Da gaske ƙasashen waje na taimaka wa Boko Haram?

Asalin hoton, Getty Images
Bayani game da inda ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya ke samun kuɗaɗe da makamai wani gaibu ne da aka daɗe ana muhawara a kai.
Sau da yawa akan riƙa mamakin yadda irin waɗannan ƙungiyoyi waɗanda yawanci kan fara daga ɗaiɗaikun mutane marasa galihu ke yin ƙarfin da ke zama alaƙaƙai ga gwamnatoci waɗanda ke ware biliyoyin kuɗaɗe domin ƙarfafa ɓangaren tsaro a ƙasashensu kowace shekara.
Kimanin shekara 15 da fara rikicin Boko Haram, ɗaya daga cikin ƙungiyoyi mafiya hatsari a duniya, wadda ta yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 36,000 da tarwatsa miliyoyi, muhawara kan waɗanda ke taimaka mata ta sake tasowa.
A tattaunawarsa da kafar yaɗa labarai ta Aljazeera, babban hafsan tsaron Najeriya, Laftanar Janar Musa ya yi zargin cewa akwai lauje cikin naɗi, sannan ya yi kira ga hukumomin duniya su bincika domin gano masu ɗaukar nauyin "ta'addancin".
Jawabin na Janar Musa na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya suka cigaba da fuskantar matsalolin tsaro duk da nasarorin da sojojin ƙasar suka bayyana cewa suna samu.
Me Janar Musa ya ce?
Janar Musa ya bayyana a tattaunawar cewa suna magana da ƙasashen duniya kan buƙatar a bincika masu ɗaukar nauyin harkokin ƴanbindiga a ƙasar
Ya ce, "Yanzu da muke magana, sama da ƴan Boko Haram 120,000 sun miƙa wuya, kuma yawancinsu idan suka zo za ka gan su da kuɗaɗen ƙasashen waje. Ta yaya suke samun kuɗaɗen ƙasashen waje? Ta yaya suke samun horo? Ta yaya suke samun makamai? Ta yaya suka iya ɗaukar kusan shekara 15 suna yaƙi? Waɗannan tambayoyi ne da ya kamata kowa ya tambaya," in ji shi.
Da aka tambaye shi akwai wanda yake zargi, sai ya ce, "wataƙila akwai wani abun daga ƙasashen waje. Ya kamata Majalisar Ɗinkin Duniya ta shigo domin bincikawa tare da gano masu ɗaukar nauyin su."
Ya ce ba Najeriya kaɗai ba ce matsalar take shafa, "yankin Afirka ta yamma da yankin Sahel, sannan ma idan ba a ɗauki mataki ba, matsalar za ta shafi duk duniya."
"Burinmu kawai ƙasarmu ta zauna lafiya, amma wasu mutane ba sa so, kuma a shirye suke su yi duk abin da za su iya yi domin su kawo mana tsaiko. Kusan shekara 33 ke nan ina aikin soja, amma duk lokacin da muka fara samun nasara, sai wasu su kawo mana tsaiko."
Da aka tambaye shi yana zargin wasu a cikin gwamnati ne, sai ya ce, "ba sai daga gwamnati ba. Lamarin na da alaƙa da ƙasashen waje." Sai dai ya ce suna fata nan da shekara biyu za su kawo ƙarshen matsalar.
Waɗannan kalamai na babban hafsan sojin Najeriya ya tayar da ƙura a Najeriyar, wannan ne ya sanya BBC ta tuntuɓi masana harkar tsaro a yankin Sahel domin ƙarin bayani kan kalaman na Janar C.G. Musa.

