' Muna fama da karuwar hare-haren 'yan bindiga a yankinmu'

'Yan bindiga

Asalin hoton, OTHER

Jama'ar garuruwa a kalla takwas na yankin Dan-Kurmi a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara a Najeriya, na ci gaba da fama da matsalar yawan hare-haren 'yan bindiga.

Hari na baya-bayan nan da aka kai an halaka mutum 46, baya ga kona garuruwa da dukiyoyi.

Jama'ar yankin dai na cikin tsaka mai wuya, sakamakon yadda matsalar hare-haren 'yan bindigar ta tsananta a dan tsakanin nan.

Hon Iliyasu Salisu Daraga, shi ne kansilan wannan yanki, ya kuma shaida wa BBC cewa, daga lokacin karamar sallah kawo yanzu an kai musu hare hare 17.

Ya ce, “ A harin farko an kashe musu mutum 51, na biyu an kashe mana mutum 17, akwai kuma harin da aka kai mana Hayin Getso da Farin Ruwa aka kashe mana mutum 54, sannan akwai hare haren baya bayan nan da aka kai mana wasu kauyuka sai da aka kashe mana mutane 46.”

Kansilan y ace bayan kasha mutanen da ‚yan bindigar ke yi sun kuma kona gidaje da dukiyoyi har ma da kayan abinci.

Ya ce, “ Mu yanzu babu abin da muke so illa gwamnati ta taimaka mana ta dube mu mu al’ummar dan Kurmi, saboda talakawanmu na son yin noma amma bam ai iya zuwa gona.”

Su kuwa jama'ar yankin Shinkafi cewa suke, sun fara samun saukin matsalar tsaron, tun da sojoji suka fara kai samame kan 'yan bindigar, amma kuma har yanzu da sauran fargaba.

Wani mutumin yankin mai suna Honarabul Aliyu Moyi, Dan Madamin Shinkafi, ya shaida wa BBC cewa, an dan fara ganin saukin hare-haren 'yan bindigar, tun da aka tura jami'an tsaro, amma kuma har yanzu da sauran fargaba.

Koda BBC ta tuntubi, jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar ta Zamfara, ASP Yazidu Abubakar, ya ce rundunarsu da sauran jami'an tsaro na ci gaba da yin iya bakin kokari, don magance wannan matsala ta tsaro a sassan jihar.