'Ciwon zuciya da hawan jini': Sabbin buƙatun iyayen 'yanmatan Chibok

Abu kamar wasa, Talata 15 ga watan Afrilun nan ne 'yanmatan sakandare ta Chibok ke cika shekara 11 a hannun mayaƙan ƙungiyar Boko Haram mai iƙirarin jihadi.
A irin wannan rana ne a shekarar 2014 'yanbindigar ɗauke da makamai suka afka makarantar da ke da nisan kilomita kusan 125 daga birnin Maiduguri na jihar Borno, inda suka sace yaran 276 da tsakar dare.
Satar ɗaliban ce irinta ta farko da aka taɓa gani a Najeriya, kuma tun daga lokacin 'yanbindiga suka mayar da abin sana'a.
Ƙungiyoyin fafutika, da 'yansiyasa, da fitattun mutane sun yi kiraye-kirayen ceto 'yanmatan bisa maudu'in BringBackOurGirls, wadda ta zama ƙungiya kuma take ci gaba da gwagwarmayar nema wa ɗaliban 'yanci.
Har yanzu sama da 80 na hannun waɗanda suka sace su bayan gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ta cim ma yarjejeniyar sakin 82 daga cikinsu, da kuma waɗanda suka dinga sulalewa da ɗaya-ɗaya.
Ana ƙiyasta cewa kusan 180 ne suka kuɓuta daga hannun masu garkuwar tun daga lokacin.
"Cikin baƙin ciki, har yanzu babu wani cigaba da aka samu a yunƙurin ceto su," a cewar ƙungiyar fafutika ta BringBackOurGirls cikin wata sanarwa a ranar Talata. "Iyayensu na ci gaba da fata cikin ƙunar zuci."
Wasu daga cikin 'yanmatan da BBC ta tattauna da su a Afrilun 2024 sun bayyana damuwa game da rashin ba su kulawa a wuraren da gwamnati ta tsugunar da su.
"Na yi da-na-sanin gudowa daga dajin Sambisa zuwa Najeriya," a cewar ɗaya daga cikinsu wadda muka sakaya sunanta.
"Wani lokacin sai na yi kuka idan na tuna. Sai na tambayi kai na: 'Me ya sa na bar Sambisa na dawo Najeriya don na tarar da wulaƙanci da zagi a kullum?' Ban taɓa fuskantar irin wannan yanayin ba lokacin da nake Sambisa."
'Ciwon zuciya da hawan jini'

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tun bayan sace 'yanmatan na Chibok, iyayen yaran kusan 30 ne suka mutu, kamar yadda Allen Manasseh, wani mai magana da yawun al'ummar garin Chibok, ya shaida wa BBC Hausa.
"Kuma yawancin cutukan da suka kashe su ciwon zuciya ne, da hawan jini, da sauransu saboda tsabar damuwa ta jiran ganin yaran nasu," in ji shi.
A ranar Litinin ne iyayen ɗaliban suka taru a harabar makarantar ta Chibok, inda suka yi addu'o'i na addinai daban-daban tare da jaddada kira ga gwamnati ta ceto sauran 'ya'yan nasu.
Allen ya ce bayanan da suka samu na cewa gwamnati na da rahoton tabbacin waɗanda suka mutu daga cikin 'yanmatan bayan sace su, amma har yanzu ba a bayyana musu hakan ba a hukumance.
Ya ƙara da cewa iyayen da 'ya'yansu ba su dawo ba na kokawa kan yadda gwamnatin Najeriya ta daina ba su kulawa.
"Suna cewa gwamnati ta yashe su, ba ta ce musu komai sai shekara ta zagayo sai a tura musu 'yan ƙungiyoyi da 'yanjarida, in an gama kuma ba za su sake jin komai ba sai shekara ta zagayo."
'Abin da muke nema'
Ƙungiyar BringBackOurGirls na ci gaba da gwagwarmayar neman sako ɗaliban, inda take ci gaba da shirya taruka da kuma faɗakarwa da zimmar kada a manta da halin da suke ciki.
Albarkacin zagayowar ranar sace su, ƙungiyar ta zayyana wasu buƙatu huɗu da ta ce suna buƙatar gwamnatin Najeriya ta yi:
- Ya kamata gwamnati ta tuntuɓi iyayen yaran 82 domin bayyana musu halin da ake ciki da kuma ƙoƙarin da ake yi na ceto 'ya'yan nasu. Sannan a nemi hanyar kwantar musu da hankali domin kawo ƙarshen jan ƙafar da gwamnati ke yi.
- A fitar da sakamakon binciken da kwamatin Birgediya Janar Ibrahim Sabo ya yi game da abin da ya faru kuma a bayyana rawar da kowace gwamnatin Najeriya ta taka game da sace su.
- A kafa kwamatin da zai dinga yi wa 'yan ƙasa bayani kai-tsaye duk wata game da yaƙin da ta'addanci da sauran matsalolin tsaro daga ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro.
- A wallafa tare da gabatar da cikakken rahoto na kuɗaɗen da ake kashewa game da tsaron ƙasa tun daga 2014 zuwa yanzu, da kuma nasarorin da aka samu daga hakan.











