Shin me ya sa hare-haren 'yan fashin daji ke dawowa a Najeriya?

bandits

Asalin hoton, Getty Images

Ana ci gaba da nuna fargaba a Najeriya saboda ƙaruwar hare-haren 'yan fashin daji a sassan arewacin ƙasar, kwanaki ƙalilan bayan kammala zaɓuka.

Wani masanin tsaro a Najeriya ya ce: "Kasancewar ba wai an magance matsalar ba ne, magani na dindindin. To, ka ga, ga shi nan, gaskiya, sun koma tasowa".

A ranar Lahadi ne, gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da kashe gomman mutane da raba ɗumbin wasu da mutsugunansu a ƙauyen Aloko cikin yankin Dekina, bayan wani harin wasu ‘yan bindiga da ba a tantanace ko su wane ne ba.

Gwamnati ta ce maharan waɗanda yawansu ya kai kusan 100 sun kai hari yankin ne, daga sansaninsu da ke maƙwabtaka.

Harin na zuwa ne daidai lokacin da wasu 'yan bindiga suka sace ɗalibai kusan guda 10 a ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna. An kuma samu irin wannan hari da ya yi sanadin sace ɗalibai mata biyu daga Jami'ar Tarayya ta Gusau a jihar Zamfara mai maƙwabtaka.

A tsakiyar watan Maris ma, 'yan fashin daji sun kashe kusan mutum 21 a wani mummunan hari da suka kai cikin ƙaramar hukumar Ƙanƙara ta jihar Katsina.

Wani artabu tsakanin 'yan fashin daji da jami'an ‘yan-sa-kai bayan wata walima da wani riƙaƙƙen ɗan fashi mai laƙabin Mai-katifar-mutuwa ya yi a ƙauyen Majifa.

Bayanai sun ce bayan tashi daga walimar ne a hanyarsu ta komawa inda suka fito, ‘yan bindigar suka riƙa kai farmaki kan ƙauyukan yankin.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Haka zalika, akwai rahotannin kai hare-haren 'yan fashin daji a sassan ƙasar ciki har da a jihohin Taraba da Neja a baya-bayan nan.

Ana iya cewa luguden wuta da jerin farmaki da samamen da dakarun tsaron Najeriya ke kai wa sansanoni daban-daban na gungun 'yan fashin daji, sun yi matuƙar tasiri wajen samun lafawar hare-hare da 'yan bindigar ke kai wa, kafin ga dukkan alamu, su sake dawowa ko kuma a ƙara samun hauhawarsu.

Ƙwararre kan harkar tsaro a yankin Sahel, Dr Kabiru Adamu ya ce da ma matakan da aka ɗauka a kan 'yan fashin dajin, matakai ne na ɗan taƙaitaccen lokaci, don haka babu mamaki, idan hare-harensu suka sake dawowa yanzu.

"Wa'yanda suke kai hare-haren nan, wato ƙungiyoyi wa'yanda suke riƙe da makamai, kusan za mu ce, ba mu magance matsalarsu ba".

Ya ce hare-haren sun ɗan lafa a kwanakin baya, amma batun gaskiya shi ne har yanzu ba a iya magance su ba.

"Matakan da aka ɗauka, matakai ne na ɗan ƙaramin lokaci, wanda kuma ya taimaka, an gudanar da zaɓe," in ji masanin.

Dr Kabiru Adamu ya ce yawanci wuraren da ake kai hare-haren nan, ƙungiyoyi ne na masu riƙe da makamai, da ke da damar amfani da makaman a kan fararen hula.

Alƙawarin tura runduna ta musamman cikin daji

Dr. Kabiru Adamu ya ce ta hanyar tura dakarun tsaro, su ƙara mamaye dazukan da 'yan fashin daji suka yi sansani, da kuma ƙarfafa matakan tsaro a ƙauyuka, ana iya karya lagon gungun 'yan bindigar.

Haka zalika, akwai buƙatar ƙarin haɗin kai ta fuskar tsaro tsakanin gwamnatocin jihohi da na tarayya.

"Yawancin wa'yannan ƙungiyoyi za ka ga a ƙauyuka suke kuma a cikin dazuka. Wa'yannan dazukan kuma suna hannun gwamnatocin jihohi ne."

Ƙarfafa haɗin kan tsakanin gwamnatocin nan, in ji Dr. Kabiru Adamu zai yi matuƙar tasiri wajen hana 'yan fashin daji sakat.

A cewarsa, wani abu mai ƙarfafa gwiwa shi ne gwamnati mai jiran gado da za a rantsar nan gaba a watan Mayu, ta ambaci dazukan da 'yan fashi da suka yi kaka-gida a cikin kundin manufofin da za ta aiwatarwa a lokacin mulkinta.

Ya kuma ce "Ta yi burin cewa za ta kafa runduna ta musamman ta dakarun da za su kasance a irin wa'yannan dazuka. Muna fatan wannan alƙawari da ta yi, za ta samu ta cika".

Me hukumomi suke yi?

A ranar Lahadi, rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe 'yan fashin daji 11, wasu kuma sun arce da raunuka, bayan wata arangama, a yankin Birnin Gwari cikin jihar Kaduna.

Kwamishin tsaro da al'amuran cikin gida na Kaduna, Samuel Aruwan ya ce a lokacin gumurzun, dakarun sojin Najeriya sun fatattaki 'yan fashin dajin a ƙauyen Kakangi da katakaki.

Haka kuma, sojoji sun lalata sansanonin 'yan fashin daji a ƙauyukan Bagoma da Rema da Bugai da Dagara da Sabon layi da Gagumi da Kakangi da katakaki da kuma Randagi.

Haka kuma sojojin sun ƙwato bindigogi guda biyu ƙirar AK-47, da kurtun albarusan guda biyu, sai albarusai 57 da babur shida.

A jihar Zamfara mai maƙwabtaka ma, 'yan sanda sun ce sun kama mutum 17 ranar Lahadin bisa zargin laifuka daban-daban ciki har da tashe-tashen hankula bayan zaɓe, da fashin daji da satar shanu.

Rundunar ta ce a cikin mutanen da ta kama har da wani fitaccen ɗan fashin daji da ya addabi jihar mai suna Sulaiman Balarabe, ɗan shekara 25.

Ta kuma ce ta kama ɗan fashin ne - wanda da ma sunansa ke cikin jerin mutanen da rundunar ke nema ruwa-a-jallo - ranar Laraba 29 ga watan Maris.

Bayan kama wanda ake zargin ne ya tabbatar wa 'yan sanda cewa yana da hannu a hare-hare da sace mutane don neman kuɗin fansa.

Haka zalika a cewar sanarwar 'yan sanda, Sulaiman Balarabe ya ce ya karɓi miliyoyin kuɗaɗe daga hannun makusantan da ya sace wa 'yan'uwansu.