Sulhu da ƴan bindiga a Birnin Gwari: Ko zaman lafiya zai ɗore?

Asalin hoton, Ishaq Kasai
Har yanzu ana ci gaba da ɗarɗar kan batun dawowar zaman lafiya a yankunan ƙaramar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna, musamman ganin harkokin kasuwanci da noma sun fara komawa daidai a yankin.
Birnin Gwari ɗaya ne daga cikin yankunan da suka yi ƙaurin suna kan rashin tsaro a Najeriya, sanadiyyar ayyukan ƴan bindiga masu satar mutane domin neman kuɗin fansa.
Sannan hanyar da ta tashi daga Kaduna zuwa yankin, wadda ta ratsa ta ƙaramar hukumar Chikun na daga cikin mafiya hatsari a faɗin ƙasar.
A ƙauyen Kuriga da ke kan hanyar ne wasu ƴan bindiga suka yi garkuwa da yara ƴan makarantar firamare a farkon shekarar 2024.
Haka nan satar mutane ta zama tamkar ruwan dare a yankin da zagayensa.
Amma tun a ƙarshen watan Nuwamban bara, zaman lafiya ya fara dawowa a yankin, lamarin da ya sanya gwamnatin jihar Kaduna ta buɗe kasuwar shanun yankin da ta kusa yin shekara takwas a rufe.
Bayan wahalar bin hanyar, matsalar rashin tsaro ta kuma jefa harkokin kasuwanci da ilimi da noma cikin matsala.
An rufe makaranta, sannan mutane sun daina zuwa gona, sannan kasuwanci ya samu koma baya, musamman rufe manyan kasuwanni.
Muna cikin farin ciki - Mutanen yankin

Asalin hoton, Ishaq Kasai
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Umaru Dakare, direban mota ne da ke jigilar fasinja a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari tun daga zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce yanzu suna tuƙi cikin kwanciyar hankali.
Ya ce, "Yanzu mun gode wa Allah, hanyar Birnin Gwari an samu sauƙi bakin gwargwado saboda ni kullum sai na je garin. A da can sojoji ne suke mana rakiya kuma ko da rakiyar, ƴanbindiga sukan fito su buɗe wuta su ɗauki na ɗauka, amma yanzu idan muka yi lodi da safe muna tsayawa ne a garin Buruku, daga nan akwai sojoji da suke fitowa sai su tsaya a wuri-wuri, amma ba a mana rakiya."
Ya ce rabon da su samu labarin tare hanyar yanzu kusan mako uku zuwa huɗu ke nan, inda ya ce suna godiya ga Allah sannan suna godiya ga gwamnatin tarayya da ta jiha bisa wannan ƙoƙari.
"Sai dai muna kira ga gwamnatin da ta ƙara ƙaimi, muna roƙo a ƙara mana kula a wannan hanya. Muna so mu cigaba da tafiya cikin kwanciyar hankali.
Shi ma wani mai suna Bashir Kakangi, ya ce sun fara cin moriyar zaman lafiya da aka fara samu, "Alhamdulillahi a yanzu halin da ake ciki muna cikin kwanciyar hankali, bakin gwargwado. A da ko babbar mota ce za ta wuce da gudu a cikin garin, amma yanzu, musamman ranar Alhamis da ake cin kasuwa, ko da ƙafa kake tafiya sai ka bi a hankali saboda cunkoson mutane."
A nasa jawabin, Suleiman Mori ya ce bana zai noma gonarsa, domin a bara a bakin gida kawai ya yi noma, "Yanzu mun fara ji a jikinmu ma saboda hayyacinmu ya fara dawowa. Akwai maƙwabtanmu da saduwa ta yi wahala, amma yanzu kowane lokaci za ka iya saduwa da su ta hanyar ziyarce-ziyarce. Na je gonata wadda ban noma ba a bara saboda rashin tsaro."
Ishaq Usman Kasai, wanda shi ne shugaban ƙungiyar ciyar da yankin na Birnin Gwari da al'ummomin da ke iyaka, (Birnin Gwari/Niger Inter-Boarder Communities Union for Peace and Development) ya ce harkoki sun fara komawa da kyau a yankin, sai dai sai godiyar Allah a yanzu.
"Alhamdulilla, kamar yadda aka sani, wannan matsalar ta tsaro dama mutanen yankin Birnin Gwari kullum da ita suke kwana suke tashi. An yi shekaru ana fuskantar wannan matsala, wadda ta shafi harkokin noma da kasuwanni da tafiye-tafiye da ɓangaren ilimi, kuma an ɗauki kusan shekara takwas zuwa 10 ana haka.
"Amma bayan wannan sasanci da aka yi, a cikin ƴan kwanakin nan kasuwar Birnin Gwari wadda ta yi shekara 8 a rufe yanzu an buɗe ta, kuma ana cin kasuwar cikin walwala.
"Hanyar zuwa Kaduna zuwa Birnin Gwari da Birnin Gwari zuwa Neja da ta zuwa Funtuwa yanzu duk za ka iya tafiwa a kowane lokaci ba dare ba rana. A da ko an yi noma, ba a iya zuwa a girbe, wanda hakan ya shafi kasuwanci, amma yanzu ko cikin dare za ka iya zuwa gona. Kuma su ma Fulanin suna kawo kayayyakinsu kasuwa."

