'Masifar da muka shiga a watannin da muka yi a daji a hannun ƴan bindiga'

Asalin hoton, Hassan Usman
- Marubuci, Halima Umar Saleh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Digital Journalist
- Aiko rahoto daga, BBC News Hausa, Abuja
Sake buɗe layin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna da ke arewacin Najeriya bayan wata tara da dakatar da shi sakamakon harin da aka kai masa, na tuna wa wasu fasinjojin da aka sace a lokacin, irin mummunan yanayin da suka tsinci kansu a ciki.
A ranar 28 ga watan Maris ‘yan bindiga suka kai wa jirgin mummunan hari inda suka lalata layin dogon ta hanyar dasa nakiya a kai, yanayin da ya tilasta wa jirgin mai dauke da fasinjoji 362 tsayawa a daji cikin dare.
Tsayarwa jirgin ke da wuya aka bude wa fasinjojin wuta, harbi ta kowace kusurwa, bayan 'yan bindiga sun yi wa jirgin ƙawanya, duk da yawan jami’an tsaro da ke yi wa jirgin rakiya.
‘Yan bindiga sun yi nasarar garkuwa da fasinjoji 62, sannan a kalla mutum tara ne suka mutu a kazamin harin.
Cikin wadanda aka yi garkuwa da su a wannan dare akwai Hassan Usman, wani lauya mazaunin Kaduna da matarsa.
Ya shaida wa BBC cewa mutanen da aka kwashe daga jirgin a wannan hari sun haɗa da maza 39 da mata 18 da kuma yara biyar – waɗanda aka tilasta wa yin doguwar tafiya ta kwanaki hudu a cikin dajin da aka ajiye su.
Tafiyar ta kasance mai wahalar gaske saboda akwai tsananin zafin rana, gashi ba bu abinci sai ɗan ruwa da ake ba su lokaci zuwa lokaci.

Asalin hoton, @CHIBUIKEAMAECHI
Mutumin mai shekara 47 ya kasance wanda ke magana a madadin sauran mutanen da ƴan bindigar ke riƙe da su, cikin mutanen akwai wadanda suka shafe wata biyar a daji.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tun bayan fitowarsu suka buɗe zauren sada zumunci a WhatsApp, domin tattaunawa da kuma taimakon juna.
Ganinsa a yanzu tsaf-tsaf da shi, da wuya ka iya gane cewa shi ne mutumin da aka nuna a wani bidiyo lokacin suna cikin dajin, cikin yanayi na galabaituwa sanye da kaya launin siminti, yana roƙon gwamnati ta ceto su daga hannun ‘yan bindigar.
A wannan bidiyon wanda ƴan bindigar suka saki a watan Yulin, kana iya hango yadda ake zane sauran mutanen da ke tsare inda suke tsala sowa.
Ya ce yanayi ne na uƙuba da kaɗuwa da ba za su taɓa mantawa ba, musamman ma ga mata kula da tsaftace jikinsu kawai ya zame musu wani babban tashin hankali.
A duk lokutan da haila ta zo musu ba su da auduga sai dai su yi amfani da tsummokara.
Suna samun ruwan sha daga wani ɗan ƙaramin rafi a kusa da inda aka ajiye su, kuma a wannan rafin dai suke wanka.
"A watannin farko, a sararin Allah muke kwanciya a ƙasa, wani lokaci ma wajen a jiƙe, amma kuma da aka soma damuna sai suka haɗa manyan tantuna da muke ɗan raɓewa zuwa lokacin da ruwan zai tsaya," a cewar Barista Usman.
Sau ɗaya suke samun abinci a rana da misalin ƙarfe 11:00 na safe – yawanci dama tuwon masara ne da miyar kuka "tafa shi kaɗa, kamar an wanke kai da ita," kamar yadda ya ce.
"Daga baya mun fahimci cewa abincin da muke ci ta ɓoyayyiyar hanya ake samo shi, don haka samun abinci akai-akai matsala ce. Lokaci zuwa lokaci su kan ba mu shinkafa fara da man ja wani lokaci kuma da wake,” a cewarsa.
Amma Barista Usman ya ce a kalla an yanka musu shanu 12 ana babbake musu su ci a tsawon zaman da suka yi.
"Ko ranar Babbar Sallah ma an kwantar da shanu an yanka a matsayin tamu hidimar sallar," ya ce.
Usman ya ci gaba da cewa: "Akwai kwanakin da suke ba mu abinci sau biyu kamar da misalin 06:00 na yamma, amma ba kasafai ba.
"Matan ke mana girki sannan mazan kuma ke aikace-aikace kamar ɗebo ruwa, saro itacen girki da kuma wanke-wanke.”
'An yi ƙoƙarin cusa mana aƙidar Boko Haram'
Tsawon makonni ba a iya gano ainihin mutane da ƙungiyar da ta yi garkuwa da fasinjojin jirgin ba- sai dai an yi ta yaɗa jita-jita cewa ƴan fashin daji ne masu garkuwa da mutane domin kuɗin fansa da suka yi ƙaurin suna a yankunan arewa maso yammacin Najeriya.
Sai dai Usman ya tabbatar da zargin da ake yi cewa ‘yan bindigar mambobin kungiyar Boko Haram ne da ke gudanar da ayyukansu a arewa maso gabashin Najeriya tun a shekarar 2009.

