Me ya rage wa Simon Ekpa, jagoran IPOB da ake tuhuma da ta'addanci a Finland?

Asalin hoton, Simon Ekpa/X
Masu gabatar da ƙara a ƙasar Finland sun gabatar da jagoran IPOB, Simon Ekpa bisa zarginsa da yaɗa ta'addanci ta intanet.
A wata sanarwa da hukumar gabatar da ƙara ta Finland ta fitar, ta ce suna tuhumarsa "bisa ingiza mutane su aikata ɓarna da manufar ta'addanci da kuma shiga cikin ayyukan ƙungiyar ta'adddanci."
Sanarwar ta ce hukumomin ƙasar na zargin Ekpa ne da aikata laifukan a tsakanin shekarar 2021 zuwa 2024. Sun ce tuhumar na da alaƙa da yunƙurin wanda ake zargin na kafa ƙasar Biafra.
Masu gabatar da ƙara ba su bayyana sunan wanda ake zargin ba, amma kafar yaɗa labarai ta Finland, YLE ta ce Simon Ekpa ne.
Simon Ekpa ya sauya lauya
A watan Disamban 2024, BBC ta tura wa lauyan Simon Ekpa, Ilkka Kopra saƙo domin neman bahasin abin da ake ciki da kuma sanin wa'adin zamansa a gidan yari.
Sai lauyan ya amsa da cewa, "kotu ce ta yanke masa zaman gidan yari."
Ya ƙara da cewa sun yi duk abin da za su iya domin fitar da shi, amma sun kasa, sannan bai san wa'adin da ake yanke masa ba.
BBC ta ƙara bin diddigin lamari domin sanin me Ekpa zai yi bayan gwamnatin Najeriya ta ƙwace kadarorinsa.
A wannan lokacin ne muka bayanin cewa Ekpa ya canja lauya saboda wanda yake wakiltarsa da farko ya yi ritaya. Sai ya ɗauki wani sabon lauya.
Ba a fara yunƙurin mayar da Ekpa ba
A nasa ɓangaren, Ministan Shari'a na Najeriya, Lateef Fagbemi ya ce ba su fara wani yunƙurin mayar da shi ƙasar ba, kamar yadda ake tunanin ya faɗa.
Ministan ya bayyana haka ne a matsayin ƙara haske kan bayanin da ya yi a wajen taron ƙara wa juna sani a Abuja, wanda ya ce ba a fahimce shi ba ne.
Mai taimaka masa kan harkokin sadarwa, Kamarudeen Ogundele, ya ce abin da ake yaɗawa ɗin ba haka ministan yake nufi ba.
"Abin da ministan ya faɗa a lokacin da yake amsa tambayoyi shi ne gwamnatin Najeriya na ganawa da ta Finlanda domin tabbatar da Simon Ekpa ya fuskanci hukuncin laifin da ya aikata."