Asalin hoton, Ishaq Kasai
Akwai sauran rina a kaba- Masani
Kabiru Adamu, shugaban kamfanin tsaro na Beacon Cunsulting ya ce duk da cewa an samu sauƙin matsalar, lallai akwai sauran rina a kaba.
A cewarsa, "sakamakon yarjejeniya ce wadda gwamatin jiha da taimakon ta tarayya ta yi da ƴanbindigar da ke yankin. Sai dai abin tambaya ko jira shi ne, shin wannan zai zama na dindindin ne ko na wucin-gadi saboda abubuwan da suke faruwa a yankin. Amma babu shakka yanzu an samu zaman lafiya."
Sai dai zayyana wasu matsaloli da ya ce su za a magance idan ana so a samu zaman lafiya na dindidin:
- Rashin zamantakewa mai kyau
- Talauci
- Yawaitar makamai
- Ɗumamar yanayi
- Yaɗa labaran ƙarya
A game da fargabar da ake yi cewa an daɗe ana sulhu, kuma ana komawa gidan jiya, masanin ya ce idan ba a magance matsalolin da ya ambata ba, za a iya komawa gidan jiya.
A game da batun ɓangaren mutanen gari, waɗanda lamarin ya shafa, ya ce, "shi ya na kawo batun zamantakewa. Amma a baya gwamnati ta yi ƙoƙarin fito da hanyoyin taimaka wa waɗanda irin matsalar ta shafa irin su hukumar 'victim support fund', sai dai babu alƙaluma na zahiri da ke nuna an taimaka musu."
A ƙarshe ya yi kira ga gwamnati da sauran al'umma cewa kada a sake jiki, "a cigaba da bin hanyoyi na samun zaman lafiya. Kuma wannan haƙƙi ne da ya rataya kan gwamnati, amma ta nemi goyon bayan jama'an gari. Kowa ya sa a ransa cewa zaman lafiya yake so," in ji shi.
'Ya kamata a yi irin haka a jihohi masu maƙwaftaka'

Asalin hoton, FB/Isa Muhammad Galadima
Shugaban ƙungiyar cigaban al'ummar Birnin Gwari (BEPU), Isah Muhammad Galadima ya ce al'umma sun yi maraba da zaman lafiyar da aka samu ta hanyar sulhu.
Ya ce "a yanzu al'umma na iya yin bacci kuma suna iya sada zumunci".
"Babban abin da muke fata shi ne gwamnati ta tabbatar an bi duk hanyoyin da suka dace domin tabbatar ɗorewar hakan."
Sai dai ya nuna damuwa kan abubuwan da ke faruwa a wasu jihohin da ke maƙwaftaka da yankin na Birnin Gwari.
Ya ce "Ƙin yin sulhu a jihohin maƙwafta bazarazane ce ga zaman lafiyar yankin Kaduna."
Ya kamata gwamnonin Zamfara da Sokoto da Katsina da Neja su yi tunanin yin irin wannan sulhu.











