Yadda Boko Haram ta 'kashe masunta da manoma 40' a Borno

Asalin hoton, Boko Haram
Ƙungiyar Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare a yankunan jihar Borno, kamar yadda ta sake yunƙorowa a baya-bayan nan.
A ranar Lahadi, ƙungiyar ta kai hari kan masunta da manoma a ƙauyen Dumba da ke kusa da Baga a ƙaramar hukumar Kukawa, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.
Wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labaru na jihar Borno, Usman Tar ya fitar ta ce rahotannin da aka tattara na baya-bayan nan sun nuna cewa an kashe manoma 40 a harin na ranar Lahadi.
Haka nan kuma akwai mutane da dama waɗanda ba a san inda suke ba.
Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum ya yi alla-wadai da harin, sannan ya buƙaci dakarun Najeriya da ke aiki a yankin arewa maso gabashin ƙasar da su zaƙulo waɗanda suka kai shi.
Yadda manoman suka faɗa tarkon mahara

Asalin hoton, fb/Babagana Zulum
Sanarwar ta bayyana cewa manoman sun faɗa tarkon maharan ne lokacin da suka tsallake yankunan da ke da tsaro, zuwa yankunan da babu tsaro, lamarin da ya bai wa maharan damar kai musu farmaki.
"Waɗannan yankuna wurare ne da ƴan bindiga masu shawagi ke iya kai hare-hare cikin dare, kuma yankuna ne da ke ƙunshe da nakiyoyi," in ji sanarwar.
Lamarin da ya sanya gwamnan ya yi kira ga mutanen yankin su riƙa tsayawa a wuraren da aka riga aka tabbatar da tsaron su.
Sanarwar ta ƙara da cewa "fita daga tuddan mun-tsira da aka keɓe abu ne mai haɗari yayin da dakaru ke ƙoƙarin ganin sun tabbatar da tsaron lafiyar al'umma a ɓangare ɗaya kuma suna ƙoƙarin yaƙar 'ƴan ta'adda', inda suke fargabar za a yi amfani da fararen hula a matsayin garkuwa".
Hare-hare na baya-bayan nan
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Hari na baya-bayan nan da mayaƙan na Boko Haram suka kai wanda ya girgiza al'umma, shi ne wanda suka kai a kan wani sansanin soji da ke ƙaramar hukumar Damboa, lamarin da ya haifar da asarar rayukan sojoji shida, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shalkwatar tsaro ta Najeriya, Edward Buba ya fitar ta bayyana cewa harin na ramuwar gayya ne.
Sai dai sanarwar ta ce sojojin Najeriya sun samu nasarar kashe mayaƙa 34 a lokacin harin.
Baya ga haka, akwai rahotannin da ke nuna cewa a baya-bayan nan mayaƙan sun kai hari a ƙaramar hukumar Chibok, inda suka kashe mutane da sace amfanin gona.
A watan Yunin shekarar da ta gabata ma an kai wasu hare-hare biyu na ƙunar baƙin wake a garin Gwoza, waɗanda suka yi ajalin aƙalla mutum 18.
Waɗannan hare-hare na baya-bayan nan sun saka shakku a zukatan al'umma game da ikirarin da rundunar sojojin Najeriya ke yi na cewa ta ci galaba a kan ƙungiyar ta Boko Haram, wadda ta kwashe sama da shekara 10 tana ayyukan ta'addanci a faɗin arewa maso yammacin Najeriya da kuma ƙasashe masu maƙwaftaka.
Wane hali Boko Haram ke ciki?
Barrister Bulama Bukarti, masani kan harkar tsaro a yankin Sahel ya ce duk da cewa an ci ƙarfin Boko Haram nesa ba kusa ba to amma har yanzu akwai sauran rina a kaba.
Ya ce dalilin da ya sa ba a cika ji cewa sun kai hari ba shi ne tun bayan mutuwar Abubakar Shekau, shugabannin ƙungiyar na yanzu ba sa kai hare-haren kisa kamar irin na baya. Sannan kuma akan samu yanayin da ake ɓoye batun hare-haren da ƙungiyar ke kaiwa.
"Ƙunigyar tana nan da makamai da mayaƙa. Sannan Boko Haram da sojojin Najeriya kowa ya kama wani sashe ba a kai wa juna hari. To idan ka ga an yi irin wannan zama to kowanne ɓangare na neman dama ne kan abokin hamayyarsa.
Har yanzu Boko Haram na cikin dazuka da ƙauyukan tafkin Tchadi da arewacin jihar Yobe. Kuma a gaskiya sojojin Najeriya ba su fiya kai musu hari ba. Za ma a iya cewa kamar an sallama musu dazukan da ƙauyukan. Suna nan sun ja tunga kuma lallai sai an kai musu hari har inda suke idan ana so a gama da su." In ji Bulama Bukarti.










