Yadda ake watsar da jarirai a titi sanadiyyar yawan fyaɗe a yaƙin Sudan

Asalin hoton, Plan International / Abdelazim Yousif
- Marubuci, Kate Bowie
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Global Health, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 3
Rahotanni sun nuna cewa a Sudan ana samun ƙarin jariran da aka watsar yayin da ƙasar ke cika kwanaki 1,000 cikin rikici.
Masu rajin kare haƙƙin bil'adama sun ce a wasu yankuna, ana yi wa aƙalla mace ɗaya fyaɗe a kowace sa'a, yayin da likitoci ke cewa kusan kashi biyu bisa uku na mata da aka yi wa fyade sun kamu da cututtukan da ake kamuwa da su ta hanyar jima'i.
Mata da suka fuskanci fyade suna kuma fama da rashin samun kulawa lokacin haihuwa da abinci da sauran abubuwan bukata na yau da kullum, in ji ma'aikatan ƙungiyoyin agaji.
Tun daga Afrilun 2023 ne yaƙi ya ɓarke tsakanin Sudan da dakarun RSF.
An zargi duka ɓangarorin da aikata laifukan yaƙi.
A halin da ake ciki, fiye da mutum miliyan 11 ne suka bar muhallansu inda kuma dubban mutane sun mutu tare da amfani da cin zarafi ta hanyar lalata a matsayin makamin yaƙi, abin da Majalisar Dinkin Duniya ta kira mafi girman rikicin jin kai a duniya.
Binciken Majalisar Ɗinkin Duniya ya zargi RSF da aikata mafi yawan fyaɗen inda aka ce suna amfani da fyaɗe wajen tsoratar da fararen hula da murƙushe masu adawa. Zargin da RSF ta ƙaryata.
Nahid Ali, wata ma'aikaciyar jin ƙai a Sudan ta ce mata matasa sun fi fuskantar wannan tashin hankalin.
Ta ce: "Na haɗu da 'yan mata da mata da aka yi wa fyaɗe a gaban iyalansu har da waɗanda aka yi wa fyaɗe a hanyoyi yayin da suke tserewa daga tashin hankali.
A yayin wata ziyara a babban sansanin 'yan gudun hijira a arewacin Sudan, Ali ta haɗu da wata yarinya mai shekaru 18 da ta samu ciki sakamakon fyaden gungun maza.
Ta ce: "Mutum ma ba zai iya tunanin yadda take ji ba a yanzu kuma tana buƙatar kulawa ta musamman wajen haihuwar jaririnta."
Amma ta yi gargaɗi cewa saboda ma'aikatan lafiya a sansanonin gudun hijira suna fama da cututtuka kamar zazzaɓin cizon sauro da kwalara, kulawar lafiya ga mata masu ciki tana da wahala sosai lamarin da ke barin rayuwar matan da suka samu ciki sakamakon fyaɗe cikin haɗari.
Mata na ceto rayuka
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A yankin Darfur na yammacin Sudan, barazanar fyaɗe ta ƙaru sosai cikin kwanaki 1,000 na rikicin ƙasar in ji Hala al-Karib, daraktar yanki ta SIHA, wata ƙungiya da ke tattara bayanai kan yawaitar fyaɗen.
"Ana yi wa aƙalla mace ɗaya fyade a kowace sa'a a Darfur," in ji ta.
"Sabbin hanyoyin tashin hankali na cin zarafi ta hanyar lalata suna bayyana a gaban idonmu," ta ƙara da cewa mata masu shekaru daban-daban ciki har da yara da tsofaffin mata.
Ta ce yawancin jariran da aka haifa sakamakon fyade ana watsar da su a asibitocin yankin.
Haka kuma, likitocin da ke kula da waɗannan mata sun shaida mata cewa kusan kashi 65 na marasa lafiya da aka yi wa fyaɗe sun kamu da cututtukan da aka kamuwa da su ta hanyar jima'i (STIs).
Daga cikin waɗannan cututtuka akwai cutar sanyi ta syphilis da cutar hanta da kuma cuta mai karya garkuwar jiki, duk waɗannan na iya zama babban haɗari idan ba a samu magani ba.
Rashin ingantaccen tsarin lafiya ya bar yawancin waɗanda abin ya shafa ba tare da kulawar haihuwa ko maganin STIs ba.
"Cibiyoyin kiwon lafiya da ake da su sun lalace sosai kuma ba sa bayar da isasshen kulawa," in ji Al-Karib.
Amma duk da wannan rikici, mata a Sudan har yanzu suna taimakawa al'ummominsu.
"Duk da dukkan ƙalubale da tashin hankali, mata suna ƙoƙarin ceto rayuka," in ji ta.
"Na haifi ɗa na ba da jimawa ba rikici tsakanin sojin Sudan da dakarun RSF ya ɓarke kwanaki 1,000 da suka wuce kenan" in ji ma'aikaciyar jin kai Ali.
"Ba zan iya raba aikin da nake yi na jin ƙai ba da rayuwata ba, waɗannan mutane namu ne, muna ƙoƙarin taimaka musu kuma ba za mu yi watsi da su ba," in ji ta.











