Shin ko sulhun da ake yi da ƴan bindiga a Jibiya da Batsari zai ɗore?

Asalin hoton, OTHERS
Ga dukkan alamu, hukumomi a jihar Katsina sun fara bin matakin yin sulhu da ƴan bindiga a ƙananan hukumomin Batsari da Jibiya.
Matakin na ɗaya daga cikin hanyoyin da masu ruwa da tsaki ke bi wajen kawo ƙarshen zubar da jini da garkuwa da mutane da ƴan bindiga ke yi a yankunan karkara.
Majiyoyi masu ƙarfi sun tabbatar wa BBC, cewa an yi tattaunawar sulhu da ƴan bindiga a ranar Juma'ar da ta gabata a garin Kwari na yankin ƙaramar hukumar Jibiya ta jihar Katsinar.
Haka kuma bayanan da BBC ta tattaro suna nuna cewa, shugaban ƙaramar hukumar yana daga cikin masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sulhun, inda ƴan bindigan suka bayar da tabbacin daina kai hare-hare.
Wasu manyan jami'an gwamnatin jihar da muka tuntuba dai, sun tabbatar da cewar an yi wancan zama na sulhu, amma dai ba su yarda mun naɗi muryoyinsu ba.
Sai dai wani ganau, ba jiyau ba, ya tabbar mana da abin idonsa ya gane masa, tun daga waɗanda suka yi kwamba a wajen taron sulhun:
'' Akwai shi shugaban ƙaramar hukuma, akwai DPO, akwai wakilan sojoji da ma sibil defence, akwai shugabannin kwamiti na ƴan kasuwa da babban limamin sarkin malamai'' in ji shi
A ɓangaren ƙan bindiga kuwa majiyar cewa ta yi:
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
''Akwai Abdullahi Ofisa wanda aka fi sani da Lankai, akwai wanda ya gaji Ibrahim Dangawu, akwai a Loda da Bala Wuta da sauransu''
''Ɓangaren ƴan bindigan dai sun yi bayanin cewa abinda su ke buƙata shi ne a bar matsawa mutanensu a cikin garuruwa idan suka shigo, a bar mutanensu da matansu su zo su ci kasuwa saɓanin yadda ake yi a baya''
Bayyanai sun ce ƴan bindigan sun yi alƙawarin ba za su sake kai hare hare ba
'' Abinda suke so, idan har wani abu aka ji ya faru, ko da ba su bane, ko wani ne ya shigo ya yi, to kada a tada hankali, a gaya mu su, za su ɗauki mataki'', in ji shi.
Shaidu sun ce ƴan bindigan sun kuma yi alƙawarin sakin wasu mutanen da aka kama wadanda suka hada da mata kusan 11.
Sun kuma ce shugaban ƙaramar hukuma ya nemi su akan su cika alƙawarin da suka yi, kada ayi yadda aka yi irin wannan sassanci a can baya, aka yi amana aka zo aka saɓa.
Bayyanai sun ce ƴan bindigan sun bada tabbacin cewa ba za su saɓa alƙawari ba kuma sun miƙa makansu ko da yake ba'a bayyana adadinsu ba.
Rahotanni sun ce wannan ba shi ne karon farko da za a yi sassanci irin wannan ba.
Sun ce a baya an yi zama irin wannan a garin Kofa da ke ƙaramar hukumar Batsari kuma sun yi iƙirarin cewa ya yi tasiri.
Wannan sabon matakin sulhu da aka fara bi a yankunan ƙananan hukumomin Batsari da Jibiya na jihar Katsina, a iya cewa wani zakaran gwajin dafi ne, wanda ake ganin idan ya ɗore, zai iya zama hanyar magance matsalar tsaro da ake fama da ita a wasu sassan jihar, da ma wasu jihohi, musamman na arewa maso yammacin Najeriya.














