Me harin ISWAP na Borno da ɗaukar alhakinsa ke nufi?

Asalin hoton, AFP
A karon farko a tsawon shekaru ƙungiyar mayaƙan ISWAP ta ɗauki alhakin kisan mutum 26 a wani harin bam da ta dasa a garin Rann a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Ƙungiyar ta yi wannan iƙirari ne a shafinta na Telegram.
Lamarin dai ya faru ne ranar Litinin bayan da wata mota ta taka bam a gefen hanya a garin na Rann da ke iyaka da jamhuriyar Kamaru.
Hakan na zuwa ne kimamin mako biyu bayan da wata motar bas ta taka wani abin fashewa da aka binne a yankin, abin da ya janyo mutuwar fasinjoji takwas da kuma raunata wasu 11.
Ƙungiyar Boko Haram da ISWAP sun shafe tsawon shekara 15 suna kai hare-hare da kuma artabu da jami'an tsaron Najeriya a arewa maso gabas.
Sun sha amfani da abubuwan fashewa wajen afkawa fararen hula da kuma jami'an tsaro.
Me hakan yake nufi?
Malam Kabiru Adamu, masani kan tsaro a Najeriya da yankin Sahel kuma shugaban kamfanin da ke samar da bayanan tsaro na Beacon Security and Intelligence Limited ya ce harin da Iswap ta kai bai da ɗaukar alhakin kai wa ba zo musu da mamaki ba.
"Duk da munin wannan hari amma bai ba mu mamaki ba saboda mun ga yadda a baya-bayan nan yadda ita ƙungiyar ISWAP da ta Boko Haram suka ƙara ƙaimin kai hare-hare a wurare da dama ciki har da yadda suke amfani da dasa bama-bamai da kuma yadda suke kai hare-haren.
A taƙaice dai wannan harin da ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula yana cikin irin hare-haren da ƙungiyoyin ke kai wa a baya-bayan nan masu jimurɗa da ake kira da 'complex attacks'." In ji Malam Kabiru Adamu.
Masanin ya kuma ƙara da cewa "lallai hare-haren Iswap da na Boko Haram sun dawo a yankin arewa maso Gabas, inda a yanzu haka suke abin da suka ga dama a ƙananan hukumomi guda uku na jihar ta Borno."
A baya-bayan nan ne dai gwamnan jihar Borno, Farfesa Umar Zulum ya koka dangane da komen da hare-haren ƴan Boko Haram suka yi a jihar.
Rundunar sojojin Najeriya ta fara shiri

Asalin hoton, NDHQ/X
Rundunar sojin Najeriya ta naɗa Manjo-Janar Abdulsalam Abubakar a matsayin sabon kwamandan dakarun Operation Hadin-Kai mai yaƙi da ta'ddanci a arewa maso gabas.
Naɗin nasa na zuwa ne bayan dawowar sabbin hare-hare a yankin a watanni huɗu da suka gabata - waɗanda suka janyo mutuwar fararen hula da dama da kuma sojoji.
Wata sanarwa da rundunar sojin Najeriyar ta fitar, ta ce Janar Abdulsalam shi ne kwamanda na 15 na dakarun Haɗin-Kai da ke yaƙi da Boko Haram da kuma ISWAP a yankin arewa maso gabas.
Abubakar ya riƙe mukamin mataimakin kwamandan kwalejin tsaro da kuma kwamandan wata rundunar tsaro a arewa maso tskakiyar Najeriya.
Boko Haram da takwararta ta ISWAP sun zafafa kai hare-hare a baya-bayan nan a yankin.
Hakan ya janyo fargabar dawowar hare-haren masu iƙirarin jihadin, waɗanda a yanzu ke amfani da jirage marasa matuki da kuma abubuwan fashewa a kan hanyoyi, a cewar wani ƙwararre kan harkar tsaro.
Ko naɗin kwamandan yaƙi ka iya sauya al'amarin?
Dangane da naɗa sabon kwamandan yaƙi da ta'addanci, Malam Kabiru Adamu ya ce"wannan ba sabon al'amari ba ne. Lalle irin wannan sauyi na taimakawa wajen sabunta yanayin tsaro kasancewar batun taɓrɓarewar harkar tsaro ne abin da ƴan Najeriya suka fi tattaunawa a kai."
Sai dai kuma Malam Kabiru ya ce "inda gizo ke saƙar shi ne rashin waiwayar inda ake da kuma tambayar mece ce matsalar wato mene ne ke hana cigaba wajen burin kawo karshen matsalar ta'addanci."
Masanin ya bai wa sabon kwamandan shawarar waiwayar dokoki da tsare-tsare da kundin yaƙi da ta'addanci na Najeriya da kuma sanya dukkan masu ruwa da tsaki a al'amrin domin samar da mafita.











