Abin da ya sa aka samu ƙaruwar hare-hare a Najeriya - Shalkwatar tsaro

Asalin hoton, DHQ
Cikin makonnin da suka gabata a Najeriya, an ga yadda Boko Haram da kuma ƴan fashin daji suka ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare a wasu sassan ƙasar.
Lamarin da ya bar al'ummar ƙasar cikin taraddadi kan dalilin faruwar hakan.
Mayaƙan Boko Haram sun kai hare-hare a jihar Borno, waɗanda ya zuwa yanzu ba a kammala tantance ɓarnar da hakan ya haifar ba.
Duk kuwa da cewa rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa jami'anta shida ne aka kashe a harin da aka kai 'na ramuwar-gayya' a ƙaramar hukumar Damboa da ke jihar Borno.
Sannan kuma gwamnatin jihar Borno ta bayyana cewa an kashe aƙalla manoma da masunta 40 a harin da mayaƙan Boko Haram ɗin suka kai a ƙaramar hukumar Kukawa da ke jihar ta Borno, duk da cewa wasu rahotannin sun ce alƙaluman sun zarta haka.
A arewa maso yammaci ma an samu ƙaruwar hare-haren ƴan bindiga, lamarin da ya kai ga cewa rundunar sojin Najeriya ta kai wani hari ta sama, wanda ya faɗa kan fararen hula a ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.
Dalilin ƙaruwar hare-hare

Asalin hoton, X/DHQ
A ranar Alhamis ne shalkwatar tsaro ta Najeriya ta yi ƙarin haske kan dalilan da suka sanya aka samu ƙaruwar ayyukan ƴan bindiga a ƙasar cikin kwanakin nan.
Lokacin da ya gana da manema labarai, daraktan harkokin yaɗa labarai na shalkwatar, Manjo-Janar Edward Buba ya bayyana cewa babban dalilin hakan shi ne kwararowar baƙin ƴan bindiga daga ƙasashen waje.
Ya ce "dakarun Najeriya na tarwatsa da kuma kawar da sake ɓullowar hare-haren ta'addanci a arewa maso yamma da kuma arewa maso gabas, wanda ke faruwa sanadiyyar kwararowar mayaƙa daga ƙasashen yankin Sahel".
Ya ƙara da cewa "zai iya yiwuwa dakarun (Najeriya) su samu koma-baya wajen gudanar da ayyukansu, abu ne da aka saba gani a duk wani wuri da ake yaƙi.
"Babbar manufarmu ita ce karya ƙarfin da ƴan ta'adda ke da shi na yin yaƙi, kuma muna nan a kan hakan," in ji Buba.
Jami'in na shalkwatar tsaro ya kuma ɗora wani ɓangare na laifin ƙaruwar hare-haren kan wasu mutane a cikin Najeriya waɗanda ke haɗa kai da mayaƙan da ke shigowa ƙasar.
"Su ne infoma, waɗanda ke bai wa ƴan ta'adda rahoton ayyuka da zirga-zirgar dakaru. Amma duk da haka, dakarunmu na sane da nauyin da ke kansu na yaƙi da masu tayar da ƙayar baya a faɗin ƙasa."
Waɗanne mayaƙa ne suka shiga Najeriya?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Duk da dai shalkwatar tsaron ta Najeriya ba ta yi ƙarin haske kan mayaƙan da suka kwarara zuwa Najeriyar ba, amma a baya-bayan nan ƙasar ta fuskanci ayyukan wata sabuwar ƙungiyar ƴan bindiga da ake kira Lakurawa.
Wata majiya ta shaida wa BBC cewa 'yan ƙungiyar sun shiga yankunan jihohin Sokoto da Kebbi ne daga ɓangaren yankin Sahel, wanda ya ƙunshi ƙasashen Nijar, da Mali, kuma mutane ne da suka ƙunshi ƙabilu daban-daban na Sahel.
Bayanai sun nuna cewa idan mutanen suka yi wa'azi ko faɗakarwa sukan fassara da Hausa, da Fulatanci, da Abzinanci, da Tubanci, da Barbarci, har ma da Ingilishi.
Dama dai yankin na Sahel ya daɗe yana fama da matsalar ƴan tayar da ƙayar baya da na masu iƙirarin jihadi.
Misali, yankin 'Zone de trois Frontieres' wanda ya ƙunshi iyakokin ƙasashen Jamhuriyar Nijar da Mali da Burkina Faso, ya yi ƙaurin suna wajen ayyukan mayaƙa masu kai hare-hare.
Sannan a shekarun baya hukumomin Najeriya sun koka kan kwararowar mayaƙa da makamai daga ƙasar Libya, ƙasar da ke fama da rikice-rikice tun bayan faɗuwar gwamnatin marigayi Muammar Ghaddafi.
'Mun kashe ƴan bindiga da ƴan Boko Haram 156'
Sanarwar da Shalkwatar tsaron Najeriyar ta fitar kan ayyukan da take gudanarwa a faɗin ƙasar ya bayyana wasu nasarari da ya samu, waɗanda suka haɗa da:
- Kashe mayaƙa da ƴan fashin daji 156
- Ƙwato bindiga 'labarbar' guda ɗaya, wato GPMG
- Ƙwato bindiga ƙirar AK47 guda 68
- Ceto mutane 181 da aka yi garkuwa da su