Asalin hoton, Getty Images
'Akwai ƙamshin gaskiya'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Barista Audu Bulama Bukarti, wanda mai bincike ne kan harkokin tsaro, ya ce ya daɗe da gano cewa ƙungiyar Boko Haram na samun taimako daga ƙasashen waje.
A cewarsa, "za ka iya cewa akwai ƙamshin gaskiya domin mun daɗe da bankaɗowa cewa akwai ƙungiyoyi na ƙasa da ƙasa da suke taimakon Boko Haram.
"Misali tun kimanin shekarar 2011, bayan an ci ƙarfin Boko Haram a 2009, da suka ɗan ja baya, ƙungiyar Al-Qaida ce ta turo musu kimanin miliyan 50 na wancan lokacin da makamai wanda da shi suka fara dawowa. A shekarar 2014 Boko Haram ta yi mubaya'a ga ISIS, kuma tun lokacin muke da shaidar cewa tana taimaka musu."
Ya ce ko wasu ƴan Najeriya da aka hukunta a Dubai da zargin suna canja wa BH kuɗaɗe, "takardun kotun sun nuna daga Turkiyya aka kai kuɗin Dubai, su masu canjin ba ƴan Boko Haram ba ne, kuma ba lallai sun san masu kuɗin ba, su dai kawai sai su canja, su tura wa wakilansu na Najeriya. Sai masu kuɗin su zo su karɓa, kuma takardun kotun na nuna cewa ƴan Boko Haram ne."
Sai dai ya ce Boko Haram da na wasu hanyoyin na samun kuɗaɗe, cikin irin waɗannan hanyoyi su ne na karɓar kuɗi daga gwamnatoci da hukumomi ta hanyar aikata ɓarna.
Ya ce misalin irin wannan shi ne lokacin da ƴan ƙungiyar suka yi garkuwa da ƴan matanan makarantar gwamnati ta Chibok a jihar Borno.
Bukarti ya bayyana cewa an biya maƙudan kuɗaɗe domin sako wasu daga cikin ɗaliban.
Baya ga gwamnatin Najeriya, Bulama ya ce hatta gwamnatin Faransa ma ta biya kuɗade domin ceto wasu daga cikin ƴan ƙasarta da Boko Haram ta yi garkuwa da su.
Najeriya da Faransa dai ba su tabbatar da hakan ba, kuma sau da yawa sun sha ƙaryata batun biyan irin waɗannan ƙungiyoyi kuɗaɗe domin biyan wasu buƙatu.
Haka nan kuma Bukarti ya ce ƙungiyar Boko Haram na yin noma da kuma karɓar haraji wurin masu kiwon kifi.
A nasa ɓangaren, Dr Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited ya ce lallai bincike ya nuna cewa Boko Haram na samun tallafi daga ƙasashen waje.
Sai dai ya ce inda yake da ɗan ja shi ne maganar cewa ba a san su waye suke ɗaukar nauyin ba.
Ya kuma ce bai kamata babban jami'in gwamnati ya je babbar kafar watsa labarai ta ƙasar waje, "ya nuna gazawar tsari na tsaro ba."

Asalin hoton, Getty Images
Saɓanin ra'ayi
Sai dai a nasa ɓangaren Group Captain Sadiq Garba Shehu (Mai Ritaya) wanda mai sharhi ne da bayar da shawara kan harkokin tsaro da aikin soja, ya shaida wa BBC cewa ya zuwa yanzu bai samu wata ƙwaƙƙwarar hujjar da ke tabbatar da iƙirarin taimaka wa Boko Haram daga ƙasashen waje ba.
Ya ce, "gaskiya wannan batun cewa ko wasu ƙasashe suna da hannu a waɗannan abubuwan da ke faruwa a Najeriya, an daɗe ana yi. Amma a matsayina na mai bincike, duk lokacin da aka dawo da maganar idan muka bibiye ta, sai mu ga babu wata shaida ƙwaƙƙwara.
Ya ce babu wata hujja da take bayyana irin ribar da wata ƙasa za ta amfana idan Boko Haram ta ci Najeriya da yaƙi ko ta kafa gwamnati.
Me ya kamata a yi?
Barista Bulama ya bayar da wasu hanyoyi da yake ganin suka fi kamata Najeriya ta bi domin magance matsalar.
- Amfani da kundin daƙile ta'addanci wato terrorism prevention act wanda ya bayyana yadda za a daƙile hanyoyin shigowar kuɗaɗe.
- Duk wanda zai tura kuɗi Najeriya ko da bai bi ta banki to dole ya haɗa wani kasuwanci.
- Gwamnatin Najeriya ta jagoranci bincike, sai ta nemi haɗin kan ƙasashen duniya da ƙwararru.
- A tabbatar da daƙile hanyoyin da ƙungiyoyin suke kashe kuɗaɗe.
A nasa ɓangaren, Kabiru Adamu ya ce ya ce ya kamata a ce akwai haɗin kai tsakanin ɓangarorin tsaro domin a cewarsa, "Akwai Hukumar NFIU, wadda haƙƙinta ne sa ido a kan safarar kuɗaɗen ta'addanci, kuma tana da hanyoyi da yawa na sa ido. Har sun kama wasu. Amma matsalar ita ce rashin hukunta waɗanda aka kama."
Ya ce majalisar dokokin Najeriya na da rawar da za ta taka domin sa ido da tabbatar da kowane ɓangare yana aikin da ya dace.
A game da fargabar da ake yi na yiwuwar sauran ƙungiyoyin ƴanbindiga da ke Najeriya na fara samun tallafi daga ƙasashen waje, Kabiru Adamu ya ce ai dukkan kungiyoyin laifuka suna amfani da ƙungiyoyin ƙasashen waje. "Ai ƙungiyoyi ne da suke da alaƙa da ƙungiyoyi masu ikirarin jihadi irn su al-Qaed da ISIS. Sannan akwai ƙungiyoyin laifuka na ƙasa da ƙasa da suke amfani da hanyoyin safarar kuɗaɗe da ƴan'adam kuma suna taimakon ta'addanci da irin kuɗaɗen."










