Zaɓen Najeriya 2023: Shin Buhari ya yi maganin Boko Haram?

Children in Potiskom

Asalin hoton, Ayo Bello/ BBC

Bayanan hoto, Duk da yanayin tsaro ya inganta a arewa maso gabashi - amma har yanzu mutane da yawa ba za su koma ba.

Yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ke neman takarar shugabancin Najeriya shekara takwas baya, ya zo da alƙawarin cewa zai taimaka wajen kawo karshen matsalar Boko Haram wanda ya tilastawa Miliyoyin mutane barin muhallansu daga arewa maso gabashin ƙasar zuwa wasu yankuna.

Yanzu shekara takwas kenan da wannan alƙawarin kuma yanzu ya samu zaman lafiya, kuma an kwato wasu yankuna masu girma wanda a baya mayaƙan Boko Haram suka ce sun ƙwace su. Sai dai yayin da 'yan Najeriya ke ƙoƙarin zaɓar magajinsa, halin da ake ciki cike yake da ru ɗani.

Ruƙayya Goni wadda ke zaune kusa da wata makarantar firaimare da masu iƙirarin jihadin suka ƙona, lokacin da suka ƙwace yankin Damasak a ƙarshen 2014.

Manufar Boko Haram dai ita ce "ilimin boko haramun ne" kungiyar ta sha kai hare-harenta kan makarantun da babu ruwansu da addini, tare da sace sama da 'yan makaranta 200 daga garin Chibok.

Shekara tara da ta gabata, Ruƙayya ta gudu daga gidanta tare da iyalanta su 11, inda suka tsallaka iyakar da take kusa da su ta ƙasar Nijar.

"Mun gudu ne saboda matsalar tsaro da Boko Haram ta janyo" ta bayyana da yaren Kanuri, kuma wani mai fassara ya fassara. "Sun kwace Damasak shi yasa muka tsallaka Diffa, da ke Nijar." A lokacin tana da 'yarta 'yar shekara shida da haihuwa. Ta haifi duka 'ya'yanta maza biyar a Nijar daga baya kuma ta koma Damasak a bara.

"Mun ji cewa komai ya daidaita a yanzu, shi yasa muka yanke shawarar mu koma gida," kamar yadda ta yi bayani. Na tambayeta ko ta taɓa tunanin komowa gida. "Eh muna ta fatan komawa gida, kullum sai mun yi addu'ar zaman lafiya. Na ji daɗin koma. Babu wani wuri da ya fi gida.

Rukaiya Goni

Asalin hoton, Kyla Herrmannsen/ BBC

Bayanan hoto, Rukaiya Goni na zaune ne a Nijar da ke maƙwaɓtaka da Najeriya na tsawo shekaru, amma a ƙarshe ta koma Damasak inda gida ne a gareta.

Duk lokacin da aka tambayi Shugaba Buhari da magoya bayansa game da tsaron yankin sai su ce, yanayin tsaro ya fi na lokacin baya da suka karɓi mulki.

Idan aka yi la'akari da mutane irinsu Ruƙayya da suka koma gida za ka iya cewa iƙirarunsu na kan daidai. Sai dai har yanzu saman lafiya ya yi wa yankin nisa.

"Matsalar tsaro har yanzu na kaikawo a yankin, kuma mafi mahimmanci shi ne yana shafar mutanen da suke nan domin taimakawa," in ji David Stevenson, daraktan hukumar abinci ta duniya a Najeriya.

"Suna ci gaba da tserewa, akwai sabbin da suka zo amma suna shaida mana ba sa jin cewa suna da aminci a nan ko a wuraren nomansu."

Kungiyoyin masu iƙirarin jihadi irinsu Boko Haram, har yanzu suna da barazana kan tsaro a Borno duk da cewa ba su da yankuna da yawa a ƙarƙashinsu.

Akwai yankunan jihar da dama da ake ganin suna da haɗari idan za a shige su a mota. Idan har kana son zaman lafiya daga Damaturu da ke Yobe zuwa Maiduguri babban birnin Borno sai dai ka tafi a jirgin saman MDD.

Kungiyar ISWAP da ta ɓalle daga Boko Haram shkaru bakwai baya, ita ma na ƙara zama babbar barazana. A 2022 ta yi iƙirarin kai hare-hare sama da na kowacce ƙungiya tun bayan kafata, kuma a nitse ta kama yankin Tafkin Chadi mai mahimmanci.

Akwai bayanai da ke cewa ayyukan ƙungiyar sun fara tsallakawa yankin arewa maso yammacin ƙasar, inda suka haɗa kai da gungun masu satar mutane.

Kundin tsarin mulkin Najeriya ya haramtawa Buhari sake takara, amma rashin kakkaɓe matsalar tsaron da ke addabar ƙasar da kuma yadda matsalar ke yaɗo ya sanya mutane a arewacin Najeriya sanya ayar tamabaya a kan jam'iyyarsa ta APC.

A jihar Kano ɗaya daga cikin manyan garuruwan kasuwanci a yankin Afrika ta Yamma, wani ɗan kasuwa Muktar Garba Intini ya ce ba zai zaɓi APC ba.

Millet seller Mukhtar Garba Intini

Asalin hoton, Kyla Herrmannsen/ BBC

Bayanan hoto, Mukhtar Garba Intini baya son APC ta ci mulki

"Ƙarƙashin mulkin APC mun sha wuya, shi yasa muke addu'a PDP ta dawo," in ji Malam Intini. Yana siyo hatsin da yake kasuwancinsa ne daga Maiduguri, ko da yaushe cikin fargabar matsalar tsaro yake.

"Rashin tsaro matsala ne, akwai mutanenmu da yawa da suka tafi Maiduguri har yanzu ba ma jin ɗuriyarsu, kullum addu'a muke musu."

