Ƴan bindiga sun sanya wa mutanen ƙauyukan Zamfara harajin kusan miliyan 200

.

Asalin hoton, .

Bayanan hoto, .
Lokacin karatu: Minti 2

Rahotanni daga garuruwan ƙaramar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara na cewa ƴan bindiga sun ɗorawa jama'a harajin da ya kai naira miliyan 172 baya ga neman ba su buhunan abinci da makanatan su.

Haka ma a ƙaramar hukumar Bukkuyum duk dai a jihar ta Zamfara an samu rahoton cewa wasu gungun ƴan bindigar sun yi garkuwa da fiye da mutum 40 wadanda galibinsu mata ne da yara kanana.

Rahotannin na cewa 'yan bindigar karkashin jagorancin shugabansu Ɗan-Isuhu, sun wajabtawa al'ummar yankunan su ba su tarin buhunan waken suya da sauran kayan abinci.

Rahoton wanda wani mai bincike kan sha'anin tsaro a tafkin Chadi ya Zagazola Makama ya rawaito, ya ce ƴan bindigar sun dora musu dimbin harajin wuce kima da suka raba a garuruwan Gijinzama masu naira miliyan N8.5 million sai Dakolo mai 5 tare da buhunan waken suya 20 da kauyen Gunja da suka dorawa mazaunansa harajin miliyan 7 da Kauyen Kane mai 5 da Kurar Mota da aka tilastawa samo miliyan 6 da za su fansar kansu da sauran garuruwa.

Haraji mafi yawa shi ne wanda aka dorawa al'ummar Kunchin Kalgo na naira miliyan 20 yayin da Sungawa da Rakyabu za su biya naira miliyan 15 kowanensu.

Kazalika, duka dai a jihar ta Zamfara, wasu bayanai cewa karin wasu gungun 'van bindiga sun afkawa kauyen Ganau da ke karamar hukumar Bukuyyum inda suka kone gidaje da kuma sace mutane kusan 40 da suka hada da mata da yara kanana. Wannan lamari dai ya tilasta daruruwan mutane da suka hada da mata da yara kanana da ake jan hannuwansu na tafiya a kasa tserewa suna barin gidajensu.

Duk ƙokarin da BBC ta yi na jin ta bakin rundunar yan sandan jihar haƙanmu bai cimma ruwa ba, amma kakakin gwamnan jihar Mallam Sulaiman Bala Idris, ya ce zafara hare haren da ƴan bindigar suka yi na nuna irin yadda suka rasa mafita ne sakamakon gana masu azaba da jami'an tsaro ke yi, don haka a cewarsa, idan ganga ta fiye zaƙi lokacin fashewarta ne ya yi.

Wannan dai na zuwa ne dai dai lokacin da hare-haren 'yan bindiga ke kara kunno kai a sassan jihar tun bayan da shahararren dan bindigar nan Bello Turji ya bayar da sanarwar far ma garuruwa da yawa a jahohin Sokoto da Zamfara da sauran makwabta muddin ba a sako 'yan uwansa ba, ya vin da a hannu daya kuma gwamnatin Najeriya da ta Zamfarar ke bayyana cewa suna cin galaba akan 'yan fashin daji.