsa ta kasance tana taimakawa sojoji a yaƙi da suke yi da Boko Haram da kuma ƴan ta'adda na tsawon shekaru, abin da ya sa aka samu saukin lamarin, sai dai a yanzu matsalar na ƙoƙarin dawowa sabuwa.
"Abin damuwa ne matuka yadda maharan suka far wa sansanonin sojoji a garuruwan Wajirko da kuma Sabon gari a karamar hukumar Damboa, da Wulgo a Gamborun Ngala da Izge a karamar hukumar Gwoza da kuma sauran yankuna.
"Kashe fararen hula da ba su ji ba su gani ba da kuma wasu jami'an tsaro abin damuwa ne ainun kuma koma-baya ne a jihar Borno da kuma arewa maso gabas," in ji gwamna Zulum.
Yayin da yake yaba wa gwamnatin Tinubu kan goyon baya a yaƙi da Boko Haram, ya yi kira da a ƙara ƙaimi da kuma samar da kayayyakin yaƙi na zamani ga sojoji domin daƙile barazanar sabbin hare-haren, waɗanda suka addabi jihar wadda ke makwabtaka da ƙasashen Afirka uku da suka haɗa da Chadi da Nijar da kuma Kamaru.
'Kalaman Zulum hannunka mai sanda ne ga jami'an tsaro'
Kalaman da gwamna Zulum ɗin ya yi a taron majalisar tsaro na jihar sun janyo samun mabambamtan ra'ayoyi daga jama'a.
Sai dai a Kabiru Adamu, masani kan harkokin tsaro a Najeriya da yankin Sahel, ya shaida wa BBC cewa kalaman na Zulum jan hankali ne ga jami'an tsaro da ke yaƙi da matsalar Boko Haram.
"Hannunka mai sanda ne yake yi ga jami'an tsaro na cewa nasarar da aka samu a yaƙi da Boko Haram da kuma ISWAP bai wadatar ba, dole a ƙara ƙaimi. Saboda ƙungiyar ta fara numfasawa inda take kai manyan hare-hare a jihar," in ji Kabiru Adamu.
Ya ce kalaman gwamnan wani babban kira ne gare su na cewa su ci gaba da ƙoƙari, kada su ba ri a koma gidan jiya - inda ƙungiyoyin suka mamaye garuruwa kusan huɗu.
'Idan aka yi sakaci Boko Haram za ta iya farfaɗowa'
Masanin kan harkokin tsaro ya kuma ce irin iskar da ƙungiyoyin ta'addanci ke shaƙa, za ta sa su ci gaba da cin karensu babu babbaka.
"Idan ba a daƙile hanyoyin da suke samun kuɗaɗe da makamai da damar ɗaukar sabbin mayaƙa, to fa ƙungiyoyin suna nan daram," in ji masanin.
Ya ƙara da cewa kashe manyan su da wasu da ke miƙa wuya kaɗai ba zai wadatar ba, har sai an kuma kyautata tsaro kan iyakoki da kuma magance saɓani tsakanin ƙasashe da ke ƙoƙarin magance matsalar ta Boko Haram.
"Indai ba a magance wannan ba, to za a ci gaba da samun matsaloli.
Ya kuma ce dole ne a saka gwamnoni wajen yaƙi da matsalar ta Boko Haram da kuma na ƴan bindiga.











