Da a kashe mutum ɗaya a Kaduna, gara na yi sulhu da ƴanfashi - Uba Sani

Asalin hoton, facebook/Uba Sani
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya bayyana wa BBC dalilan da suka sanya gwamnatinsa ta amince ta yi sulhu da ƴanfashin daji a jihar yayin da jihohin da ke maƙwaftaka suka yi watsi da irin wannan tsari.
A cikin watan da ya gabata ne bayanai suka ɓulla kan sasancin da gwamnatin jihar ta yi da ƴanfashin waɗanda suka daɗe suna addabar yankunan jihar.
Lamarin da al'ummar yankunan da rashin tsaro ya fi shafa, kamar Birnin Gwari da Giwa da ƙauyukan ƙaramar hukumar Igabi suka ce ya kawo musu kwanciyar hankali.
Kaduna ta fuskanci munanan ayyukan ƴan bindiga a shekarun baya, kamar satar ɗaliban makarantar firamare a Kuriga, da satar fasinjojin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna da kuma harin da ƴanfashin suka kai wa sojojin kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.
A tattaunawarsa da BBC, gwamnan na jihar Kaduna ya yi bayani kan dalili da kuma matakan da aka bi wajen yin sasanci da ƴanfashin.
Hakan na faruwa ne yayin da jihohin da ke zagaye da Kaduna, kamar Zamfara da Katsina ke bayyana cewa ba za su taɓa zama kan teburin sulhu da ƴan bindiga ba.
'Al'umma ne suka buƙaci a yi sulhu'
Uba Sani ya bayyana wa BBC cewa tun farko al'ummar yankunan da suka fi fama da matsalar tsaron ne suka buƙaci a yi zaman sasanci da ƴan bindiga, inda gwamnati ta duba sannan ta yanke shawarar amincewa da hakan.
"Alal misali, Sarkin Birnin Gwari ya zo da al'ummarsa ya ce yana so a zauna a tattauna a yi sulhu," in ji Sani.
"Na tambaye shi 'me ya sa'? Ya ce min 'shekara sama da 10 ana ta yaƙi ana kashe mana mutane, ana ɗauke mana mutane amma ba a samu ƙarewar wannan fitina ba'".

Asalin hoton, X/Uba Sani
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Uba Sani ya ce bayan haka ne ya tattauna da ofishin mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkar tsaro, Nuhu Ribadu da sauran shugabannin tsaro kafin aka yanke hukuncin amincewa da yin sasanci.
Ya kuma bayyana cewa sai da ƴan fashin dajin suka sako mutane 200 da suke garkuwa da su a ƙananan hukumomin Giwa da Birnin Gwari kafin gwamnati ta amince da batun zaman yin sulhu.
Gwamnan ya ce yana sa ran sulhun zai haifar da zaman lafiya ta yadda manoma da ƴan kasuwa za su ci gaba da harkokinsu domin farfaɗo da tattalin arziƙi.
Matsalar ƴan fashin dajin wadda ta addabi jihoin arewa maso yammacin Najeriya ta tursasa wa manoma barin ƙauyuka, lamarin da ya sanya albarkatun noma da ake samu ya yi ƙasa, wanda masana suka bayyana cewa ya taimaka wajen haifar da tashin farashin kayan masarufi.
Uba Sani ya ce "da a kashe min mutum ɗaya a Kaduna, gara in yi sulhu...in ba haka ba ranar gobe ƙiyama ni Allah zai tambaya domin ni ne na ɗauki alƙawari, na rantse."
Ko an biya kuɗi wurin yin sulhu?
Gwamnan na jihar Kaduna ya bayyana wa BBC cewar gwamnatinsa ba ta biya kuɗi domin yin sasanci da ƴan bindigar ba.
"Ina son in tabbatar maka cewar ko naira ɗaya ba a ba su ba," in ji Uba Sani.
Gwamnan ya shaida wa BBC cewa an yi sulhun ne tare da haɗin kan sarakuna da malaman addini, kuma an kwashe wata shida ana tattaunawa ba tare da an sanar wa al'umma ba.
Sulhun zai ɗore?
Wani abu da ke sanya al'umma a yankunan da ke fama da rashin tsaro na Najeriya yin ɗari-ɗari da batun yin sulhu da ƴan fashin daji shi ne batun ɗorewar al'amarin.
A shekarun da suka gabata an gwada yin sulhu a wasu yankunan ƙasar da ƴan fashin dajin, sai dai lamarin bai ɗore ba.
Baya ga ƙauyukan da suka sha kwatanta irin yin hakan, wani babban misali shi ne sulhun da gwamnatin jihar Zamfara ta taɓa yi da ƴan fashin daji, lamarin da ya rushe daga baya.
Sai dai Uba Sani ya ce matakin da ƴan fashin suka ɗauka tun daga farko na sakin mutanen da suke garkuwa da su a yankunan jihar Kaduna, gabanin yin sulhun, wata manuniya ce kan cewa da alama sulhun zai iya ɗorewa.
"Sun sako mana mutane, kuma bayan haka al'ummarmu na nan suna ta kasuwanci da noma, shi ya sa nake tabbatar wa al'umma cewa za mu ci gaba da addua'a kuma sauƙin da aka samu zai tabbata."
Mutane da dama a baya sun soki batun yin sulhu da ƴan fashin daji bayan abubuwan da suka faru a baya na karya irin wannan alƙawari daga ɓangaren ƴan fashin.
Daga cikin waɗanda suka soki batun yin sulhu da ƴan bindiga a baya har da tsohon gwamnan jihar ta Kaduna, Nasir El-Rufa'i.
A wata tattaunawa da BBC, El-Rufa'i ya ce "Ni a ganina waɗannan ƴan tadda a daji suke, kuma babu wani mai gaskiya a dajin, kashe mutane suke yi suna ɗaukar dukiyar al'umma, yadda aka tayar wa Boko Haram haka ya kamata a yi musu, in da za a sa sojojin sama a cikin sati ɗaya ko biyu su bi dazuka su yi jefa musu bam, to wallahi za a yi maganin matsalar nan."
Haka nan tsohon ministan yaɗa labarun Najeriya, Lai Mohammed a wata hira da tashar talabijin ta Najeriya ya taɓa bayyana cewa gwamnoni sun gane kuskurensu bayan yin sulhu da ƴan fashi.
"Gwamnonin sun koyi darasi daga kura-kuran da suka faru a baya kuma sun yanke shawarar cewa ba za su tattauna da ƴan fashi ba sai dai su fatattake su," in ji ministan.
Matsalar rashin tsaro sanadiyyar ƴan fashin daji a arewa maso yammacin Najeriya ta haifar da asarar ɗimbin rayuka da kuma tagayyara al'umma da dama.
Lamarin ya fi addabar jihohin Kaduna, da Katsina da Zamfara da Sokoto da kuma Neja.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa tana bakin ƙoƙarinta wajen shawo kan matsalar.
Sai duk da nasarorin da ta samu a baya-bayan nan, ƴan fashin na ci gaba da tsananta wa al'umma ta kisa da kuma garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.