Asalin hoton, DAILY TRUST
An daɗe ana tunanin cewa ƙungiyar Boko Haram wacce ke son kifar da gwamnati tare da assasa daular Musulunci, na faɗaɗa ayyukanta zuwa kudancin ƙasar.
“Sun shaida mana cewa su ƴan Boko Haram ne kuma sun kama mu ne don tura buƙatunsu ga gwamnati.
“A wasu lokutan sukan ba mu wayoyinsu don saurarar wa’azuzzukansu,” in ji shi, yana mai bayyana cewa cikin wa’azuzzukan har da na shugabannin Boko Haram na farko wato Mohammed Yusuf da Abubakar Shekau – waɗanda a yanzu sun mutu.
“Sun ma yi ƙoƙarin jan hankalinmu don shiga ƙungiyar tare da bayyana mana muradunsu.
“A duk lokacin da wani ba shi da lafiya a cikinmu to suna da likitocin da ke duba mu, waɗanda ni dai a ganina ba ƙwararru ba ne.
“Wasu lokutan kuma sukan nemi taimakon ma’aikatan lafiya a cikinsu don duba marasa lafiyan, kuma duk maganin da aka buƙata suna kawowa,” ya ce.
Lauyan ya shaida min cewa sau da dama har masu rashin lafiya irin su hawan jini da ciwon sikari ana kai musu irin magungunan da suke sha.
“Su kuwa likitocin je-ke-na-yi-kan nasu har allura da ƙarin ruwa suna yi wa marasa lafiyan cikinmu musamman masu fama da zazzazɓin taifod da maleriya.”
Akwai lokacin da sai da kusan gaba ɗaya fasinjojin suka kwanta rashin lafiya don tsananin halin da suke ciki, amma cikin ikon Allah duk sun ɗan sa mu sauƙi.
A cikin yaran da aka kama, Barista Usman ya yi matuƙar sabo da wata Fatima ƴar shekara 10, ta yadda ko tana cikin damuwa shi ke iya rarrashin ta har ma su ci abinci tare.
Fatima na tsare a lokacin da ta cika shekara 10 a duniya har ma Barista Usman ya yi ƙoƙarin ba ta wani abu komai ƙanƙantarsa don sanya ta farin ciki a ranar.
Akwai lokacin da shugaban ƴan bindigar ya buƙaci zai kai yaran gidansa don su fi samun kyakkyawar kulawa da sharaɗin idan iyayen sun yarda, amma ba wanda ya amince da wannan shawara a cikinsu.
'Ba mu kuɗi'
Barista Usman ya ce daga baya ƴan bindigar sun dinga ba su kyautar ƴan kuɗade tare da ce musu idan har suna da abin da suke so a sayo musu to su rubuta.
"Kowa ya rubuta abin da yake so a sayo masa, inda a lokacin ne mata suka samu zarafin buƙatar a sayo musu audugar mata don tsaftace yanayin al'adarsu," ya ce.
Sannan a lokuta da dama idan mata da yara suka shiga cikin matsanancin yanayin damuwa, to mazan ne ke ƙoƙarin rarrashinsu.
"Sau da dama cikin dare matata kan ruɗe ta rikice har sai na je na dinga lallashinta sannan a samu sauƙi," ya ce.
'Biyan kuɗin fansa ya jawo wa wasu talaucewa'
An saki da yawan fasinjojin ne bayan biyan makuɗan kuɗaɗen fansa da iyalansu suka yi, yayin da ƴan bindiga suka ci gaba da riƙe sauran don neman wasu buƙatun a hannun gwamnati.
Wasu masu sharhin na ganin cikin buƙatun har da sake musu fursunoninsu da ake tsare da su - duk da dai babu tabbas a kan hakan.

