Me ya sa Boko Haram ke ci gaba da kai hare-hare?

Asalin hoton, Boko Haram
Tun bayan harin da mayaƙan Boko Haram na ɓangaren ISWAP suka kai wa sojojin Najeriya a ƙauyen Sabon Gari da ke karamar hukumar Damboa ta jihar Borno inda suka kashe sojojin guda shida, ƴan Najeriya ke ta nuna shakku kan ikrarin jami'an tsaron Najeriyar na tarwatsa ƴaƴan ƙungiyar.
Sai dai kuma wata sanarwar da shalkwatar tsaron ƙasar ta fitar, ranar Laraba ta ce harin na ramuwar gayya ne, kan kisan da dakarun ƙasar suka yi wa wani kwamanda da wasu mayaƙan ƙungiyar.
Sanarwar ta ce dakarun soji sun kashe ƴanbindiga 34 tare da ƙwato bindiga kirar AK 47 guda 23 da alburusai fiye da 200.
Me harin ke nufi?

Asalin hoton, Getty Images
Masana harkokin tsaro da suka haɗa da Malam Kabiru Adamu shugaban kamfanin Beacon Consulting a Najeriya da Barrister Bula Bukarti lauya mai zaman kansa a Burtaniya na ra'ayoyi babanta kan ko har yanzu Boko Haram na da ƙarfi.
"Lallai an ci ƙarfin Boko Haram to amma yanzu ƙunigyar babbar barazana ce ga ƙasa. Wannan hari abu ne mai tayar da hankali domin yana alamta cewa ƴan Boko Haram har yanzu na da ƙarfin da za su iya kai wa sansanin soji hari musamman bisa la'akari da cewa harin ba sojoji ne suka kai wa Boko Haram ba ko kuma su yi arangama a kan hanya.
Boko Haram ne suka niƙi gari suka kai hari kan sansanin sojoji. Kuma wannan irin abun da muka gani a shekarun baya ne lokacin da ƙungiyar ke da ƙarfi. Wannan abu ne mai tayar da hankali." In ji barrister Bukarti.
To sai dai shi kuma ma Malam Kabiru Adamu ya ce harin ba abun mamaki ba ne bisa la'akari da dalilai guda uku:
"Boko Haram tana yaƙin sunƙuru ne saboda haka ba abun mamaki ba ne idan suka kai wa sojoji hari ba wai don ƙungiyar na da ƙarfi ba ne. A koyaushe dama ƙungiyar ke nema wajen kai hari kuma a duk lokacin da suka samu dama za su kai hari.
"Sannan abu na biyu shi ne akwai wasu garuruwa da ke da muhimmanci ga ƙunigyar ciki har da Damboa da suke ganin idan sun kama su za su kasance cibiyoyin daulolinsu. To akwai yiwuwar wannan ne dalilin da ke sa suke kai musu hare-haren."
Dalili na uku shi ne tun bayan da rundunar sojin hadin gwiwa da ke yaƙi da ƙungiyar a yankin tafkin Tchadi suka fatattaki ƴan ƙungiyar, an samu rahotannin kwararowarsu zuwa cikin Najeriya saboda haka babu mamaki ganin irin wannan harin," in ji Malam Kabiru Adamu.
A wane hali Boko Haram ke ciki?

Asalin hoton, Getty Images
Barrister Bulama Bukarti ya ce duk da cewa an ci ƙarfin Boko Haram nesa ba kusa ba to amma har yanzu akwai sauran rina a kaba.
Ya ce dalilin da ya sa ba a cika ji cewa sun kai hari ba shi ne tun bayan mutuwar Abubakar Shekau, shugabannin ƙungiyar na yanzu ba sa kai hare-haren kisa kamar irin na baya. Sannan kuma akan samu yanayin da ake ɓoye batun hare-haren da ƙungiyar ke kaiwa.
"Ƙunigyar tana nan da makamai da mayaƙa. Sannan Boko Haram da sojojin Najeriya kowa ya kama wani sashe ba a kai wa juna hari. To idan ka ga an yi irin wannan zama to kowanne ɓangare na neman dama ne kan abokin hamayyarsa.
Har yanzu Boko Haram na cikin dazuka da ƙauyukan tafkin Tchadi da arewacin jihar Yobe. Kuma a gaskiya sojojin Najeriya ba su fiya kai musu hari ba. Za ma a iya cewa kamar an sallama musu dazukan da ƙauyukan. Suna nan sun ja tunga kuma lallai sai an kai musu hari har inda suke idan ana so a gama da su." In ji Bulama Bukarti.
Hanyoyi biyar na kawo ƙarshen Boko Haram
Masanan biyu sun amince da wasu hanyoyi da suka ce su ne idan aka bi su to za a ga bayan ƙungiyar Boko Haram.
- Dole a kai musu (Boko Haram na ɓoye a dazuka da kauyuka) yaƙi har maɓoyarsu
- Daƙile yunƙurin ƙungiyar na ɗaukar sabbin mambobi
- Daƙile hanyoyin samun kuɗaɗensu na gudanarwa
- Daƙile hanyoyin samun makamai da hanyoyin sufuri
- Bin dokokin daƙile hanyoyin ta'addanci a tsarin kundin Najeriya











