Najeriya ta ayyana Lakurawa da Simon Ekpa a matsayin masu ruruta ta'addanci

Asalin hoton, SIMON EKPA
Gwamnatin Najeriya ta ayyana mutum 17 a matsayin waɗanda ta ƙaƙaba wa takunkumin tare da kulle asusun bankinsu saboda harkokinsu da ake zargi na tallafa wa ayyukan ta'addanci.
Simon Ekpa wanda yanzu haka yake goyon bayan haramtacciyar ƙungiyar fafutikar kafa ƙasar Biyafara wato Ipob da ke gidan yari a Finland, bisa zargin shi da ƙasar ke yi da harkokin ta'addanci yana cikin waɗanda gwamnatin ta rufe wa asusun bankin.
Haka kuma Lakurawa da ke ikirarin jihadi a yankin arewa maso yammacin ƙasar na ciki.
A ranar Alhamis ne gwamnatin Najeriya ta ɗauki wannan mataki bayan wani taro a Abuja, inda ta ayyana mutanen guda 17.
Kwamitin ya ɗauki matakin ne bisa dogaro da sashe na 54 na dokar hana yaɗuwar ta'addanci ta 2022.
Sashen ya bai wa kwamitin damar ganowa da rufe asusun bankuna da sauran kadarorin waɗanda ake zargi ba tare da sanar da su ba.
Wani ɓangare na sashen dokar ya ce "rufe asusun bankunan da wasu kadarorin zai shafi dukkan dukiya da kadarorin da suke da alaƙa da wanda ake zargi da ɗaukar nauyin ta'addanci ko ake musu kallon barazana."
Hakan ya sa kwamitin ya rufe asusun banki da wasu kadarorin Simon Ekpa da Lakurawa da wasu mutane guda 15 da suke cikin waɗanda kwamitin ya gano.
Haka ma asusun bankunan da suke da wata alaƙa da waɗanda ake zargin ma za a rufe su, kamar yadda kwamitin ya bayyana.
A watan Maris na 2024 ne rundunar sojin Najeriya ta ayyana Ekpa da wasu mutane guda 96 a matsayin waɗanda ake nema ruwa a jallo bisa zargin su da ta'addanci da ingiza yunƙurin ɓallewa daga ƙasar da tayar da zaune tsaye.
Haka kuma a watan Nuwamban 2024, gwamnatin ƙasar Finland ta ce Ekpa yana "ingiza fararen hula su yi wa gwamnati bore da sauran laifuka a kudu maso gabashin Najeriya," alhalin yana zaune a Finland.
Sunayen waɗanda aka rufe wa asusun banki da kadarori
- Simon Ekpa Njoku
- Godstime Promise Iyare
- Francis Chukwuedo Mmaduabuchi
- John Anayo Onwumere
- Chikwuka Godwin Eze
- Edwin Augustine Chukwuedo
- Chinwendu Joy Owoh
- Ginika Jane Orji
- Awo Uchechukwu
- Mercy Ebere Ifeoma Ali
- Ohagwu Nneka Juliana
- Eze Chibuike Okpoto
- Nwaobi Henry Chimezie
- Ogomu Peace Kewe
- Igwe Ka Ala Enterprises
- Seficuvi Global Company
- Ƙungiyar Lakurawa
Waɗanda aka rufe musu asusun da kadarorinsu za su yi abubuwan da kwamitin ya zayyana:
Za su bayyana a gaban kwamitin domin kare duk wata hada-hada da suka yi da suke ganin sun yi a kan ƙa'ida.
Dole su haɗa rahoton hada-hadar da ba su amince da su ba a hukumar yaƙi da ɗaukar nauyin ta'addanci ta NFIU domin su ƙara nazartar hada-hadarsu.
Dole su haɗa bayanan hada-hadar da suke gani ba amince da su ba, kamar dukkan sunayen da suke kama da juna tun kafin a fitar da sunayen nan zuwa bayan fitar da sunayen ga hukumar NFIU.
Abin da ya kamata Ku sani game da kwamitin ƙaƙaba takunkumin
Kamar yadda bayanai suka nuna a shafin intanet na kwamitin ƙaƙaba takunkumi na Najeriya, an kafa kwamitin ne domin ƙaƙaba takunkumi ga duk waɗanda ake zargi da harƙallar kuɗaɗe da ake zargi na da alaƙa da ta'addanci.
Takunkumin hada-hadar kuɗi da ake kira Targeted Financial Sanctions wato TFS a ƙataice na faɗa wa kan duk wani wanda ake zargi na da alaƙa da ta'addanci da ɗaukar nauyin ta'addanci da taimakawa wajen yaɗuwar makamai ta hanyar taimaka musu da kuɗi da kayan aiki.
Ministan shari'a ne ke zama shugaban kwamitin kuma yana da ikon ɗaukar duk matakan da ayyana, waɗanda suka dace da ƙa'idoji da tsare-tsaren kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya.

Asalin hoton, Simon Ekpa/X
Wane ne Simon Ekpa?
Simon Ekpa ɗan Najeriya ne mazaunin Finland wanda yake fafutikar kafa ƙasar Biafra, kuma yake ikirarin maye gurbin tsohon shugaban ƙungiyar Ipob, Nnamdi Kanu.
Ekpa yana zaune ne a ƙasar Finland, amma yake jagorantar harkokin kafa ƙasar ta Biafra daga can, sannan yake kira da ƴan ƙabilar Igbo da ke kudu maso gabashi da su ƙauracewa zaɓe har ai gwamnatin Najeriya ta saki Kanu.
A shafinsa na X, Ekpa ya bayyana kansa a matsayin mai fafutikar ƙwatar ƴancin mutane, babban jami'in gudanarwa, kuma babban mai bada shawara kan harkokin shari'a na Ekpa & Co Oy, mai bincike kan harkokin shari'a, marubuci, mai sharhi kan al'amuran yau da kullum, ɗan siyasar Finlanda kuma kakakin Biafra.







