'Ƴanbindigar da aka yi sulhu da su a Kaduna na kawo mana hare-hare'

Asalin hoton, OTHER
Jama'ar jihar Neja sun ce ƴanbindigar da aka yi sulhu da su a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna na shiga garuruwansu su na aikata ɓarna sannan su koma inda suka fito.
A watannin da suka gabata ne gwamnatin jihar Kaduna ta jagoranci yin sulhu da ƴan fashin daji a wasu yankunan jihar waɗanda suka shafe shekaru masu yawa suna fama da hare-hare.
Al'ummar yankunan da aka yi sulhun sun sanar da cewa sun samu sauƙi sanadiyyar ɗaukewar hare-haren ƴan fashin dajin.
Sai dai jihohi da dama masu maƙwaftaka da Kaduna na adawa da ɗaukar irin wannan mataki na sulhu da ƴan bindiga.
Zubairu Isma'il Zanna, wanda ɗan majalisa ne mai wakiltar ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja ya ce sulhun na jihar Kaduna bai zamo alheri ga jama'ar sa ba.
A hirarsa da BBC, Zanna ya ce kafin sulhun a jihar Kaduna, jama'arsa na zaune lafiya amma yanzu sun tsinci kansu cikin hare-haren ƴanbindigar, waɗanda yanzu haka suke riƙe da mutane 132 da suka kwasa daga ƙauyukan jihar Neja.
"An samu tsawon watanni ba a samu irin wannan matsala ba, sai yanzu da aka yi sulhu da ƴanbindiga a Birnin Gwari, tun daga lokacin suke gangarowa yankin jihar Neja, dajin Alawa nan suke zuwa su laɓe su ɗebi mutane su wuce," Cewar Hon Zanna.
Ɗan majalisar ya ce sun gabatar da ƙuduri domin ganin gwamnatin tarayya da ta jiha sun ƙara tura jami'an tsaro yankunan domin shawo kan matsalar, "An daukar mana mutane 132 yawancinsu mata da ƙananan yara."
Zanna ya ce ana sanar da su lokaci da kuma hanyoyin da ƴanbindigar ke bi domin kai hare-hare, lamarin da ya sanya suka san daga inda suke fitowa.
A kwanakin baya, gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya bayyana wa BBC dalilan da suka sanya gwamnatinsa ta amince ta yi sulhu da ƴanfashin daji a jihar yayin da jihohin da ke maƙwaftaka suka yi watsi da irin wannan tsari.
Uba Sani ya ce tun farko al'ummar yankunan da suka fi fama da matsalar tsaron ne suka buƙaci a yi zaman sasanci da ƴan bindiga, inda gwamnati ta duba sannan ta yanke shawarar amincewa da hakan.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Matsalar ƴan fashin dajin wadda ta addabi jihoin arewa maso yammacin Najeriya ta tursasa wa manoma barin ƙauyuka, lamarin da ya sanya albarkatun noma da ake samu ya yi ƙasa, wanda masana suka bayyana cewa ya taimaka wajen haifar da tashin farashin kayan masarufi.
Wani abu da ke sanya al'umma a yankunan da ke fama da rashin tsaro na Najeriya yin ɗari-ɗari da batun yin sulhu da ƴan fashin daji shi ne batun ɗorewar al'amarin.
A shekarun da suka gabata an gwada yin sulhu a wasu yankunan ƙasar da ƴan fashin dajin, sai dai lamarin bai ɗore ba.
Baya ga ƙauyukan da suka sha kwatanta irin yin hakan, wani babban misali shi ne sulhun da gwamnatin jihar Zamfara ta taɓa yi da ƴan fashin daji, lamarin da ya rushe daga baya.
Matsalar rashin tsaro sanadiyyar ƴan fashin daji a arewa maso yammacin Najeriya ta haifar da asarar ɗimbin rayuka da kuma tagayyara al'umma da dama.
Lamarin ya fi addabar jihohin Kaduna, da Katsina da Zamfara da Sokoto da kuma Neja.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa tana bakin ƙoƙarinta wajen shawo kan matsalar.
Sai duk da nasarorin da ta samu a baya-bayan nan, ƴan fashin na ci gaba da tsananta wa al'umma ta kisa da kuma garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.










