'Wasu manyan kwamandojin barayin daji sun mika wuya a jihar Katsina'

Hoton mutane da wasu makamai

Asalin hoton, OTHERS

Lokacin karatu: Minti 2

Wata kungiya a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce wasu kwamandojin 'yanbindiga da dama sun mika wuya sakamkon shiga tsakanin da ta yi a sulhun da aka yi da su.

Kungiyar ta ce 'yanbindigan da kansu ne suka nemi sulhu tare da amincewa su dakatar da kai hare-hare kodayake wasunsu ba su ajiye makamansu suna rike da su a matsayin kariya.

Shugaban kungiyar kwamared Hamisu Sai'idu Batsari shi ne ya tabbatar wa da BBC wadannan bayanai a tattaunawa da shi.

Ya ce daga cikin jiga-jigan ko kacallolin da suka mika wuya akwai, irin su Abu Radda da Maikada da Umar Blak da Tukur Dannajeriya tare da yaransu.

''Kowannensu musamman shi Abu Radda za ka iya samunshi da yaran da suka kai 500 a karkashinsu,'' ya ce.

Ya kara da cewa, ''su kuwa su Tukur Mairakumi da su Maikada su Tukur Dannajeriya su kuma za ka iya samunsu da yaran da suka kai dari bibbiyu ko dari uku kowannensu.

Kwamared Hamisu ya ce, a zaman sasancin da suka yi da wadannan barayin daji, wasu daga cikinsu suna rike da makamai ne kawai da sunan suna son samun tabbacin za a ba su kariya su da dabbobinsu daga wasu daga cikin barayin da su ba su yarda da sulhunba, idan suka mika wuya.

Shugaban ya ce suna da kwarin gwiwa na samun zaman lafiya daga wannan sulhu domin a cewarsa, 'yanbindigan ne a wannan karon da kansu suka nemi sulhun sabanin na baya da ake nemansu a yi musu wasu alkawura da kuma ba a cikawa, wanda hakan ke sawa su koma ruwa a can baya.

Daga cikin sharuddan da ya ce sun cimma da barayin dajin akwai cewa, dakatar da ayyukan ta'addanci da suke yi sannan su saki dukkain wadanda suka kama ba kuma lalle sai na wannan yanki ba.

Sa'idu Batsari ya kuma ce su a bangarensu 'yanbindigan sun nemi gwamnati ta tabbatar da adalci a tsakaninsu tsakanin su mazauna daji da sauran al'umma ta fuskar sama musu abubuwan more rayuwa, kamar ruwan sha da makarantu da sauransu.

''Sannan sai kuma sai bangaren jami'an tsaro 'yanbindigan sun nemi da a daina kamasu haka kawai ana kashe su, ba tare da wani laifi ba, in kuma sun yi laifi a kama su a gurfanar da su gaban shari'a a yi musu hukunci kamar yadda doka ta tanadar,'' in ji shi.