Mun zama bayin ƴan bindiga - Al'ummar Birnin Gwari

Yan bindiga

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun cinnawa gonakin mutane da dama wuta inda suka ƙona dukkan amfanin gona, a ƙaramar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna a yankin Arewa maso yammacin Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan da aka yi wani zaman sulhu tsakanin ƴan bindigar da al’ummar yankin na Birnin Gwari da zummar kawo ƙarshen ɓarnar da suke yi.

Maharan sun cinnawa gonakin masara da wake wuta ne a tsakar dare, inda suka ƙona gonaki da dama, abinda kuma ya haifar da hasara mai ɗimbin yawa.

Wasu daga cikin manoman da suka tafka asarar cikin sun shaida wa BBC irin yadda suka ji, tare da bayyana cewa suna ganin sun zama bayi ta la’akari da matsayin da suka tsinci kansu, kamar yadda ɗaya daga cikin su ya shaida wa BBC.

Ya ce: ‘‘Gonaki kusan guda 11 aka cinna masu wuta. Gonakin Marasa ne da na waken soya, wanda aƙalla ana sa ran za a iya fitar da buhu dubu.

‘‘Duk sun amshe mana dukiyoyin mu suna yin abin da suka ga dama, bautar da mu suke yi. Abin da suke so kawai suke yi don gwamnati ne.

‘‘Abin da suke so shi suke yi domin wata gwamnati ce ta musa, nan.’’

Haka nan kuma, a ɓangaren mahukunta, Hon Bashir Zubairu Usman, Chiroman birnin Gwari dan majalisa wakilai ne na tarayya mai wakiltar Birnin Gwari da Giwa ya tabbatar da aukuwar harin.

Ya ce ‘‘Gaskiya an yi asarar dukiya ta fi ta miliyan ɗari da wani abu, kuma ba wai sun daina bane suna kan yi. Suna maganar cewa an taɓa masu mutanen su, don haka sai an dawo masu da bindigogin su da aka ƙwace.

‘‘Ba za a je a zauna da mutane ba, a ɗauki maƙudan kuɗi a basu, bayan na jama’a da suka ƙwace, bayan kashe mutane da ƙona dukiyar su. Ya za a ce an ƙona dukiyar jama’a sannan kuma a yi maganar sulhu.

Hon Bashir Zubairu Usman ya gargaɗi hukumomi da sauran masu jagorantar tattaunawar sulhun su sani cewa duk wata maganar sulhu ba za ta yiwu ba sai an biya jama’a irin ɓarnar da aka yi masu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ciroman na Birnin Gwari, ya ce ba mafita ba ce ɗaukar makamai, amma idan hakan ya zama dole to jama’a fa za su kare kansu da kansu.

‘‘Za mu kai ga faɗin sunayen ainihin mutanen da ke wannan ƙulle-ƙulen sulhun nan. Wancan karon an yi, an ɗauko waɗannan ɓarayin an kawo su fadar mai martaba sarkin Birnin Gwari kuma an ɗauki maƙudan kuɗi an basu. Su mutanen da aka kama iyalan su, aka ƙona dukiyar su, su nawa aka basu?’’

A ɓangaren rundunar ƴan sandan jihar Kaduna kuwa, kakakin ta, ASP Mansur Hassan ya ce sun samu labarin abin da ya farun kuma suna gudanar da bincike domin sanin abin da ya kamata rundunar ƴan sandan ta yi a kai.

Yankin na Birnin Gwari dai ya zama tamkar wani babban ɗan yatsa ne a harkar noma, wanda galibi aka yi ittifaki cewa yana sahun gaba wajen samar da amfanin gona, ba wai ga jama'ar Najeriya kadai ba, har ma da kasashen ƙetare.

To sai dai ga shi yanzu ƴan bindigar na ci gaba da ƙona gonakin noma domin haifar da cikas ga yankin Arewa da kasa baki daya.