Rashin tsaron wani abu ne da matafiya a kullum ke fuskanta. Duk lokacin da muke tafiyar kilomita 300 daga gabashin zuwa Potiskum a Yobe, sai dai mu yi amfani da mota mai sulke, tun da masu garkuwa da mutane sun mamaye titinan namu.

Faded Boko Haram graffiti on a wall in Damasak

Asalin hoton, Kyla Herrmannsen/ BBC

Bayanan hoto, A iya cewa an ci ƙarfin Boko Haram, amma tasirinsu har yanzu yana nan a yankin

Gazawar Buhari wajen magance matsalar tsaro shi ne dalilin da magoya bayan Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP mai adawa suke ganin ya kamata a ba shi wannan damar a wannan karon. Ganin cewa shi kaɗai ne ɗan takarar da ya fito daga yankin.

Dolly Kola-Balogun 'yar ksuwa ce kuma magoyin bayan PDP da ke zaune a Abuja babban birnin Najeriya.

"Ba na goyon APC saboda sun kasa a ganina a mataki na ƙasa. Sun kasa kawo ƙarshen rashin tsaro a arewa maso gabas, kuma yanzu ga matsalar garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa.

Tana ganin mutanen da suka yi rijistar zaɓe da niyyar zaɓen suna da yawa, duk da cewa ya girmi duka 'yan takarar da ce neman shugabancin ƙasar, ya kai shekara 76. Kimanin kashi 40 cikin miliyan goma sabbin masu rijistar matasa na 'yan ƙasa da shekara 35 ne, kuma kusan duka Atiku suke so.

Zaben Najeriya 2023: Waɗanne alƙawura ne jam'iyyu suka yi muku

Zaɓi wani batu da jam'iyya domin ganin tsare-tsare

Tsare tsaren Jam'iyyu

  • All Progressives Congress

  • Labour Party

  • New Nigeria Peoples Party

  • Peoples Democratic Party

End of Zaben Najeriya 2023: Waɗanne alƙawura ne jam'iyyu suka yi muku

Mutum miliyan 49 ne suka yi rijistar zaɓe, kuma kusan rabinsu suna zaune ne a yankin arewacin Najeriya, kamar yadda aka saba kuma masu fitowa su yi zaɓe a yankin sun fi yawa idan aka kwatanta da garuruwan da suke kudancin ƙasar kamar su Legas. Kuma idan mutum iya cin yankin za a iya sa masa ran lashe zaɓe.

Wani koma bayan da APC za ta sake fuskanta shi ne mutum miliyan 1.6 da ke gudun hijira a Borno, saboda yaƙin Boko Haram.

Damasak IDP

Asalin hoton, Ayo Bello/ BBC

Bayanan hoto, Sama da mutum miliyan ɗaya ne ke gudun hijir a Borno

Hauwa Goni tana da shekara 25 a duniya, ta kuma bar ƙauyensu na Dikwa da ke Borno shekara bakwai baya. "Boko Haram sun riƙa kashe mazajen mutane tare da sace wasu da yawa, shi ya sa na yanke shawarar na gudu tare da mijina." Kamar yadda ta yi bayani.

Bayan ta ɗan zauna a Maiduguri sai ya yi ƙoƙarin koma Laegas ɗaya daga cikin manyan biranen ƙasar mafi girma tana da fatan samun rayuwa mai kyau, amma shekara ɗaya kawai ta iya zama.

"Rayuwar ta tsauri da yawa, ga tsada, ba za mu iya ci gaba da zama ba a nan". In ji Hauwa.

Yanzu ta koma Maiduguri, amma an daina kai kayan agaji sansanin da suke, wannan wani mataki ne da gwamnatin APC mai mulki a jihar ta ɗauka domin karfafa gwiwar 'yan gudun hijira domin su koma gidajensu.

Hawa Goni and her daughter Amina

Asalin hoton, Ayo Bello/ BBC

Bayanan hoto, 'Yar Hawa Goni na da wata tara da haihuwa a yanzu kuma tana fama da cutar tamowa

Babu ko ɗaya da kai tsaye ya lissafa Boko Haram ko Iswap a cikin manufofinsa. Sun fi magana kan yadda za su kawo ƙarshen masu iƙirarin jihadi baki ɗaya.

Ɗan takarar jam'iyyar APC Bola Tinubu ya ce yana son ƙirƙirar "wata tawaga da za a bai wa horo da kuma tawagar yaƙi da 'yan ta'adda da dakaru na musamman." Domin neman goyon bayan mutanen da wannan bala'i ya shafa ya ce zai smar musu da taimakon gaggawa da na bangare tattalin arziki.

Atiku Abubakar yace zai kawo ƙarshen wannan matsala ta hanyar amfani da wani zaɓi na daban domin warware rikicin ta hanyar diflomasiyya, leƙen asiri, karɓe iko da iyakoki amfani da tsarikan al'ada da kuma haɗa hannu da makotan ƙasashe." Kuma yana so ya kai ci gaba yankin arewa maso gabas.

Shi ma haka ɗan takarar jam'iyyar Labour Peter Obi ya yi maganar zai nemi haɗin kan yankin domin ƙarfafa tsaron kan iyaka, da kuma " gabatar da masu aikata laifuka da 'yan bidiga da 'yan ta'adda wanda hakan zai iya kawo ƙarshen masu aikata laifi ba tare da an hukunta su ba".

Babu wanda ya yi bayanin nawa hakan zai iya laƙumewa a hukumance ko kuma ta yaya za su samo kuɗin yin aikin.

Amma ko wanene ya gaji Buhari na da buƙatar shiri na gaske domin tabbatar da alƙawarin da ya yi shekara takwas baya.

map of Nigeria