Asalin hoton, Reuters
Barista Usman ya ce ba shi da masaniyar ko an biya kuɗin fansa don karɓarsa ko ba a biya ba, don ba su taɓa ce masa komai ba kan hakan.
Sai dai a ranar da ƴan uwansa suka kammala sasantawa da ƴan bindigar don karɓarsa sai abubuwa suka rincaɓe.
“Ƴan sanda da ke sintiri a hanyar sun hana ƴan uwan Usman wucewa don su ƙarasa matsayar da za su karɓe ni, dole sai komawa suka yi ni ma aka mai da ni sansani.”
Wannan abu ya tunzura ƴan bindigar inda har suka tara mutanen suka zane su aka kuma nadin wannan bidiyon aka yaɗa, amma washe garin ranar aka dangana Usman da danginsa.
Yawanci iyalan da suka biya kuɗaɗen fansa sun samu kansu a cikin halin ƙa-ƙa-ni-ka-yi da matsin tattalin arziki bayan fitar su – don yawancin kudin fansar da aka biya ya kai naira miliyan 100 ga duk mutum ɗaya.
A cikin zauran Whatsapp din da suka ƙirƙira, inda fasinjojin a yanzu suke mu’amala da juna tamkar ƴan uwa, mutane suna bayyana irin mummunan yanayin da suka shiga na taɓarɓarewar tattalin arziki.
“Yanzu da yawa wasu abinci sau uku a rana ma gagarsu yake yi, wasu kuma an fitar da su daga gidajen haya,” in ji Barista Usman.
Kazalika lauyan ya koka kan yadda ba a bai wa mutanen da aka sace irin taimakon da ya kamata ta fannin saita tunaninsu sakamakon kaɗuwar da suka shiga.
“Muna da Ma’aikatar Jin Ƙai wacce aikinta shi ne ta taimaki irin wadannan mutanen – Ina ga akwai buƙatar tallafinta ta wannan ɓangare a wannan lokaci.”
Ɗaya daga cikin matan da aka sace ɗin cikin kukan tuna wa da halin da ta shiga ta shaida min yanayin da ta shafe watanni a cikinsa a dajin.
Matar wacce ba ta so a bayyana sunanta, ta sha alwashin ba za ta sake bin hanyar Abuja zuwa Kaduna ba - ko a mota ko a jirgin ƙsa - saboda kaɗuwar da ta shiga.
Dubban mutane ne ke bin hanyar zuwa biranen biyu saboda mafi yawan ma'aikatan gwamnati ba sa iya biyan haya a Abuja saboda tsada, don haka sun gwammace ajiye iyalansu a wasu garuruwan.

Asalin hoton, oTHERS
Sun zaɓi barin iyalansu a Kaduna ko sauran jihohi masu maƙwabtaka da ita don sai su dinga zuwa hutun ƙarshen mako.
Mutane da dama na ɗaukar jirgin ƙasan wanda aka buɗe shi a 2016, a matsayin mafita kan bin babar hanyar – wacce ta yi ƙaurin suna wajen sace mutane don kudin fansa.
Cikin waɗanda aka sace a jirgin akwai masu fargabar sake hawa jirgin, amma Barista Usman ya yi maraba da sake buɗe layin dogon mai tsawo kilomita 174 – da aka yi ranar Litinin 5 ga watan Disamban 2022.
Shawararsa gagwamnati ita ce a tabbatar da samar da tsaro da sa ido kan abin da ke faruwa a layin dogon tsawon sa’a 24 na rana.
Hafsan hafsoshinrundunar tsaron Najeriya Janar Lucky Irabor ya tabbatar da cewa an samar da kyamarorin da za su dinga sa ido, ta yadda har shugaban ƙasa ma zai iya ganin “duk abin da yake faruwa a lan layin daga ofishinsa.”












