'Tsananin zafi ne ya haifar da fashewar abubuwa a barikin sojoji a Maiduguri'

Asalin hoton, Dandal Kura
Hedikwatar rundunar haɗin gwiwa da ke yaƙi da Boko Haram ta a Maiduguri ta sanar da cewa fashewar abubuwa a rumbun makamai a barikin soji na 'Giwa barracks' ta faru ne sakamakon tsananin zafi da birnin ke fuskanta.
Wata sanarwa mai ɗauke da sahannun Kaftin Reuben Kovangiya, ta ce tuni jami'an kashe gobara suka kashe gobarar.
Gobarar dai wadda ta janyo fashewar abubuwa tare da haddasa fargaba a tsakanin al'umma a Maiduguri saboda ƙara mai ƙarfin gaske da aka ji a ƙwaryar birnin da kewaye, ta faru da daren Laraba.
Mazauna birnin Maiduguri sun shiga zullumi sakamakon tashin gobarar, inda galibin jama'a suka zaci cewa 'yan Boko Haram ne suka kai hari.
Hukumar da ke kula da kashe gobara ta jihar Borno a cikin wata sanarwa, ta ce gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 10 da rabi na dare a ranar Laraba, inda ta lalata rumbun adana makamai na barikin sojojin.
Daga bisani 'yan kwana-kwana sun samu nasarar kashe gobarar.
Binciken farko da hukumomi suka yi kan musababbin tashin gobarar, ya gano cewa tsananin zafi a Maiduguri na da alaƙa da tashin gobarar.
A shekara ta 2014 ne, ƙungiyar Boko Haram ta kai hari a barikin sojoji na Giwa lamarin da ya janyo hasarar rayuwa da dama.











