Bam ya halaka mutum 26 a jihar Borno

Duk da cewa al'ummar yankin sun ɗora laifin kan ƙungiyar Boko Haram amma har kawo yanzu hukumomin tsaro ba su ce uffan ba.

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Rahotanni daga arewa maso gabashin Najeriya na cewa aƙalla mutum 26 ne suka rasu ranar Litinin sakamakon tashin wani bam da motar da suke ciki ta taka a kan hanyar da ke tsakanin garin Rann zuwa Gmaboru Ngala.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewa mutanen da abin ya rutsa da su sun haɗa da maza 16 da mata huɗu da ƙananan yara guda shida.

Bam ɗin da ake zaton ƙungiyar Boko Haram ce ta dasa binne shi, ya kuma jikkata aƙalla mutum da dama waɗanda suke asibiti domin samun kulawa.

Duk da cewa al'ummar yankin sun ɗora laifin kan ƙungiyar Boko Haram amma har kawo yanzu hukumomin tsaro ba su ce uffan ba.

An kashe mutum bakwai a yankin Chibok

Mayakan Boko Haram

Asalin hoton, BOKO HRAM

A wani harin kuma na daban, mayakan Boko Haram ɗin sun halaka akalla mutum bakwai a wani hari da suka kai garin Koful da ke yankin karamar hukumar Chibok a jihar Borno, ta arewa masu gabashin Najeriya.

Mayakan sun dirar wa mutanen ne yayin da suke tsaka da zaman makokin wani mutumin da ya rasu, bayan yin jana'izarsa, inda suka bude wuta tare da bankawa wasu mujami'u da gidaje wuta.

Shugaban karamar hukumar ta Chibok, Mallam Modu Mustapha, wanda ya tabbatar wa da BBC afkuwar lamarin, ya ce mayakan sun kai harin ne da misalin karfe biyar da yammacin Litinin.

''Jiya ne da misalin karfe biyar da wani abu akwai rasuwa da aka yi ana wajen makokin rasuwa kawai a ankara kawai sai ga mashina, sai harbi kawai,'' in ji shugaban.

Ya kara bayani da cewa : ''Mutane sun tashi sun fara guduwa, ana binsu kamar dabbobi a jeji ana ta harbe su, ana ta kone-kone har Mangariba ta wuce mayakan Boko Haram suna nan sai da sojoji suka dawo sannan suka tafi.''

Mallama Modu ya ce an dan dauki lokaci kamar wata biyu mayakan na Boko Haram ba su kai musu harin ba sai a yanzu da suka kai musu wannan na ranar Litinin.

Ya ce mayakan sun yi wa garin dirar-mikiya ne a babura dauke da makamai, inda shigarsu ke da wuya suka nufi inda ake wannan zaman makoki suka bude wuta, mutane suna gudu suna binsu suna harbewa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayan wadanda suka rasu wasu kuma sun jikkata, ga kuma kone-konen da suka yi na coci-coci da sauran gidajen jama'a.

Shugaban ya tabbatar wa da BBC cewa mayakan sun shiga garin ne daga bangaren Dambuwa.

Ya ce har zuwa lokacin da yake wannan bayani wasu mutanen da suka warwatsu a jeji ba su komo ba.

''Kafin wannan hari al'ummar wannan yanki wadanda manoma ne da makiyaya suna gudanar da harkokinsu cikin walwala da komai,'' ya ce.

Daman a baya-bayan nan hatta hukumomin jihar ta Borno sun tabbatar da cewa hare-haren mayakan Boko haram da sauran kungiyoyi masu ikirarin jihadi na kara dawowa bayan sun lafa na wani dogon lokaci da har an fara mayar da mutanen da suka yi gudun hijira a sakamakon rikicin.

Gwamnan jihar ta Borno, Babagana Umara Zulum ya nuna damuwa kan yadda jihar ke rasa wasu yankunanta sakamakon hare-haren kungiyar Boko Haram a baya-bayan nan.

Zulum ya bayyana haka ne yayin wani taro kan harkar tsaro da ya kira domin tattauna batun.

A makonnin baya-bayan nan ma, wasu da ake zargi ƴan Boko Haram ne sun kashe sojojin Najeriya da dama, yayin da wasu da dama suka jikkata a jihar - a hari da suka kai Wajirko a Damboa da sansanin soji na Wulgo a Gamboru Ngala.

Jihar ta Borno ta shafe tsawon shekaru tana fama da matsalar Boko Haram, wanda ya janyo asarar rayukan gomman mutane da kuma ta dukiya.