'Yan Boko Haram sun hallaka mutum 14 a jihar Borno

Boko Haram

Asalin hoton, OTHERS

Lokacin karatu: Minti 3

Mayakan Boko Haram sun halaka mutum goma sha hudu da jikkata karin hudu, yayin da har yanzu ba a san inda wasu suke ba, bayan wani hari da suka kai kan wasu manoma a yankin Goza na jihar Borno ranar Asabar.

Harin ya auku ne yayin da ake kokarin ganin an mayar da jama'ar yankin garuruwansu don su ci gaba da rayuwa, bayan kwashe shekaru da dama suna gudun hijira a wasu wurare saboda hare-haren na 'yan Boko Haram.

Sanata Muhammad Ali Ndume, mai wakiltar shiyyar Borno ta Kudu a majalisar dattawan Najeriya, shi ne ya tabbatar wa da BBC hakan a wata tattaunawa.

Ya ce : ''Bayananin da na samu daga wajen ciyaman wato shugaban karamar hukuma shi ne jiya Asabar din nan mutane sun je gona don su sare itace da kuma su share gona ana son maganar a yi noma sai Boko Haram suka afka musu sun kashe mutum 14, wanda aka riga an yi jana'izarsu kenan.''

''To amma har yanzu ma mutane dai ba a gama tantancewa ba don yadda na samu labari sojoji sun je wurin ana so a samu kididdigar mutane nawa ne suka rasa rayukansu amma wanda mun sani guda hudu sun ji ciwo sun jikkata an kawo su asibiti sannan zuwa nan gaba za mu samu cikakken bayani kan abin,'' in ji Sanatan.

Dan majalisar dattawan ya yi karin bayani da cewa, ''an kai harin ne a tsakanin wasu garuruwa uku - Fulka zuwa wani kauye Bokko da kuma ta gefen hagu akwai Kirawa.''

''To inda ma suke fitowa wanda an sani ana kiran kauyen Bilei to daman can ne kamar burtalin Boko Haram,'' ya ce.

Ndume ya kara bayani da cewa lamarin ya faru ne kasancewar ana samun lafiya kuma gwamnan jihar ta Borno yana kokarin ganin mutane sun koma garuruwansu da zama don ci gaba da rayuwarsu da suka saba.

Ya kara da cewa : ''To wannan ne ya sa mutane suka je gonakinsu su share kuma su samu itacen da za su yi amfani da shi a gida sai Boko Haram suka afka musu.''

Ndume ya ce ko a ranar Juma'a gwamnan jihar Babagana Umara Zulum a matsayinsa na babban mai kula da tsaro na jihar ya yi gargadi a kan halin da ake ciki a wannan yanki, musamman wurare guda uku.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Gwamman ya yi gargadin cewa muddun idan ba a dauki kwakkwaran mataki ba an dakile abin da Boko Haram suke yi ba a yankin Tibuktu na Tafkin Chadi da tsaunin Mandara da kuma Sambisa wato Goza, to mayakan Boko haram za su kara karfi sosai.

''Suna nan a kan duwatsu suna saukowa su kai hari wadannan yankuna, to idan ba a dauki mataki a kan waddan wurare uku ba, kamar yanda Chadi suka yi lokacin Idriss Déby, a sanadiyyar wannan ne ma ya rasa ransa,'' in ji Sanatan.

Danmajalisar ya ce yana ganin daya daga cikin abin da ya janyo wannan matsalar a yanzu shi ne, kasashen Chadi da Nijar da Kamaru sun dage a kan korar Boko Haram a yankunansu - hakan ya sa yake ganin su kuma Boko Haram suka karkato yankunan Najeriya - musamman jihohin Borno da Yobe da ma jihar Adamawa.

Ya ce yanzu abin ya yi kamari sosai suna so su hana manoma noma a bana su ma kori mutane a wasu garuruwan gaba daya kamar yanda ya ce sun yi a Sabongari da Wajir ko a Dambuwa.

''Abin da nake fada kullum shi ne wannan abin muna ganin za a iya maganinsa idan an tashi da gaske.'' In ji Ndumen.